51

1.1K 80 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

       5⃣1⃣



Kan sa ya daura akan kujera, ya cigaba da kuka a haka har bacci ya kwashe sa, kasan cewar lecture daya ne da ita tana fitowa gida ta nufo karfe sha biyu ta iso gida, a hankali ta bude kofar ta shigo cikin falon, turus tayi ganin Abdul a zaune ya dora kansa bisa kujera, tausayi ya bata amma ta dake tabi ta gefen sa ta wuce, daki ta shiga ta zauna bisa gado, idon tane ya ciciko da kwalla amma tayi saurin gogewa, ta shige toilet dan yin wanka

         Ummi ce ta sakko ta gansa zaune a haka, sosai tayi mamakin dama Abdul na zaune bai tafi ba, zuwa yanzu ta fara tausaya mashi, a hankali ta zauna gefen kujerar da ya dora kansa, dago kanshi tayi ta dora a cinyar ta tana zura hanun ta cikin gashin sa, a hankali ya fara bude idon sa, ganin sa akan cinyar Ummi yasa shi jin dadi a hankali ya furta "u..m..m.I " murmushi ta mashi, Abdul ka tashi kaje dakin ka kwanta ai sai wuyan ka yayi ciwo" murmushi yayi "toh ummi na nagode" ya fada yana mikewa ya nufi dakin sa yayi wanka ya kwanta saboda wani irin zazabi da yaji ya fara rufe shi

       *WASHE GARI*

     Tin safe gidan kowa ya fice ya rage daga Abdul sai Marwiyya, Ummi da Mumy sun tafi gaisuwa yar yayar Mumy ta rasu, sai Dady, Abba, Deen sun tafi office, Ama kuma tana da lecture

        Gajiya da yayi da zaman dakin yasa ya shigo cikin falon, tana zaune tana kallon wani Indian film *HAPPY NEW YEAR* sosai take jin dadin film din duk da cewa ba sabon film bane amma bata gajiya da kallon sa, tana sanye cikin atamfa Ash mai ratsin baki, kanta babu dan kwali

      Da sallama ya shigo, ba tare da ta kalleshi ba ta amsa mashi sallamar, kasa ya zauna kusa da kafafun ta, "Baby" ya fada cikin dasaciyar muryar sa" ba ta ko kalle shi ba bare ta sa ran zai amsa mata, hanunsa ya Dora kan cinyar ta, "baby ki duba girman Allah ki yafe mun, wallahi na gane kuskure na, kuma duk wani hali nawa na canza Allah bazan kara zama sanadiyar kukan ki ba, ina sanki sosai baby"

      Hanun sa ta janye daga cinyarsa "Abdul baka san Allah ba da ka sanshi da baka hadani da shi ba kace na yafe maka, kuma ina gargadin ka ka bar harkata dan ni ba ajinka bace, ni ba wayayi ya bace kaje ka samu wadda tsarin rayuwar ku zai zama daya amma ban dani" ta fada tana barin wajen ba tare da ta jira cewar sa ba

      Tana barin wajen Abdul ya fara tari kamar ransa zai fice aman jini ya farayi nan take ya fadi sumame

       Cikin sauri ya shigo gida saboda wata takadda da ya manta, ganin Abdul kwance bakin sa na jini yasa Deen fara anbaton Allah, daukar sa yayi ya nufi asibiti yana zuwa aka karbeshi cikin gagawa, ana shiga dashi daki  Deen ya kira wayar su Abba ya shaida masu sannan ya kira su Ummi ma, cikin minti ashirin gaba daya suka halacci asibitin, ta window suka hango Abdul ummi da Mumy kan har kwallah sukayi saboda ganin halin da yake ciki

       Wayar da ake tayi mashi yasa dole komawa gida ya dakko takaddar ya kai masu office sai ya dawo

      Tin da ta dawo daga makaranta take zaune a falo haka kawai taji gaban ta na faduwa, cikin sallama ya shigo falon ta amsa mashi cikin sanyin murya "sannu da zuwa" yauwa ya fada yana shiga dakin Ummi dan ya takko takardar daman nan ya ajiye ta

