42

1.1K 78 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

          4⃣2⃣

          Kiran sallar asuba ne ya tashi Abdul daga bacci, ganin yadda Marwiyya kwance a jikin sa yasa yayi mata pecking dinta yayi a goshi sannan ya kwantar da ita bisa pillow ya mike ya fice

       Yana fita itama ta mike tayi banda ki ta dauro alwala, raka'atul fajr ta fara yi sanan ta fara yin sallah

        Zahradeen kuwa bayan ya gama adduo'in sa ya hau gado tare da janyota Ama jikin sa a haka bacci ya kwashe sa

      Da asuba shi ya fara tashi sannan ya tashi Ama ya fice masallaci saboda ganin ya kusa makara

         Bayan an idar da sallah sun fito daga masallaci suka gaisa, Zahradin ne yace "Abdul jiya na kira wayan ka har kusan sau biyad amma baka daga ba lafiya"

       Cikin mamaki Abdul yace "Ayyya bro bana kusa, Marwiyya ce ta dagulan lissafi, tin da na ajiye wayan ma ban kara bin ta kan ta ba" kallon sa Zahradin yayi yace "kamar ya me ya hada Ku" bari kawai laifi ta mun amma ai har mun shirya" murmushin takaici Zahradin yayi sannan yace "ka dai dinga kulawa" nan sukai sallama kowa ya nufi gdan sa

       Abdul na shiga yayi dakin Marwiyya yaji kofar a rufe hakan yasa ya nufi dakin sa,

     Marwiyya na idar da sallah ta rufe dakin da mukulli, Bayan ta rufe dakin ta haye gado wayar ta dakko, zaro ido tayi ganin kiran yayan nata har guda biyar hakan yasa ta kira number sa

      Yana shiga gida dakin sa ya wuce tare da rufo kofar, wayar sa dakko dan kiran ta, sai ga kiran Marwiyya ya shigo ya daga tare da karawa a kunne

     "Assalamu alaykum" ajiyar zuciya ya sauke "waalaikumus salam" cikin sanyin murya tace "yaya ina Kwana" lpya lau kanwata" yaya jiya nayi bacci na ga kiranka yanzu" 

     Ajiyar zuciya ya sauke "daman kira nai naji me ya hadaki da Abdul? Me yayi miki?" Tambayar tazo mata a bazata hakan yasa ta fara inda inda sannan tace "yaya shi yace ma mun samu sabani? " a'a bai fadan ba ni naga hakan" a'a yaya ba abinda yayi mun"

       Murmushi Zahradin yayi "kice yanzu har kinyi girman da zaki fara boye mun damuwar ki kwata kwata guda nawa kike da zaki dorawa kanki damuwa da hawan jini " yaya ba haka bane babu fa abinda........."

     Sawar da ya daka mata ne ya sata yin shiru "kina tunanin zaki iya boyen damuwar ki toh wallahi Allah mudum baki fadan ba Allah akan Ama zan huce yadda ya kun ta ta miki Allah sai na kuntata mata"

      "Yaya ka duba girman Allah kayi hakuri zan fada maka kar ka huce kan sis bata san hawa ba bata san sauka ba" nan Marwiyya ta bashi lbrin komi har da zuwa wajen ta da yayi da daddare, sosai Zahradin yaji ba dadi amma yay ta mata nasiha tace ba komi nan yay ta janta da hira ba kyaleta ba har sai da ya tabbatar bata tattare da damuwa sannan yayi mata sallama

         Abdul kasa bacci yayi haka yay ta juye juye sai wajen 7sannan bacci ya kwashe sa,

      Karfe tara  Marwiyya ta fito ta hada masu break fast sannan ta koma tayi wanka ta shirya cikin wata atamfa Ash sosai tayi mata kyau

      Karfe tara ya mike ya shiga wanka ya shirya cikin wata jar riga mai karamin hannu sai 3quater baki, sosai ya bata lokaci wajen gyara kansa sannan ya fito falo,

       Ganin ta shirya komi akan dining yasa ya nemi gu ya zauna yana jiran fitowar matar sa

       A hankali ta fara sakkowa daga sama har ta shigo tsakiyar falon tin da ta fara sakkowa ya tsare ta da idanun sa, maganar sa ce ta katse mashi tunanin

        "Ina Kwana?" Ta fada ciki ciki ba tare da ta kalle shi ba, "lpya lau" ya fada a takaice dining ta nufa shima ya taho kujera ta ba zata zauna yayi saurin zama, bata tanka mashi ba ta ja kujerar kusa dashi ta zauna

     Plate ta janyo ta zuba abinci sannan ta hada tea iya nata ta fara ci, shiko tsare ta yayi da idanun sa komi take burge sa take ganin kallon yayi yawa ta galla mashi harara

       Dariya yayi yace "baby ni kike harara, banza ta mashi hannun ta ya ruko, " nasan nayi laifi amma ke kika fara bata mun kiyi hakuri bazan kara ba" fizge hanunta tayi "ni ka sake ni meye zaka ban hakuri matar da take da kima da daraja wadda kuma ake kishi ake bawa hakuri

      Lumshe idon sa yayi " baby kiyi hakuri baki fahimce ni bane, amma abun duk bai kai ayi fada ba kin san ban iya jure fishin ki ina sanki ina kaunar ki fiye da tunanin ki" nan dai Abdul yay ta tsara Marwiyya har sai da ya samu ta hakura sannan suka cigaba da cin abinci cikin so da kaunar junan su

*BAYAN SATI DAYA*

         Yau sati guda da auren su, soyayya suke nunawa junan su cikin kulawa, kawu Ahmad da kawu Adamu na ta shirin tafiya, basu koma ba saboda su Abba sun hana su komawa

     Yau ya kama asabar deen ne zaune bisa kujera Ama na jikin sa Abdul ya turo kofar dakin ya shigo, Kusa da kafar Ama ya zauna, "toh mage uwar san jiki kullum kina kwance a jikin sa ranar Monday dai zai koma aiki sai a koma kwanciya bisa kujera

      Turo bakin ta tayi deen yace " kaga Abdul meye damuwan ka ai ba a jikin ka ta zauna ba dan haka kar ka takura mata" dariya Abdul yayi yace "yanzu Dady ya kirani matan kawu zasu tafi gobe muje mu masu sallama yau, ni da kai kuma su Ama zasu je fito da takaddun su na jamb na sannin inda zasu zana dan saura two weeks a fara"

      Jin an ambaci jamb ran Ama ya baci a duniya idan da abinda ta tsana bai wuce karatu ba na secondary school din ma da ya ta karasa shi za a kara dakko mata wani,

     Deen ne yace "toh Allah ya kaimu da la'asar sai muje muyi masu sallama daga nan sai mu wuce cafe din, toh Abdul yace sannan ya fice

       Deen ne ya mai da duban sa zuwa ga Ama yace " baby me ya faru naga kina bata fuska" turo bakin ta tayi "ni wallahi yaya ban san karatun nan kwata kwata takurawa rayuwata kawai zaiyi" dariya Deen yayi yace "kar ki da Ama insha Allah zakiyi alfahari da karatun nan" da kyar ya samu ya shawo kanta ta dan saki ranta

       Kamar yadda sukayi alkawari sunje sunyiwa kawun nin su sallama sannan suka wuce cafe suka fito masu da takaddun jamb din su suka ci sa'a rana daya zasu zana amma wajen ya banbanta amma duk kan titin airport road

      Sanda suka kawo masu takaddun Marwiyya tayi murna sosai amma kuma Ama da aka kai mata har kusa kuka tayi


TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIOnde histórias criam vida. Descubra agora