30

1.1K 82 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

         3⃣0⃣

      A tsakar gida suka tadda kawun nan su da iyayen su sai kuma makwabta suna ta zuwa ganin su wadan da suka sansu, inna suwaiba ma ta zo tana ta jiran dawowar su Ama ta gansu,

       Kiran sallar mangariban da akayi ne yasa mazan suka wuce masallaci matan kuma kowa ya shige daki dan gabatar da sallah, basu sake fitowa ba sai bayan sallar isha'i suka fito Abdul na makale da Marwiyya yana ta bata labari" kawu Adamu yace " soyayyar zamani babu koh kunya Abdul" dariya Abdul yayi yace "toh kawu in ban nuna mata so ba me zan mata" duka Mumy ta kai mashi, yayi saurin kaucewa yana dariya, basu suka kwanta ba sai wajen goma sannan kowa ya tafi makwancin sa



        Washe gari basu tashi ba sai wajen goma, bayan sunyi wanka suka karya, sannan su Dady suka fice, basu dawo gidan ba sai la'asar sannan suka ce ma su kawu sun canza masu gida a Bayan layi kato mai kyau ban gare uku ne,


       Kayan su masu anfani suka diba gaba daya Wanda zasu bayar suka bayar suna ta murna a ka debesu zuwa sabon gidan an tanadi komi na rayuwa kama da gado, kayan kallo, kayan abinci da abubuwa kala kala, bangare daya na kaka da Yan matan bngare daya na Kawu Ahmad, ban gare daya na kawu Adamu, bangaren kakan su Dady suka  zauna kafin su tafi, washe gari suka sa aka fara rushe wancan gidan dan a kara gina shi, katon shagon dake sabon gidan guda biyu suka cika da kayan masarufi dan su dinga siyarwa


       Ranar da za su koma gida suka basu kudade masu yawa sannan sukaima makwabtan alkairi suka masu sallama akan in biki ya rage sati za a aiko da mota a kwashe su,



         Kwanci tashi ba wuya wajen Allah, duk abinda aka sakama lokaci zai zo, bikin su Ama ya rage saura sati biyu, shirye shirye suke ba kama kafa, kullum suna busy, haka ma bangaren angwayen gaba daya babu zama

      Abba da Dady ne tsaye a wani gidan flat dan madai daici, wani mutum ya fito cikin shigar sa ta kamala, cikin girmamawa suka gaida shi ya amsa cike da mamaki manyan mutane masu kudi amma kudin su bai rufe masu ido ba suna girmama mutane, maganar su ce ta katse mashi tunanin

      "Kawu Hamza baka gane mu ba ne?" Suka tambaya cike da mamaki, "eh wallahi ban gane ku ba kuyi hakuri" ba komi ni sunana Abubakar sai kuma wannan umar yaran ka ne" cike da mamaki Hamza yace "ikon Allah kune kuka zama magidanta haka, ku shigo, ba musu suka shiga suka gaida matar sa nan suka shaida masu auren yaran su za'ayi, sosai sukai mamakin tare da fatan alkairi kuma zasu zo



      Tin safe suke yawan rabon I.v din bikin su, tin suna shawar yaron har suka gaji, basu suka koma gida ba sai Bayan sallar isha'i

Abdul ne zaune a office aka kwankwasa kofar tare da shigowa, Zahradin da Adnan da kuma yusuf da Khalil  suka shigo, zaro ido Abdul yayi "me ya faru kuka yo min gayya haka a office" dariya Yusuf yayi "tin da ka ganmu da yawa Kasan da alkairi" murmushi yayi "toh bismillah ku zauna" ba musu suka zauna" Adnan yace "ango me kuka shirya mana ne na bikin  dan mun tambayi Zahradin yace mu tambaye ka" dariya Abdul yayi "toh sunce zasuyi kamu, walima sai dinner" amma bamu gama shirye shirye ba tukun" toh mu dai namu gudummawar za mu shirya maku hadaden party a *MEENA EVENT* dan har mun tambayo kuma muna so ranar ya zama ranar alhamis" toh Alhamdulilah mun gode sosai da naku gudummawan nan suka cigaba da tsara event din


       Ana saura sati guda biki aka takko wata mata takanass ta kano tin daga mai duguri dan ta masu gyaran jiki, tin a kwana na uku suka yi kyau sosai, tin da aka fara gyaran jikin su Abdul basa ganin su Ama hakan bai masu dadi ba duk hanyar da zata sada su ummi ta toshe dole suka hakura badan sun zo ba


      Yau ya kama Tuesday  tin safe suka tafi salon kasan cewar gobe laraba kuma gobe za'a fara bikin, da laasar kuma suka wuce gidan su Zainab kasan cewar a can za a masu jan lallen

       Zaune suke suna hira an sa ma Amatullah lalle, ita kuma Marwiyya ana mata na kafa, wayar ta tayi kara ganin Abdul ke kira yasa ta zauna tare da karawa a kunnenta, "kuna ina ne nasan bakwa gida plsss kimin taimako ki gayan inda kuke nazo na ganki nayi missing ki a lot" shagwaba fuska tayi kamar zatai kuka tace "gaskiya Mumy da Ummi zasu mana fada kayi hakuri, duk yadda Abdul yaso ya zo inda suke taki yarda daga karshe yayi fishi ya kashe wayan



TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