Bayan ya dakko takarda ya nufo waje Ama ta tare shi "Yaya ka yi hakuri ka saurare ni yau kadai" banza yayi mata zai wuce ta gefen ta, kara tare shi tayi "ko ba dan ni ba ko dan darajar abinda ke cikina ka saurare ni" jin ta ambaci abinda ke cikin ta yasa jikin sa yin sanyi yasan bai kyauta masu ba, Dafa ta yayi yace "Ama ina sauri ne jirana ake yi a office in na dawo mayi magana" ya sake ta ya nemi fita, har yaje kofa ya dawo, hanunta ya kama ya zaunar da ita shima ya zauna, "sweat heart Abdul ne ba lpya muna asibiti su Mumy ma na can" cikin tashin hankali tace "yaya me ya same shi" nima ban sani ba kice wa Marwiyya ta shirya zan kai sako in na dawo zan kai ku, toh kawai tace mashi ta fice

      Abu kamar wasa Abdul kwanan sa hudu a asibiti amma ko matsin kirki baya yi bare a saka ran zai motsa ya tashi, zuwa lokacin kowa jikin sa yayi sanyi ciki harda  Marwiyya amma hakan bai sa taje asibiti duba shi ba, duk yadda aka so taje tayi kememe taki zuwa

      Deen, Dady da Abba ne zaune gaban likita yana masu bayani "insha Allah komi ya kusa dai daita yanzu mun samu numfashin sa ya dai dai ta, amma zan baku shawara daga yau zuwa gobe zai iya farkawa amma dole a bashi abinda yake so, domin kuwa akwai abinda yake matukar so a duniya mudum kuma ya rasa abun zai iya rasa ransa gaba daya" gaba dayan su babu Wanda bai tausayawa Abdul ba musamman Deen kuma yayi alkawarin shawo kan Marwiyya ta yadda ta koma dakin Abdul

        Yau suke sa ran farfadowar Abdul tin safe suke zaune gaba dayan su amma banda Marwiyya a hankali ya fara motsa hanunsa, yana bude idon sa dishi dishi ya fara gani har ya ga komi dai dai,

     Idon sa ya fara kaiwa kan Ummi yaga tayi mashi murmushi, sannan ya kalli Abba, Deen Mumy, Dady da kuma Ama ya ga duk sun mashi murmushi, runtse idon sa yayi ganin babu Marwiyya a dakin nan da hannu yayi ma Deen alamar yazo, babu musu kuwa yaje a hankali Deen ya daga shi ya jinginar dashi da gadon, roba ya dakko da brush ya wanke mashi baki sannan yaje ya zubar ya dawo kusa dashi a hankali Abdul ya furta "brother yau Kwana na nawa a nan" ba tare da ya kawo komi a ransa ba yace "kwanan ka Biyar" kuka Abdul ya fara "Abba na san  baby bata zo nan ba, tsanar da tamun ta kai har nai Kwana biyar a asibiti bata zo ba, Abba me zan ma Baby da ku, Wanda zai sa Ku yarda na canza Ku bani matata, Dady Allah muna mashi laifi ya yafe mana amma ni me yasa baza  a yafe mun nawa laifin ba, saboda kawai Allah ya jarabce ni da Santa,  Ummi kuna zaune tace na saketa har marina tayi, na sake ta ne saboda kurum na faran ta mata, amma kuma Bayan nayi sakin naga bazan iya rayuwa babu ita ba, Mumy Deen na yarda koh kullum Marwiyya zata na haihuwa bazan kara shan kwaya ba, Ku yafe mu...." Kuka ne yaci karfin sa ya kasa karasa kukan

       Gaba daya yan dakin babu Wanda baiyi kuka ba ni kaina da nake dakko maku rahoto sai da *Mzz dady* ta rarashe ni na daina kuka

       Deen ne yayi karfin halin cewa "Brother ka daina kuka, mun yafe maka, ita ma kuma zata yafe maka ka kwantar da hankalin ka" taya Deeni hankali na zai kwanta bayan ban da farin ciki" da kyar Deen ya rarashe sa yayi shiru sannan suka hada mashi tea ya bashi ya sha




TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now