20

1.1K 86 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


                2⃣0⃣

       Sanda Hanan taji lbrn auren Abdul nan da wata shida kuka tayi sosai kaman ta cire ranta ta huta.



      Kwance take a daki duk tayi laushi kaman bata ita ba, iyayenta da cousin dinta Rufaida sosai suke tausaya mata saboda Hanan yarinya ce da maza basa gabanta.



     Amma gashi yau da bakinta tace ga wanda takeso, ga wanda ya mata, amma sedai kash! ta makaro.



      Hawaye ne kebin gefen fuskan ta a zuciyarta tace "I don't think I give up so soon, tinda Dad ne yaje yama Daddyn shi magana kila ma shi Abdul din besan da magana ta ba, saboda haka ni zanje na sameshi da kaina in fada mishi abinda ke raina kila nayi dace".



      Da wannan tunanin ta tashi ta fada bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata atampa super holland ash wanda yasha aiki da stone work me ratsin baki a jiki, sannan ta zauna ta tsantsara kwalliya, jaka da mayafi da takalmi ta dauko duka black sannan ta feshe jikinta da turare ta fito.



    Mamin ta na ganin ta tace " ina zuwa haka Hanan?", "Mami zanje na gwada sa'a ta ki min addu'a", duk da Mami bata gane abinda take nufi ba amma setace " Allah yasa a dace", "Amen Mamina se na dawo".



      Da haka ta fita ta tare napep basu tsaya ko ina ba se gaban company din, biyan me napep din tayi sannan ta juya ta shiga.



    Wurin receptionist din taje ta mata sallama ta amsa tareda cewa " how may I help u", "plss ma I'm here to see Abduljaleel Umar", " do u have any appointment with him?", "no I don't", " okay Abduljaleel is having a meeting which will last for half an hour, if u can wait then pls sit there", da sauri tace "sure ma'am I  will wait".



       Zuwa tayi ta zauna banda addu'a ba abinda takeyi na Allah yasa ta dace, a haka har kusan awa daya tana zaune sannan taji receptionist na waya tana cewa " Yes sir, no, a female", alama tama Hanan da hannu akan tazo sannan tace "ur name", " Hanan Muhammad Sani", nan receptionist din tace "Hanan Muhammad Sani, ok" ajiye wayan tayi tace "u can go in, his office is on the fifth floor", " thank u" tace wa matar sannan ta shiga lift wanda ya tsaya a fifth floor sannan ta fita.



      Office biyu kawai ne a floor din, daya and rubuta 'ZAHRADEEN ABUBAKAR' da manyan letters dayan kuma 'ABDUL JALEEL' gabanta ne ya fara faduwa tayi addu'a kafin ta kwankwasa daga ciki taji yace "come in".




       Seda taja wani dogon numfashi sannan ta bude ta shiga office din ya tsaru iya tsaruwa, kanshi na kan wasu files yana dubawa ya dago ya kalleta. Kallo daya ya mata yaga kamannin su da co worker dinshi Adnan Muhammad Sani, nuni ya mata da kujera alaman tazo ta zauna ta karasa cikin rangwada ta zauna tana kare mishi kallo.




      Ita se yanzu ma taga kyawunshi sosai dan last time data ganshi ganin nisa tamai, clearing throat dinshi yayi ganin kallon bame karewa bane yace " welcome, wat can I offer u", da sauri tace "oh no nothing I'm ok", yace " toh shikenan, meke tafe dake", sunkuyar da kanta tayi tace "actually dama wurinka nazo, da fatan abinda zan fada ma yanzu baze batama rai ba?".



     Girgiza kanshi yayi yace " baki fada ba tukun ballantana nasani ko ze batamun rai ko baze bata", da sauri tace "bazema bata ba", kada kanshi yayi yace "ok, can u get straight to the point, as u can see I'm busy".



      Cikin sanyin murya ta fara " em, dama dama", "can't just get it straight", gyara nutsuwar tayi tace " dama tin randa akayi bikin bude company din nan na ganka kuma naji ka kwanta min har cikin raina, shine nace in bazaka damu ba can we  be lovers".




      Tinda ta fara magana ya hade rai a zuciyarshi yace "bama friends ba", kala bece mata ba, wayanshi taga ya dauko ya kunna ya mika mata. Wallpaper din ta kalla wanda hoton shida Marwiyya ne akai, a zuciyarta tace " na bani, wannan ai ko kafarta ban kamo a kyau ba, yanzu ya zanyi?", katse mata tunani yayi da cewar "wannan da kike gani itace wacce zan aura, kuma ita kadai nakeso tin ina dan karami na, da sonta na rayu sannan kuma banda sha'awar mata biyu, saboda haka I'm sorry to say I decline ur offer".



        Runtse ido tayi dan jin kalmominshi tayi kaman mashi yake soka mata a kirji, hawaye ya gani a idonta seta bashi tausayi amma wannan besa ya canza ra'ayinshi ba sema cewa da yayi " mikomin waya ta", mika mishi tayi ta tashi ta fita dan haushi da takaici ko sallama batamai ba, shikuwa binta kawai yayi da ido.......



Manage dis pls, yau da ciwon kai na tashi.




TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang