26

1K 80 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

              2⃣6⃣

Dauke kanta tayi kamar  bata  gansu ba tayi niyyar fita  Abdul ya ruko hanunta " me aka miki  da zaki fishi ko kuwa saboda abin fishin  bashi da wuya"

         Turo bakin  ta tayi tace " na koshi ne  yaya" harar  ta yayi "wuce kije kici" ya fada yana mata nuni da dining, turo baki tayi kamar  zatai kuka


      Kan tai magana Zahradin ya ruko hanunta "sorry baby na karkiyi kuka kinji, muje kici  abincin ki ita Marwiyya wasa take maki" da kyar ya rarasheta taje suka ci abincin bayan iyayen sun fito


      Bayan sun gama dinner Amatullah da Zahradin suka fice zuwa falon baki don  suyi hira Ama tace  "yauwa yaya gobe da safe tin da Sunday ne ba aiki zaka min tsifa" ta karasa maganar cikin shagwaba



      Zaro idon  sa yayi  "tsifa kuma?" Girgiza kan ta tayi alamar eh, murmushi yayi  "haba baby Ina ni ina  tsifa sai kace........." Bai karasa ba Amatullah tasa kuka


      Idonta ya share mata "yi hakuri ki daina kukan zan miki kinji, Allah ya kaimu goben" cikin murna ta rungumeshi "thank yuh bro" tana sakin sa taga ya bata fuska



       Gaban ta ne ya fadi tunowa da ranar da yayi mata gargadi akan rungume sa, langwabar da kanta tayi kamar  zatai kuka "am sorry swt mantawa nayi" girgiza kansa kawai yayi suka canza hirar sai  ten ya rakata daki shi ma yayi nashi dakin




         Amatullah da Marwiyya ne zaune a falo suna hira gefen Amatullah kuma kibiya da kum ne tana jiran shigowar Zahradin



    "Sisto ki kawo na taimaka na maki tsifan nan mu tafi  yaya kan na san bayi miki zaiyi ba" dariya Amatullah tayi kan tai magana Zahradin ya turo kofar ya shigo tare da sallama



      Bayan sun amsa tace "yaya ina ta jiranka tin dazu kamun tsifa"


      "Am sorry dear nima ina ta sauri na fito na maki aikina na karasa taho na yi maki" ya fada yana zama bisa kujera


       Kasa ta zauna ta mika mashi kibiyan, ya karba ya fara yi mata tsifa hankali kwance Bayan ya tsefe daya ya fara taje mata a hankali



    Cikin shagwaba tace "yaya kayi a hankali akwai zafi fah" toh baby yi hakuri" Marwiyya kan sakin baki tayi tana kallon ikon Allah wai yaya da tsifa, Amatullah ce ta katse mata tunanin ta



     "Sisto a shiga  ciki a dakkon ribbon dina" hade fuska Marwiyya tayi "wace ribbon din kin ban ajiya ne"



      Dariya Amatullah tayi "kin fi kowa sanni wace ribbon din nake magana dan haka je ki dakkon" banza Marwiyya ta mata bata kulata ba




     Sai da Zahradin ya gama yima Ama tsifa Amatullah tace nagode tana mikewa dai dai nan Abdul ya shigo

       "Yawwa yaya gwanda daka shigo cema Marwiyya ta dakon ribbon dina" wacce ribbon din?" Abdul ya tambaya, nan Amatullah ta basu labarin komi bayan ta gama Abdul yay tsaki




      "Toh dan ya maki tsifan sai me ko an fada maki ni bazan iyayi mata sifan ba, kuma salon din ma baza ta ba ni zan mata da kaina, in shi Zahradin din ya isa yayi maki"




      Tabe bakin ta Amatullah tayi "matsalar kuce kai da ita ni dai a dakko min ribbon dina"


      "Allah Ama kika batan rai bazan baki ba" yaya bari mu shirya ka kaimu salon din, Marwiyya ta fada tana kalon Abdul




     "Ki bari zan wanke maki kan da kaina na gyara maki baby na" girgiza kanta tayi "banso ka wahala yaya ka kyale su kawai" da kyar Marwiyya ta rarashi Abdul ya hakura bazai wanke mata ba amma zai kai su daki ta shiga ta dakkowa Ama ribbon sannan suka shirya Abdul ya kai su salon din ya jira suka gama suka koma gida







*Bayan sati uku*



         Biki ya rage saura wata biyu sai faman shirye shirye suke tin safe suka gama duk wani aiki da zasuyi sabida yaune zasu fitar da ankon bikin da kuma fara nunawa kawaye ankon



     Kwanan Zahradin da Abdul uku da tafiya India dan karasa hado laife  inda zasuyi sati guda a can, kullum suna cikin kasuwa saboda siyayya





      Amatullah ce sanye cikin atamfa riga da skirt sai karamin mayafi Itama Marwiyya atamfar ta saka amma da hijab ta saka iyayen su sukayiwa sallama sannan driver ya kaisu gidan su Zeee dan su dauketa su tafi








TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now