48

991 71 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*



               4⃣8⃣

         Ganin kukan babu inda zai kaita yasa ta Shiga daki ta janyo akwati daya, kayanta tafara hadawa a ciki, sai da ta cika akwatin ta rufe, dan yau babu abinda zai sa bata koma gida ba, sai dai koh me za a mata ayi mata, bayan ta gama ta fito falo zaman jiran dawowar sa


         A hankali ya turo kofar tare da yin sallama, ganin ta hada kai da gwiwa yasa yay saurin karasawa inda take "baby lpya, me ya sameki?" Ya jero mata tambayoyi cike da tashin hankali

      Dago rinanun idanun ta tayi ta sauke su a fuskar sa, "ka cuce ni Abdul, ka cuci rayuwa, kuma bazan yafe maka ba" jin yadda ta kirasa da sunan sa babu ko yaya yasa shi Shiga mamaki, tabbas ba karamin damuwa take ciki ga, maganar tace ta katse mashi tunani


       "Meye wannan,daman shine abinda ka ke sha kullum, in kasan baka shirya haihuwa ba meyasa zakai tarayya dani" ganin abinda ta tunana mashi duk sai yaji ba dadi, amma wannan bai kai abinda zatai fushi haka ba


       Murmushin takaici Marwiyya tayi tare da mikewa, "daman nasan dole ka rasa abin fada domin kasan ba ka kyau...." Kan ta karasa ya mike tare da ruko hanunta "Baby kiyi hakuri na san ban kyauta ba, amma wannan bai kai abinda zakiyi fishi saboda shi ba"

         Murmushi tayi "a wajen ka ba, kai da baka san darajar kanka ba, toh wallahi bazan iya daukan wulakancin ka ba dole ka sake ni dan bazan zauna da Wanda a wajen sa aikata Sabo ba komi bane"

         Cikin bacin rai yace "toh an fada maki daman in bake bazan iya rayuwa bane, da har kike ikirarin na sake ki, kin san a yanzu na sake ki gobe zan iya auro wadda zata fitar dani kunyar abokanai na"



        Cikin bacin rai tace "matsalar kace wannan ba tawa ba, abinda na sani kawai dole ka sake ni Abdul ko ka ki ko ka so" ta fada tana fizge hanun ta, ta haye sama cikin takaici

        Kiran sallar da yaji an fara ne yasa ya shige daki ya dauro alwala, ya wuce masallaci, yana fita masallaci ta dakko akwatin ta ta fito waje mai gadin su na mata magana bata bi ta kan sa ba ta fice


        Tana fitowa ta ci sa'a mai napep ya sauke wasu kwatan ta mashi inda zata je tayi ta shige ya ja suka tafi


        A bangaren Ama kuwa bayan ta tashi daga bacci taje tayi brush sannan tayi wanka saboda wani azababen zafi da take ji, bayan ta fito bata shafa komi ba ta saka wata riga iya gwina wandan ma da kadan ya wuce rigar, ice cream tai sha'awa gashi babu a gda hakan yasa ta fito waje dan bawa driver ya siyo mata bata damu da rashin dankwalin da kuma suturar da ke jikin ta ba

       A zaune ta taddashi shi da mai gadi suka gaida ta cikin girmamawa nan ta bawa driver sakon, har zata juya taji horn din deen hakan yasa ta tsaya

      Tin da aka bude gate din ya hangota wani malulun bakin ciki ne ya tokare shi, ko gama parkn din baiyi ba ya bude ya fito, lkcn da yayi dai dai da karasowarta wajen,


        Kallon da yayi mata ne yasa gaban ta faduwa, bata ankaraba ya ja hanunta yayi cikin gda da ita a parlour ya tsaya da ita fuskar nan tashi a hade yace


       "Ke wacce irin mara hankali ce, tinanin ki bai gaya maki wannan shigar da kikayi bata dace ba, kuma sabagen rashin hankali ki fita koh hijab babu"


        Cikin yanayin kuka tace "kayi hakuri bazan karaba, yinwa nake ji kuma babu abinda nake so sai ice cream hakan yasa na fita na bawa driver dan ya siyomin amma kayi hakuri" ta karasa maganar cikin kuka,

      Ganin yanayin ta yasa jikin sa yin sanyi "kiyi hakuri ki daina kuka, kishin ki nake yi wallahi, kwata kwata ban so na ga wani namiji ya ganki koh kadan"

        "Yaya kar ka ban hakuri, ni nai laifi ni zan baka hkri kawai kace ka yafe min" na yafe miki swt hrt muje nayi wanka" ya fada yana jan hanunta zuwa sama
  

      Marwiyya na sauka ta mikawa mai napep dari biyar tace ya rike, ya shiga jero mata godiya bata bi ta kansa ba ta wuce gida, a falo ta tadda Ummi da Mumy suna ganinta suka mike cikin tashin hankali "Marwiyya lpya, me ya sameki ina Abdul din?" Suka jero mata tambayoyin

        Kasa ta durkusa wajen kafar Ummi ta ruko kafar  Ummi ki min rai kicewa Abba bazan iya zama da Abdul ba ya sakeni, ku tausaya min" ta karasa maganar cikin kuka mai tsuma zuciya,

     Ummi kan rasa abinda zata ce tayi, dan tabbas kana ganin Marwiyya kasan tana cikin tashin hankali, Mumy ce tai karfin halin dagota "Marwiyya ki daina kuka ki fadan komi insha Allah wannan karan dole a bi miki hakkin ki"

         Cikin kuka Marwiyya ta fada masu komi sannan ta nuna masu maganin, gaba dayan su mutuwar tsaye sukayi, Mumy kan zama tayi tana sharar hawaye

       Bayan Abdul ya dawo daga masallaci ya nufi gida, ganin bata falo yasa ya nufi dakin ta, yana turawa yaji kofar a bude, ganin bata ciki ya kalli kofar bandaki a bude ya leka bata ciki

       Cikin tashin hankali ya nufi waje mai gadin ya tambaya yace "kaga fitar Marwiyya" eh yallabai amma..... Bai jira Mai gadi ya karasa maganar ba ya nufi gida da gudu dan ya dakko key din motarsa,

       Wayarsa ce tai kara ganin Mumy ce yasa gaban sa faduwa tare da dagawa "toh gani nan zuwa"

       Ama ce kwance kan cinyar Deen tana ta zuba shagwaba wayarsa tai kara ganin Ummi yasa ya daga "toh Ummi" ya fada yana sauke wayar, Ama je ki shirya Ummi tace naje ban san barin ki ke kadai" toh tace ta shiga ta sako hijab har kasa, shi kuma ya dau key din motar sa suka fice




   TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now