47

965 71 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

  

                4⃣7⃣

       Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba ganin pills wanda aka rubuta ECP baro baro a jiki, "ECP", ta maimaita sunan a hankali kafin cikin rawar jiki ta dau wayanta ta shiga  opera mini tana dubo ma'anar abinda ta gani.



     Tana dubawa taga an rubuto mata (Emergency Contraceptive Pill are high dose birth control). Wani jiri ne ya soma dibanta wanda yasata dafe window din da take tsaye a jikinshi.



  

     Kalma biyu kawai ke ringing a kanta "birth control", hawaye ne taji ya taro a idonta a hankali ta koma kan dressing mirror ta duba kwalin da kyau, indai idonta ba karya yake mata abinda taga yana hadiya kenan kafin ya sadu da ita.




       Zama tayi kan kujerar da ke wurin tana girgiza kai wani abu nace mata taje tayi confirm karta shiga hakkinshi kila ba pills din hana haihuwa bane. Kaman wacce aka tsikarawa allura ta tashi ta shiga dakinta ta dau mayafi ta fita.




         Wani chemist taje wanda yake kasar unguwarsu ta shiga taga yaron aikinshi ne tace " sanda aiki", "yauwa, sanda zuwa", ya amsa mata yana kallon yanayinta yanda take a firgice, "dan Allah ina me gidanka", ta tambaya ya nuna mata bayanta ta juya ta hango me gidan zuwa.




      Tsayawa tayi har ya karaso suka gaisa sama sama sannan ta nuna mishi abinda ke hannunta tace " dan Allah explain zakamin, maganin me wannan?", shiru yayi yana kallon maganin yana kallon yanayinta. Ganin shi take jira yasashi cewa "hajiya a gaskiya ECP maganin hana daukar ciki ne, mata nasha, maza ma nasha, amma in mace tasha yafi aiki saboda akwai 95% possibility na cewar bazata dau ciki ba, shi namiji in yasha yana kashe mishi sperm ne kafin yayi release saboda haka akwai 75% possibility na cewar matar da ya sadu da ita bazata dauki ciki ba".





       Banda " inna lillahi was  inna ilaihi raji'un", ba abinda ke fitowa daga bakin Marwiyya, hawaye ne kawai ke sintiri akan kumatunta kaman an bude fanfo. Me shagon ne yace "hajiya lafiya dai ko", girgiza mishi kai kawai takeyi da kyar Kalmar " nagode", ya iya fitowa daga bakinta ta fita daga shagon ta kama hanyar gida tana ganin jiri.




        Ikon Allah ne kawai ya kaita gida lfy, mai gadinsu kanshi kallonta yakeyi yana cewa "hajiya lfy dai koh?", amma ko alamar jinshi batayi ba. A parlour ta zauna dan kafafunta bazasu iya kaita sama ba, hannunta duka biyun ta dafe kai dashi tana sakin wani gunjin kuka mai ban tausayi, banda " Abdul ka cuceni", ba abinda ke fito daga bakin ta dan yau babu yayan ma, Abdul take kira kai tsaye.




      Shikuwa Abdul tinda yaje office hankalinshi ya kasa kwanciya dan ya kira Marwiyya yafi a kirga amma shiru ba'a dagawa, gabadaya hankalinshi yayi gida amma kuma sunada meeting karfe biyu da rabi shiyasa baze iya zuwa gida ba.







        A bangarensu Deen tin cikin dare Amatullah ke fama da zazzabi wanda ya kwantar da ita lokaci daya, banda amai ba abinda takeyi, Deen yaso kaita asibiti amma ta kiya tace ya bari gari ya waye.   A haka ya hakura ya zauna yana dubata har tayi bacci wanda shi bema samu baccin ba.




       Da safe seda ya mata wanka shima yayi ya dauko mata hollandia yoghurt tasha saboda kar suje hospital da empty stomach sannan suka fito. A hospital gwajin farko ya nuna musu tana dauke da ciki har na tsawon wata biyu da sati biyu, murna a wurinsu baya misaltuwa barinma Deen daya kasa rufe 32 dinshi. Seda suka karba magunguna sannan suka koma gida tace taliya da mai da yaji takeson ci, ya dafa mata ta sha magani.

Kallonshi tayi tace "bazaka office ba", girgiza mata kai yayi yace " zan kirasu in fada musu bazan samu zuwa ba", girgiza mishi kai tayi tace "a'a, pls kaje, I will be fine, ni bacci ma nakeji", kada mata kai yayi ya taimaka mata suka hau sama ta kwanta, yana zaune gefenta hannunshi daya ya rike nata dashi dayan kuma na kan cikinta har tayi bacci da murmushi a fuskarta.  Peck ya mata  a goshi da kan cikinta kafin ya furta " I love you both", sannan ya fita yana ja mata kofa, dakinshi ya shiga ya shirya ya dau briefcase dinshi ya fito ya shiga mota se office.


     Shima dai a ranan suku suku ya wuni dan duka tunaninshi nakan Amatullah da halin da ya barta ciki. Lokacin tashinsu nayi ya fito waje inda yaga Abdul cikin sauri shima zashi gida ya tsayar dashi fuskarshi dauke da murmushi yace "Abdul na kusa zama Dad", kallonshi Abdul yayi yana meditating maganan da Deen ya mishi kafin ya dago da sauri yace " kana nufin Amatullah nada ciki", daga mishi kai Deen yayi bakin yaki rufuwa Abdul yace "I'm happy for u bro", shima yana magana yana murmushi kaman wanda akacewa Marwiyya ce keda cikin.  Sallama sukayi Abdul yace " zuwa dare zezo ya duba Ama din ", da haka duk suka shiga motocinsu suka dauka hanyar gida.



TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now