45

1K 71 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*




               4⃣5⃣

      A daren ranan da sukayi jamb din aka turo musu result dinsu wanda dukkansu sun tsallake cut mark din.




     Marwiyya dadi taji sosai banda Ama da kwata kwata bataso ci ba. Washegari kaman kullum Marwiyya ta tashi ta hada breakfast kafin Abdul ya shirya ta gama sannan sukayi breakfast ta rakashi har mota ya wuce sannan ta dawo ciki.





       Ama kuwa Deen ne dai ya sake shiga kitchen amma yau ya makara saboda haka be tsaya yaci wani abincin kirki ba ya mata sallama ya wuce.





        Gabadaya setaji ba dadi dan ita kanta tasan tun farko bashi ya kamata ya shiga kitchen din ba itace, wayanta ta dauka ta kira Marwiyya, ringing daya Marwiyya ta dauka Ama tace "sister pls in bakya komai kizo", shiru tayi saboda yanda taji muryan Ama can kasa sannan tace " Ina zuwa, bari na kira Mine senazo", kashe wayan Ama tayi tana jiran shigowan Marwiyya.





         Abdul Marwiyya ta kira inda kaman jira yakeyi bugu daya ya daga yace "swthrt yanzu fa na bar gida, har kin fara missing dina ne?", ya tambaya cikin zolaya.





      Dariya tayi sannan tace " Mine Ama ce ta kirani wai nazo, kuma naji muryar ta kasa kasa, shiyasa na kiraka kamin in shiga", dan jim yayi kadan yana tunanin meyasamu Ama, Marwiyya jin shirun yayi yawa yasata kiranshi "Mine", ajiyar zuciya ya sauke sannan yace " kije ki dubata, in kinga da wani matsala ne ki kirani", "OK bye", kawai tace mishi ta kashe wayan tareda dauko mayafi ya kullo kofan ta sauko, ta kofan baya  tabi ta shiga gidan Ama, da sallama ta shiga parlourn Ama ta amsa mata tareda cewa " ai nazata bazaki zo ba", "haba dai ni na isa ki kirani inki zuwa", cewar Marwiyya tana zama tareda kallon Ama tace " lafiya dai ko, naga kinyi doll".





        Gyara zama Amatullah tayi tareda sauke ajiyar zuciya tace "sister se yanzu nake dana sanin kin jin maganarki", cike da neman karin bayani Marwiyya tace " wani magana?", Ama ta kalleta sannan tace "na  in dinga shiga kitchen muna girki tare saboda na iya, amma naki jin maganar gashi yanzu yana damuna".






       Yanzu Marwiyya ta gane inda Ama ta dosa, saboda haka tace " Toh ai yaya beda matsala, ni nasan yayana, ze iya shiga kitchen da kanshi", ajiyar zuciya Ama tayi tace "shi ke shiga kitchen tinda mukazo, gashi yau ya makara saboda ni, kila dani ke girkin da be makara", kallon Ama Marwiyya tayi tace " ki kwantar da hankalinki, wannan ba matsala bace, lokaci be kure ba ko yanzu zaki iya koya", kallon Marwiyya Ama tayi tana gada kai tace "shiyasa na kiraki dan musan daga inda zamu fara", " daga yanzu", Marwiyya ta fada tana komawa kusa da Ama da dauko wayanta ta kunna tana shiga YouTube tace "sister dauko jotter da pen", Ama da saurinta ta mike tana wani jin dadi ta dauko ta dawo, nan suka shiga duba girki kala kala wanda zasuyi jot suyi jot, wanda beda wahala suka zasu iya rikewa a kai su rike.


*BAYAN WATA SHIDA*

         A cikin wata shidan nan abubuwa dayawa sun faru wanda daga ciki akwai samun Admission dinda su Ama sukayi, inda Ama zata karanta Biochemistry, Marwiyya kuma Microbiology,  yanzu Ama ta kware a girki ba karamin taimako Marwiyya da YouTube suka bata ba, har yanzu babu abinda ya canza daga cikin zamansu sema kara jagulewa da komai yayi a halin yanzu.




      Kullum in Abdul ze sadu da Marwiyya se taga yasha wani pill wanda tun daren farkonsu ta fara lura amma bata kawo komai a kai ba saboda inya matso ta kamshin sweet takeji, sedai yanzu abinda ya soma damunta dan ta rasa ta ina pills suke fitowa saboda daya fita zata shiga dakinshi tayita dube dube ko zata gani amma bata gani.




     Abin na daure mata kai sosai gashi ba dama ta tambayeshi, har yau har gobe Abdul besan me akecewa kishi ba dan kwata kwata shirin Marwiyya baya damunshi, indai zatasa rigan daya kamata ace shi kadai ya gani toh zasu zauna lfy, amman in taki ba zaman lfy.



 

     Ta rasa hanyar da zatabi ta nuna mishi cewar jikinta nashi ne shi kadai bana kowani mahaluki a waje ba. Ganin in zasu fita batasa kayan da yakeso tasa yasa yanzu kwata kwata ma ya daina cewa ta shirya suje shopping dan a wurinshi tana shiri ne kaman na mutanen da kansu be waye ba.




      Amatullah kuma kullum kafin ta tafi skul sai sunyi rigima da Deen dan ko kadan bason karatun take ba, ga bata maida hankali, ya soma mata driver dinda zai dinga kaisu skul yace in sukayi exam din first semester yaga points dinta ze siya mata mota amma wannan besa taji tanason yin karatun ba.




        Sun jiki ne da ita bata iya aikin komai sedai ta kwanta tasa waya a gaba, a halin yanzu tace Deen ya nemo mata er aiki wanda ya amince saboda ta samu tayi karatun ta da kyau.




       Amatullah ta ajiye duk wani abu da kukasani waishi atampha ko shadda ko lace gefe ta koma sa jallabiya wanda Deen be tada hankalinshi a kai ba tinda yasan ba matsastsun kayan da tasaba sawa take sawa ba.




TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now