58

1.1K 84 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

       

            5⃣8⃣

         Cikin Ama ya shiga watan haihuwa, ga cikin ta ya girma sosai duk da kumbura musamman kafafuwan ta ko tafiya bata iyayi

       Ama ce kwance kan kujera sai kuma Marwiyya da ke gefen ta tinda cikin ta ya shiga watan haihuwa ita ke zama da Ama idan Deen ya tafi office

       "Sistoo wallahi marata bakiji yadda yake yi ba har yafi azaba lkcn da nake yi duk wata" murmushi Marwiyya tayi "Daman yaushe za a hada ciwon nakuda dana period, dole da banbanci"

       Ama zata yi magana kenan cikin ta ya kulle sakkowa tayi daga kujerar ta durkushe a kasa" cikin sauri Marwiyya ta ruko ta sannu Ama bari naje na dakko maki hijab

      Daki ta shiga ta dakko hijab ta sawa Ama ita ma ta saka ta kama ts suka fice tinda driver ya hango su yayi saurin mikewa yaje ya bude masu suka shiga shi kuma ya bude gaba ya shiga ya ja suka wuce Asibiti


      Suna shiga asibitin aka karbeta cikin gagawa ana shiga da ita Marwiyya ta dakko wayan ta dan ta kira Deen

     Yana zaune a office yana signing wasu takaddu wayarsa tai kara ganin litle Sis yasa yayi saurin dagawa "little ya akayi"

     Cikin muryar damuwa tace "yaya Ama ba lafiya muna asibiti an shiga da ita" wane asibitin kuke" Aminu kano" owk gani nan"


      A kofa suka ci karo da Abdul zai shigo, nan ya shaida mashi Ama na asibiti nan suka wuce asibitin bayan kowa ya shiga motar sa
  

      A harabar asibitin suka tadda ta tana ta zagaye cikin sauri Deen ya karaso wajen ta "sistoo" da sauri ta karasa wajen sa ta fada kirjin sa, kukan da take so tayi tin dazu ta kasa shi ta fara yi

       Sosai hankalin Deen ya kara tashi, Abdul ma da yake gefe su kamar ya dagota ya dawo da ita kusa dashi

     "Sistoo kiyi hakuri kukan ki kara daga mun hankali zaiyi" cikin kuka tace "yaya hankali na ba zai kwanta ba sai Ama ta fito" zata fito yanzu insha Allah" Abdul kuwa kallon su yake kamar yayi kukan sai kallon Marwiyya yake amma taki kallo sa

      Cikin fara'a wata nurse ta karaso inda suke "kune kuka kawo Amatullah" cikin sauri su duka suka amsa da eh, murmushin ta ya kara fadada "congratulation ta samu baby girl" Alhamdulilah, Abinda suka fada gaba dayan su" yanzu zaku kawo kaya da za a gyarata ita da babyn" cikin farin ciki Marwiyya tace toh" mota ta koma ta dakko kayan sannan ta kawo ma nurse, har zata tafi Deen ya zaro kudi ya bata kan ta mashi godiya Abdul ma ya zaro ya bata, zo kuga bakin ta yadda yaki rufuwa tana ta masu godiya ta wuce dakin bayan ta adana kudin ta

       Abdul ta kallah "yaya ka kira gida ka fadawa su Mumy" har lokacin tana rike a wajen Deen, "toh kawai ya ce mata ya dakko wayan ya fara shaida masu

     Ana fito da baby Marwiyya ta karbi yarinyar cikin so da kauna ta rungume ta Allah ya rayaki baby na" nan ta mikewa Abdul yarinyar shima yay ta kallon ta cikin so da kauna sai da ya gama kallonta ya mikawa Deen suna nan tsaye akazo aka wuce da Ama zuwa dakin hutu

      Lokacin da su Ummi suka zo lokacin Ama ta tashi daga bacci hakan yasa suka shiga dakin gaba daya tana jingine jikin gado, kusa da ita Marwiyya ta zauna "sis ya jikin" murmushi tayi "jiki yayi sauki" nan gaba daya suka dubata sannan suka mika mata babyn da take ta kuka dan ta bata mama, kunya ce ta kama Ama da kyar ta bata, Mumy kan a ranta dadi take ji wai yau Ama ce mai jn kunya


