25

1K 84 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

                2⃣5⃣

        Yana zuwa gida ya shiga parlour direct ransa bace amma ganin yanayin Amatullah yasa bacin ranshi ya kau har dariya na neman tsinke mishi.



       Zaune take ta bata rai, ta hada giran sama da kasa, ta turo dan karamin bakin ta gama ita ala dole fushe takeyi.



       Bayan ya gaishe dasu Mom ya karasa ya zauna kusa da ita Mom tace "ka ganta nan, tin dazu ta shirya su tafi taki wai ita bazata yi".



      Kallon Amatullah yayi yace " Ama da gaske?" Kada mishi kai tayi cike da shagwaba tace "Yaya toh ni ni......", seta sa kuka.


      A rikice yace " Ama lfy, yada kuka" amma shiru ba amsa, ganin haka ne yasa ya jata suka fita waje Ummi tace "Ama kenan, rigimanta na yau daban na gobe daban", Mom tace " ai Deen ne daidai ita, yanzu zakiga ta shirya sun tafi" haka sukaci gaba da hiransu Marwiyya kuwa tana zaune wuri daya tana mamakin Amatullah.



      Suna fita waje ya zaunar da ita kan kujeran da ke compound din yace "yanzu daina kukan nan ki fadamin meyasa bakyaso ki rubuta jamb din", share hawayenta tayi tace " ni yaya kawai banaso na koma school ne", kallonta yayi yace "ke yanzu zaman gida ya fiye miki neman ilimi", shiru tayi yace " look swthrt wannan karatun da zakiyi ke zaiyi favor ba wani ba, it's for ur own good ", cike da tsiwa tace " yaya I knw,amma ni gaskiya bazan iya komawa ba".


       Shiru yayi daga bisani ya nisa yace "swthrt can u do something for my sake", da daga kai yace " toh dan Allah kije kiyi register din nan for my sake kinji", shiru tayi ta turo baki gaba yace "plss", kallonshi tayi tace " naji, if dat will make u happy zanje nayi", murmushi yayi ya ja kumatunta yace "dats my babe, tashi kije ki shirya".




       Su Mom suna zaune sega Ama harta shirya Deen na bayanta tace " Sisto let's go", yanda tayi maganan yasa Marwiyya dariya amma tayi saurin gimtsewa saboda tasan halin Marwiyya, Mom tacewa Ummi "mena ce miki", ita dai gimbiyar tana tsaye se cika takeyi.




     Sallama sukayi ma su Ummi suka fita Zahradeen shi ya kaisu ya dawo da su sannan ya koma office.



*Bayan kwana biyu*

         Marwiyya ce zaune tana tsifa tace " sisto kema ki tsefe kanki muje salon tare", Amatullah dake kwance tace "gama tsefe naki kizo ki tsefe min wlh kiwa nakeji", wani kallo Marwiyya ta mata tace " sannu gimbiya, kina kwance sannan kuma kice in gama nawa inzo miki naki dayake nice bansan dadin hutu ba", yatsine fuska Marwiyya tayi tace "look I'm bazaki tsefe min ki bashi basai kin gayamin magana ba dan yaya baya nan ne daya tsefe min kema kin sani".




        Wani dariya Marwiyya tayi tace " yaya ne zai tsefe miki kai, lallai in ma mafarki kikeyi ki tashi dan bazeyi ba", kallonta Amatullah tayi tace "haka kika ce", " kwarai kuwa haka nace",  Amatullah tayi murmushi tace "shikenan muyi bet, ni nace miki ze tsefe min kuma inya tsefe min sabon  ribbon dinki zaki bani", Marwiyya tace " shikenan in kuwa be tsefe ba pouch dinki zaki bani". Haka sukayi bet Amatullah se addu'a takeyi a ranta Allah yasa ya tsefe mata dan tasan halinshi.




       Haka suka zauna har Marwiyya ta gama tsefe nata Amatullah na kwance har bacci ya fara daukan ta.


      Ganin yamma ta kawo kai yasa Marwiyya tashi tace "Ama tashi mu shiga kitchen", cikin muryan bacci Ama tace " kai Marwiyya dan Allah ki kyale ni nayi bacci haba", "ke bakisan baccin yamma ba kyau ba", " nasani kadan zanyi". Ganin Amatullah ba tashi zatayi na yasa Marwiyya tafiyan ta.



      Marwiyya ce tayi girkin ta gama sannan taje tayi wanka tayi sallan Magrib tana tunanin meyasa su yaya suka dade yau har anyi Magrib basu dawo ba.




     Tashin Amatullah tayi tace "sisto tashi Magrib yayi", tashi Ama tayi ta wuce dakinta tayi wanka sannan tayi alwallah tayi sallah ta
fito .



     Tana zuwa ta zauna kan dinning tace " kai yunwa nakeji", tareda zuba abinci ta fara ci tana santi sega Marwiyya. Marwiyya na ganin ta tace "sanda aiki Ama, sanda nace kizo muyi girkin tare kika ce min ke bacci kikeji yanzu na gama kin wani sa gaba kina cika cikinki", bata rai Ama tayi tace " dan na ci abincin ne kike nema ki gayamin magana, laifi ne dan naci, ba saboda aci kika dafa ba", Marwiyya tace "yanzu na fada wani abunne da ranki ya baci haka", Amatullah data riga ta mike tace " bansani ba" tareda jan tsaki ta juya zata wuce taga ashe yayanninta na tsaye wurin suna jinsu.




TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang