50

1.3K 78 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

  

                5⃣0⃣


       Abdul na fita yayi gidan sa, cikin tashin hankali da gaganci yake tuki har ya isa gida, ko gyara tsayuwar motar baiyi dai dai ba ya fice yayi cikin falo, dur kushewa yayi kasa yana zubda hawaye, "me yasa zaki mun haka, ina sanki, babu wadda nake so sai ke, amma kika sa na sake ki" nan ya dinga surutan shi shi kadai ganin babu inda zai kaisa yasa ya haye sama, dakin ta ya shiga ya kwanta bisa gadon ta yana rera kuka tare da kallon hotunan ta dake jikin wayar sa a haka bacci ya sace sa.

       Deen na fita ya kaita asibiti, cikin gagawa suka amshe ta, suka shiga da ita, kasa zama Deen yayi yana ta zagaye zagaye, yana addu'ar Allah ya tashe ta lafiya, nan ya dinga jin tsanar Abdul a zuciyar sa, ganin likitan ya fito daga dakin yayi saurin tarar gaban sa "Doctor lpya me ya sameta" dafa shi likita yayi yace muje office na maka bayani.

         Bayan sun shiga office din yayi mashi nuni da daya daga cikin kujerun office din ya zauna, a hankali ya fara yi mashi bayani "Ba wani abu ke damun ta ba ila damuwa, kuma damuwan yayi mata yawa sosai wanda mudum ba'a kiyaye shigar ta damuwa ba komi zai iya faruwa da ita" dafe kansa Deen yayi yana mai tausayawa tilon kanwar sa, kila ma tin da tai auren bata taba samun kwanciyar hankali ba, amma shi yana chan yana ta faman kula da kanwar sa.


      Likitan ne ya katse mashi tunani ta hanyar furta "tunanin me kake yi?" Murmushin karfin hali yayi yace ba komi likita, zan iya shiga dakin?" Eh zaka iya zuwa safiya ma za'a sallame ku, saboda za a mata karin ruwa leda hudu ne kan safiyar" toh Allah ya kaimu ya fada yana mikewa.

        Dakin da Marwiyya take ciki ya shiga, kujerar kusa da gadon ya zauna, fuskar kanwarsa yake kalla, nan ya gano ramar da tayi kamar tayi jinyar shekara guda, hawaye ne suka fara zarya a cikin fuskar sa, da kyar ya samu ya nutsu.

       Ama ce kwance jikin Mumy tana kuka tace "Mumy dan Allah ki bawa yaya hakuri, wallahi in ya sake ni mutuwa zanyi, ina san sa kuma babu abinda na mashi kawai laifin ya Abdul ne ya...." Kuka ne yaci karfin ta, hakan yasa ta kasa karasa zancen da zata yi.

       Hawayen da suka zubowa Mumy ta goge, "kiyi hakuri Ama bazai sake ki ba insha Allah" toh Mumy Allah yasa.

        Kiran sallar mangariban da akayi yasa Deen fita dan yayi sallah, bai dawo ba sai da akayi isha'i sannan ya shiga karamin super market dake kusa da Asibitin ya siyo masu abinda zasu bukata da safe sannan ya shigo, sai a lokacin ya tuna da wayarsa ke cikin mota, zuwa yayi ya dau wayar sannan ya shiga dakin da Marwiyya ke ciki.

      Missed call ya gani guda Ashirin, biyar na Mumy, biyar na Dady , biyar na Ama, uku na ummy sai biyu na Abba, lumshe idon sa yayi da tinanin Wanda zai fara kira.

       Number Abba ya danna, bugu uku ya daga tare da sallama bayan sun gaisa Abba yace "kana ina ana ta kiranka" Abba ina asibiti ne kuma ban kusa da wayan, waye ba lafiya "Dady Marwiyya ce" Abdul din ya sake ta" runtse idon sa yayi saboda yadda yaji zafin maganar "Eh Abba" toh muna nan tafe da safe insha Allah" toh Allah kawo ku lpya" nan sukai sallama.

       Kan ya kira Dady ya riga shi kira, nan suka gaisa yayi mashi ya mai jiki sannan sukai sallama, Ummi ya kira ya shaida mata suna asibiti zuwa safiya zasu dawo kar su zo" toh tace mashi ta kashe wayan, yana gama wayar ya kashe wayar gaba daya dan baiso a dame shi.

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now