7

1.8K 105 8
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

               0⃣7⃣

       Washe gari aka yi duk wani gyare gyare da ya kamata ayi a shagon, kwanan su biyu da zuwa kano da taimakon Malam Hamza suka je kasuwa sukayo siyayya, shagon suka cika makil da kaya kama da Masara, gero, dawa, mai, kayayyaki dai kala kala, lokacin da komi ya kammala a shagon, kuka kawai Abubakar yayi dan tinowa da rayuwarsa da ya tashi mutuwa ta musu yankan kauna, da ace bai sira da ragowar kudin nan ba ma da baisan yazai yi ba.


      Satin su biyu da zuwa Abubakar ya saka Umar a makarantar kudi, cikin hukuncin Allah ya fara karatunsa a ka saka shi a jss1, lokacin da zaayi jamb, Abubakar ma yayi, cikin hukuncin Allah ya samu admission a Bayero universty, bangaren Business administrtion.


      Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu da dadi gobe ba dadi har Abubakar ya shiga level 3 yayin da Umar kuma ke ss1, sosai Abubakar ke jin dadin zama da malam Hamza domin ya rike masu komi bisa amana, sannan duk sanda Abubakar da Umar ke makaranta shi ke zama a shagon, sosai suke sanshi.

      Abubakar kam kulawa yake bawa Umar ta musamman, Umar kan ya dauki yayan nasa matsayi uku ko ma fiye da haka uwa, uba, yaya kuma abokin shawara.



     Duk sanda suka tina iyayen su sukanyi kuka, suna tina gatan da suka samu duk da cewa kullum cikin godewa Allah suke da basu sha wuya sosai kuma suna samu sosai a kasuwancin su dan su suke ciyar da Iyalan Malam Hamza.


        *KATSINA*

      Kwanan su Abubakar biyu da tafiya Alhaji Nazifi ya kawo ma yaransa biyya, gidan margayi usman ya fara zuwa, yaga sababin mutane nan yake samun labarin cewa an sai da gidan, chmst din Usman ya shiga dudubawa, wasu sum rufe, wasu sun fara sai da wasu abubuwa da ban, tin da ya ga haka jikin sa ya kara sanyi sosai.

      Kasan cewar yasan gidan su Adamu chan ya nufa, lokacin da yayi sallama da su yace yazo ganin yaransa nan suka shaida mashi sun kore su saboda basu da halin da zasu rike su, takaici ne ya hana Alhaji nazifi magana ya tafi ya kamo hanyar kano.


     *KANO*

     Lokacin da ya dawo yaso ya kaisu kara, amma kuma bashi da hujjar da zai dogara da ita, hakan yasa ya cigaba da addu'a har Allah ya bayyanar da yaran kuma duk bayan shekara dai dai yakan komawa katsina ko Allah zaisa an samu labarin su.


     Kwanci tashi ba wuya wajen Allah Abubakar an shiga level 4 Umar kuma na ss2 amma anan zai zana waec bazaiyi ss3 ba, sosai Umar ke samun kulawa, duk wani abu da Umar keso Abubakar na kawo mashi dan bai san abinda zai bakanta ran kanin nashi, shima Umar na san yayan nashi domin kuwa ya dauke shi tamkar uwa, uba, yaya kuma abokin shawara, bashi da aboki sai yayansa, shi ke mashi karatu in sun dawo gida.



     Kamar kullum suna zaune a kofar shagon su Abubakar na koyawa Umar acconting, wata mota ta gifta ta wajen su, sai kuma ta dawo, duk ba su lura ba, jin kamar tsayuwar mutum akan su yasa suka dago kansu mutumin ne ya furta "Abubakar ina ka shiga, yaushe ka zo kano, kuma me kake a kano, wajen wa kazo, me yasa baka neme ni ba bayan kazo kano?" Ya jero mashi tambayoyi yana kallonsa, cikin nutsuwa Abubakar yace "uncle ina wuni?" Lpya lau" ya fada a takaice "ban amsar tambayoyina Abubakar, naje garin ku amma baku nan, yayan baban ku sunce sun kore ku? cikin takaici Abubakar ya bawa uncle labarin komi, tin daga barin su gidan har izuwa yau, sosai uncle ya tausaya masu kallon sa yayi rai a hade "amma mi yasa baka nemeni ba da kazo kano, duk sawon shekarun nan da nake ta addu'a kullum da tunanin ku nake rayuwata ashe kuna kusa da ni ina *tsamiyar boka* ina *yan dodo* amma ka kasa nemana" uncle bakin neman ka nayi ba, nayi tinanin kaima zaka gujemu ka kore mu kamar yarda yayan mahaifan mu suka mana" girgiza kansa yayi "ba duka aka taru aka zama daya ba, nasan ajalin su ne yayi amma kullum ina ganin kamar nine silar mutuwar su da basu zo ba da basuyi hatsari sun mutu ba Abubakar ko dukiyata da na mallaka gaba daya zata kare akan ku bazan taba gajiya da ku ba bare na kore ku" kallon sa ya maida ga Umar da tin da suke magana yake kallon su "ba dai Umar ne ya girma haka ba?" Murmushi Umar yayi yace "nine uncle ina wuni?" Lpya lau, ku shiga ku debo kayan ku mu tafi gidana" zaro ido Abubakar yayi "Uncle ai bamuyi sallama da masu gidan ba sannan ba mu hada kayan mu ba ka bari zuwa gobe sai kazo ka dauke mu" girgiza kansa yayi "kafa ta kafar ku yau din nan" murmushi sukayi suka shiga suka yima Malam Hamza bayani, fitowa yayi suka gaisa da Uncle sannan suka yi sallama da shi bayan sun mallaka mashi kayan shagon halak malak, kudi sosai Uncle ya kara mashi akan ya kara jari, godiya sosai Malam Hamza yayi sannan ya godewa Allah da ya kawo masa yaran cikin rayuwar sa.


'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now