46

1K 79 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

                   4⃣6⃣

       Kwance take kan gadon ta, bacci take cikin kwanciyar hankali, da sallama Deen ya turo kofar tare da shigowa dakin, ba karamin bacin rai yayi ba ganin ta kwance amma ya danne.

      

         Zama yayi gefen ta tare da dukan hanun ta a hankali ta bude idon ta, ta sauke su kan Deen, murmushi yayi mata ita ma ta mai da mashi.

       "Swt hrt ya baki tashi ba, gashi kin kusa makara", turo karamin bakin ta tayi " wallahi My D yau na gaji ban san zuwa mkranta".

       Rarashin ta Deen ya fara yi amma yaga bata niyyar tashi hakan yasa ya dauke ta kamar baby ya kaita bandaki.

       Da kansa yayi mata wankan, haka ta dinga kunci har ya gama yi mata wankan ya fito da ita sannan ya shirya ta, sanda yace tayi break fast tace ta koshi dole ya kyaleta ya kaita makaranta.

         *BAYAN KWANA BIYU*

        Marwiyya ce zaune gaban madubi tana tsarawa kanta kwaliyya kasan cewar yau malamin da suke dashi yace bazai samu zuwa, sai da ta gama kwaliyyarta saf sannan ta fito parlour ta zauna tana jiran dawo war Abdul.

       Dariyar sa taji yana bude kofa yana magana, jin muryar mace a bayan sa yasa gaban Marwiyya faduwa.

      Yarinyar dake bayan sa tayi sallama tare da shigowa ciki, da kyar Marwiyya ta amsa sallamar,  ganin ta gane yarinyar Abdul ne yayi mata nuni da daya daga cikin kujerun parlour, bayan ta zauna shima ya zauna kusa da ita har jikin su na gogan na junan su.

      "Sannun da zuwa Rahma an wuni lpya" Marwiyya ta fada cikin dakewar murya, "lpya lau Amarya, ya amarci ban samu zuwa ba sai yanzu, hope dai ba ai fishi ba".

      Murmushin da bai kai zuci ba Marwiyya tayi "ba komi wallahi mun miki uziri" kallon ta tamaida ga Abdul tace "sannu da zuwa" murmushi yayi mata "yauwa babyna da har na kusa fishi baki kula ni ba" murmushi kawai tayi ta tashi ta nufi kitchen.

        Abinci da lemu ta kawo ma Rahma,bayan ta ajiye ta nemi wajen zama ta zauna, Abdul ne ya dakko kofi ya tsiyaya lemun ya mika mata, karba tayi tare da kurba ta ajiye.

 

       Bata fuska Abdul yayi kamar bai taba dariya ba yace "meye hakan zaki wani ajiye kisha ko na maki dura" ya fada cikin sigar kulawa, cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro tace "aboki na koshi fa wucewa zanyi ma yanzu".

         Shagwabe fuska yayi "haba dan Allah yanzu daga zuwa sai tafiya gaskiya a'a" nan fah ta dinga bashi hakuri tana rarashinsa akan zata dawo yanzu sauri take da kyar ya hakura.

        Marwiyya kan kallo ta bisu dashi kawai, takaici duk ya gama lulubeta amma ta rasa me zatayi, tana ji tana gani ya fice rakata, da kyar ta iya tatara nutsuwarta ta yi mata Allah ya tsare.

Abdul bai dawo ba sai bayan sallar isha'i, a parlour ya tadda Marwiyya na kallo, Wanda a zahiri kallon take amma kwata kwata hankalinta baya wajen.

      Kusa da ita ya zauna tare da janyo ta jikin sa "baby na ya gda" janye jikin ta tayi ta mike tayi dakin ta, tana shiga zata sa key shima ya turo kofar ya shigo.

    

     "Me aka maki baby, naga ranki a bace" hararsa tayi "au tambaya ta ma kake yi, wallahi yaya zan yarda da komi amma banda sabawa Allah, jibi yadda ka ke ta faman shigewa jikin ta kamar wata matar ka ko kuma kanwar ka, ka wani zauna sai shagwaba kake mata sai an tambaye ka kace kawar ka ce toh wallahi All......" Kukan da yaci karfin ta ne yasa ta kasa karasa maganar.

        Cikin tashin hankali Abdul yace "baby kiyi hakuri, zan iya jure komi amma banda ganin ki cikin kuka, ki daure ki daina kukan nan".

 

       Cikin sarkewar murya tace "yaya kana nufin zan daina kuka alhalin baka kishi na, yaushe zan daina kuka alhalin kana koyi da dabi'un da ba naka ba, yaushe zaka canza ka zama cikin *YA'YAN ASALI* yaushe zaka daina koyi da dabi'ar yahudawa, yaushe zaka dai........." Bakin su da Abdul ya hade waje daya yasa bata karasa maganar da zata yi ba, nan ya shiga lalubar ta, hakan yasa na fice na bar masu dakin.

       Kasan cewar yau lahadi ne kuma yana da aiyuka da yawa a office yasa ya zauna tin safe yake tayi a gida Marwiyya kuma na gefen sa jefi jefi suna hira, sai da lkcn girki yayi ta tashi taje ta dora, bayan ta gama akayi kiran sallah taje tayi bayan ta idar ta zauna kusa dashi "mine har yanzu baka gama ba gashi lkcn sallah yayi" eh wallahi so nake na idasa naje nayi sallar, Marwiyya dai bata kara magana ba dan ta lura dashi kwanan hada sallah yake yi.

       Abu kamar wasa har akayi la'asar bai tashi ba nan ma da tayi mashi magana yace ya kusa, ganin har biyar da Rabi yasa Marwiyya cewa "haba mine ba kasan ba kyau hada sallah ba ne, tin dazu fa nake maka magan........" Sawar da ya daka mata yasa tayi shiru.

       Nace ki kyale ni ina gama zanyi ko kin fini sanin dai dai ne an..... Bata jira ya karasa ba ta haye sama dakin ta ta shiga tare da rufo kofar kuka sosai ta sha, sai da akayi kiran sallah ta tashi tayi mangariba ta jira har isha'i sannan ta kwanta.

       Abdul kuwa tana shiga daki ya kasa karasa aikin kawai ya mike yayi dakin sa wanka yayi sannan yayi alwala ya fara jero sallar da ake binsa.

      Karfe goma bacci ya gagari Abdul kuma Marwiyya taki bude kofar, haka ya hkra ya nufi dakin sa yayi ta juyi har yayi bacci.

     Washe gari da wuri ya tafi office, sai  da ya tafi office sannan ta fito, bayan ta hada break fast taci sannan ta wuce dakin Abdul dan tayi mashi gyara, bayan ta gama har zata fita ta hango abu kan madubi, abinda ta gani be yasa ta zaro ido tare da furta inalilahi waina ilaihi rajiun".


TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now