38

1.3K 75 1
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

          3⃣8⃣

      Kiran sallar asuba ne ya farkar da Abdul Wanda dama baccin basu dade da yi ba, kallonsa ya maida zuwa ga Marwiyya dake kwance jikin kirjin sa tana ta sauke ajiyar zuciya, kana ganinta kasan ta sha kuka

       Gashin kanta ya shafa tare da yi mata kyakyan murmushi, shi kadai yasan me yake ji, so da kaunar Marwiyya kuwa kara karuwa suke kamar su fasa zuciyar sa su fito

        A hankali ya fara janye ta daga jikin sa ya dora ta bisa filo,bandaki ya Shiga yayi wanka tare da kara daura wata alwalar, baiyi yinkurin tashinta daga bacci ba ya fice masallaci


       Bangaren Zahradin kuwa da kyar ya sha fama Amatullah ta tashi bayan ya Shiga banda ki yayi wanka ya fito ya dinga aikin tashin ta sai da kyar ta tashi ta Shiga banda ki tana kunkuni shi kuma ya fice masallaci

         Abdul na sauke Marwiyya daga jikinsa ta farka amma taki nunawa tana ji yayi wanka ya fice, yana fita itama ta tashi da kyar ta daddafa bango ta Shiga banda kin

          Ruwan zafi ta hada ta Shiga, sai da tayi ihu saboda azaba ta dan jima a ciki taji dan dadin jikinta sannan tayi wanka ta fito

      Dadduma ta shimfida ta fara raka'atul fajr sannan tayi sallar asuba, har ta idar tayi adduo'in ta bai shigo ba hakan ba karamin dadi yayi mata ba, ninke dadduman tayi ta haye gado tare da Jan bargo

         Sai da gari ya dan fara haske suka shigo gida, Abdul na Shiga dakin ya hau gadon tare da dan bude fuskarta, baccin ta take hankali kwance, fuskarta ya bi da kallo yana jin wani nishadi na Shiga zuciyar sa, idon sa ne ya sauka akan dan karamin bakin ta da yafi komai daukar masa hankali

        A hankali ya kai bakin sa kan nata ya fara kissing, kamar a mafarki taji ana kissing din ta tayi saurin bude idonta, ganin Abdul ne yasa ta fara ture shi saboda tino mata da daran jiya da yayi

       Kan kameta yayi a jikin sa yadda bazata iya kyakyawan motsi ba, a hankali ya fara shafa duk wata gaba ta jikinta, ganin yana kokarin wuce gona da iri yasa na janyo masu kofar nace Abdul ba tausayi ba hakuri

         Zahradin na Shiga ya tadda ta tana bacci,shima gadon ya hau tare da janyo ta jikin sa yana shafata a haka shima baccin ya debeshi

       Karfe goma suka farka Marwiyya ce ta fara tashi ran nan nata a hade, a hankali ta sauka da kan gadon saboda radadin da take ji a kasanta, banda ki ta bude ta Shiga tare da hada ruwan zafi ta Shiga, sosai take jin zafi amma hakan bai sa ta fita daga ruwan ba, sanda ruwan ya yayi sanyi ta kara na zafi ta kusa minti talatin tana gasa kanta sannan tayi wanka ta fito

          Gaban madubi ta zauna ta shafa mai batayi wata kwaliyya ba ta dakko riga da zani na atamfa ta saka, har lokacin Abdul na kwance yana baccin sa hankali kwance ga wani murmushi kwance a fuskarsa

        Kallo daya Marwiyya ta mashi ta dauke fuskarta da tayi niyyan tashi sa ta fasa ta fice daga dakin tayi kasa dan ta dora girki

          Buga kofar da akeyi ne yasa taje ta dakko hijab din ta ta saka sannan ta bude kofar driver gdan su ta gani rike da kulolin abinci, fuskarta a sake suka gaisa ta karba ta nufi kitchen dan ta dora tea


       A hankali ya fara bude idonsa tare da shafa gadon, ganin bata nan yasa ya mike ya nufi dakin sa, wanka yayi sannan ya brush bayan ya fito ya shirya cikin kana nan kaya riga da wando ya sakko kasa 

       Ganin bata falo ya nufi kitchen a bakin kofa ya tsaya yana kallon yadda take wanke abin da ta dafa shayi dashi, murmushi yayi ya karasa inda take

       Ta baya ya rungumeta, "baby na shine kika tashi ba ki tashe ni nayi maki wanka ba koh" turo bakin ta tayi sannan tace "ina Kwana?" Murmushi yayi "lafiya lau baby na kin tashi lpya?" Ya fada yana shafa gefen fuskarta "lpya" ta fada a takaice, zaiyi magana yaga ta debi kulolin da plate tayi waje dariya yayi yabi Bayan ta

         Akan dining ta Jere kulolin sannan ta koma kitchen din ta dakko flask din shayi ta dawo ta tadda shi zaune kan daya daga cikin kujerun abinci ta zuba mashi Wanda aka kawo masu sannan ta hada mashi shayi ta ajiye mashi, itama ta hada nata ta zauna a kujerar dake kallon sa


        Tin da ta fara aikin yake binta da kallo domin komi cikin nutsuwa take yin sa sosai take burgeshi, duk wani Abu da zatayi burge shi takeyi

         Amatullah da Zahradin ne zaune a falo suna hira kanta na cinyar Zahradin tace "yaya anjima ka bude min kofa ta cikin gidan nan naje mu gaisa da sisto" banza yayi mata

       Ganin bashi da niyyar magana tace "yaya da kai fa nake kamin shi...... Tinowa tayi tace sorry my D Allah mantawa nayi" dariya yayi yace "ai gwara da kika tina amma hukuncin mantuwar ki shine baza ki ba sai nan da sati guda,

Zaro ido tayi cike da mamaki tace "haba yaya gamu a kusa amma kace sai nayi sati zan ganta"

       "Eh mana toh miye a ciki dan nace sai kinyi sati" Allah yaya zanyi kuka, au My D" dariya yayi zanyi tinani mu bar hirar" ba musu ta canza hirar

        Ganin tana cin abincin ta hankali kwance yasa yayi gyaran murya "haba baby ya zaki kiyimun magana"

     Hararsa tayi "toh ba kai bane" zaro ido yayi "me nayi kuma" ya fada yana bubbuga kafa, yadda yayi yayi masifar bata dariya,

        Yadda take dariyar yay masifar birgesa, yayi tagumi tare da kallonta, ganin kallon yayi yawa ta tabashi "yaya wannan kallon yayi yawa, kaci abincin kar ya huce" cikin shagwaba yace "toh zanci ki dawo kusa dani ki bani a baki" ba musu ta taso saboda ta gama cin nata,

      Har zata zauna a kujera, ya janyota kan cinyarsa,nan ta dinga bashi a baki, shima yana bata a baki har suka gama, ya taimaka mata suka yi wanke wanke sannan taje ta gyara daki



TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIDove le storie prendono vita. Scoprilo ora