      Karfe shida aka sallame su daga asibiti family house din su suka nufa, bangaren Ummi aka kaita ruwwn wanka aka dafa sannan ummi ta shiga da Ama ta mata wanka ita kuma Mumy tayi ma Babyn wanka

     

      Abdul suna dawo wa dakin sa ya nufa wanka yayi sannan yayi alwala saboda kiran sallar da aka fara sannan ya fito a masjid suka hadu da Deen shima yayi wanka, basu baro masallaci ba sai da akayi isha'i, nan suka hango su Dady suka je suka gaisa sannan suka nufi cikin gida

        A parlour suka tadda su gaba daya suka zauna suka dan taba hira sannan suka je dining dan yin dinner, idon Abdul kan na Marwiyya har suka gama


       Bayan an gama dinner Abdul ya koma bangaren sa Marwiyya Ama, Deen na zaune a dakin Ummi suna hira wayar Marwiyya tayi Kara ganin Abdul ne yasa ta dauka "ki same ni a daki na yanzu" bai jira cewar ta ba ya kashe wayan

       Tashi tayi ta tafi dakin ta ta sako hijab kan rigar da ta saka ta bacci, taci sa'a babu kowa a parlour hakan yasa tayi dakin Abdul


       A hankali ta tura kofar dakin yana kwance bisa kujera idon sa a lumshe, tura kofar tayi ta rufe sannan ta karaso inda yake ta zauna a gefen kafarsa

   

         Bude idon sa yayi ya kalle ta, itama din shi take kallo, tashi yayi ya matsa inda take jikin su na gogar juna

        "Yau baza ki bar kofar a bude ba" dariya tayi saboda tuno lokacin da ta bude kofar, shagala yayi da kallon yadda dariyar tayi masifar yi mata kyau

        Ganin yadda yake kallon ta yasa taji kunya ta kwantar da kanta a kirjin sa, dora hanunsa yayi a kanta "ina sanki baby na ina san komi naki, amma cire hijab din nan" ya fada yana kokarin cire mata

       Ba tayi mashi masu ba ya cire mata, idon sa ya sauka akan kirjin ta da suke rikita mashi lissafi, a hankali ya zura hanunsa cikin rigar yana wasa da su

        Sosai hakan yayi ma Marwiyya dadi Wanda hakan yasa itama ta Dora bakin ta kan nashi ta fara tsotsa


        Nan da nan ta kara rikita mashi lissafi sun dade suna rmcn juna sannan ya kyale ta "baby a nan zaki Kwana koh, ban san kiyi nisa dani ko kadan


      Turo bakin ta tayi " gaskiya yaya kayi hakuri bazan iya Kwana ba" toh saboda me baza ki Kwana ba, miye a ciki nifa mijin ki ne" duk da haka amma kayi hakuri bazan iya Kwana ba"

      Hade fuska yayi "shikenan tashi ki bani waje tinda baza ki Kwana ba"

       Ba musu ta mike ta tafi bayan ta saka hijab din ta, da ido ya bita lalaima ma bata damu dashi ba kenan shine zata fita, sosai ransa ya baci

      Tana komawa ta shige dakin ta, kwanciya tayi cike da kewar mijin ta,

        Washe gari Abdul bai fito ba sai karfe goma lkcn har sun gama break fast su Dady sun fice aiki, Deen ma ya fita, cikin shirin sa na tafiya office ya shigo parlour ya gaida su Ummi, sanda Marwiyya ta gaida sa ciki ciki ya amsa sannan yaje yaga Ama da babyn ta ya fito, sanda Mumy tace yay break fast yace ya makara office zai karya


        Har yaje kofa ya juyo ya cewa Marwiyya ta shirya in ya dawo zasu tafi bai jira cewar ta ba ya fice office




TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now