43

1K 81 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


Ina mai baku hakuri akan kuskuren da aka samu a last page, instead of page 42 muka sa 41, mistake ne last page ne 42 wannan 43.


               4⃣3⃣


       Washegari su kawu Ahmad da kawu Adamu suka tafi su da iyalansu gida ya rage su Abba kawai, duk kewan yaransu ya ishe su.



      Deen ne zaune a daki da laptop a gabanshi yana aiki saboda gobe zasu koma office Ama ta shigo ba tareda sallama ba ta karasa ta zauna gefenshi.



     Dagowa yayi ya kalleta yace "baki iya sallama ba ko", ta shagwabe fuska tace " mantawa nayi My D", ya kada kai sannan ya maida hankalinshi kan abinda yakeyi.




      Shiru tayi tasa yatsa a baki tana cin farce, tinda yaga haka yasan cewa da magana bakinta amma ya kyaleta har seda ya gama sannan ya kashe laptop din ya juyo tareda riko hannunta yace "baby na ya akayi?", sunkuyar da kai tayi dan batasan ta ina zata fara gayamashi abinda ya kawota ba.




      Hannu yasa ya dago habarta yace " kalleni nan ki fadamin me kikeso", kallonshi tayi cikin i'ina tace "My D, dan Allah ka janye maganan karatu na, banso nayi, nafiso na zama full time house wife".




      Cike da takaici yake kallonta sannan yaja wani dogon tsaki ya mike ya shiga bathroom ya barta wurin, dama tasan za'a rina shiyasa tinda farko take tsoron fada mishi amma kuma ita harga Allah karatun nan baso take ba, secondary din ma dayaya ta gama za'a wani ce mata university.





       Tana kallo ya fito daga wanka yana shiryawa ba tare da ya kalleta ba, mikewa tayi ta bude wardrobe dinshi ta dauko mishi shirt da jeans trouser amma ko kallon kayan beyi ba ya dauko wani yasa.





       Makullin mota ya dauko ze fita tayi saurin tareshi tareda cewa " My D bakace komai ba", wani kallo ya mata yace "kinada kai?", kallon dani kake take mai yace " kinyi shiru, tambaya nayi kina da kai?", tace "da banda kai zan tsaya nan", murmushin takaici yayi yace " toh matsa na wuce", "fushi kakeyi dani?", ta tambaya cikin sanyin murya yace " toh ya kikeso nayi, so nawa ina miki magana kan karatun nan, so nawa ina fahimtar dake amma kinkasa fahimta, shine yanzu kuma zaki sake zuwa da maganan nan".




      Sunkuyar da kai tayi tace "My D ni karatun ne banaso", ta fada a hankali tareda dago kanta dan taga reaction dinshi, rasa abin fada yayi dan besan me zaice mata ba koma.




      "Baby meyasa bakyason cigaban ki, bakisan cewar karatun nan cigaban ki bane, bakyaso nan gaba muyi alfahari dake, haka kikaga Marwiyya nayi?", shiru tayi yaci gaba da cewa " zan baki lokaci kiyi tunani dan bazan takura miki akan abinda bakyaso ba, amma inaso ki sani karatun nan dazakiyi baze amfane ni ba, ke karatun nan ze amfana saboda haka kiyi tunani da kyau", yana kai nan ya bude kofa yayi ficewar shi, ita kuma ta zauna kan gado tana kallon kofa.





        "Swthrt har na fara missing dinki", cewar Abdul dake zaune a parlour ya daura Marwiyya kan cinyarshi, " missing dina kuma?", ta tambaya cike da neman karin bayani yace "basan ya zan kai yamma babu ke ba gobe, ji nake kaman karna koma office", se yanzu ta gane inda zancenshi ya dosa.




       Murmushi tayi tace "nima zanyi missing dinka sosai, saboda haka duk sanda kayi miss dina ka dau waya ka kirani, nima zan kira duk sanda nayi miss dinka", hancinta yaja tareda cewa " hakan zamuyi tawan".





       Jin ana kiran sallah ne yasasu mikewa shi ya fita itakuma ta haura sama danyin sallah. A masallaci ya hadu da Deen bayan an idar da sallah yace "mutumi na lfy na ganka haka", ajiyar zuciya Deen ya sauke kafin yace " wlh bansan yadda zanyi da Ama akan maganan school dinnan ba, kwata kwata batason karatun, nayi mata magana har na gaji amma haryanzu tana kan bakanta na batason karatu", murmushi Abdul yayi yace "Amatullah rigima, ka bari zan mata magana mugani koh zata saduda", " shikenan toh, bari na shiga ciki dan fita nayi, dawowa na kenan", cewar Deen yana mikawa Abdul hannu, "Ok toh, ka gaishe ta zuwa yamma zan shigo", " seka shigo", cewar Deen yana kokarin bude gate, iska Abdul ya furzar tareda furta "Amatullah", sannan ya kada kai ya shiga gida.





TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now