12

1.3K 116 1
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

                1⃣2⃣

Bayan sun dawo daga sallan isha sunyi dinner Abdul ya shiga dakinshi ya tsantsara wanka ya fito ya shirya cikin wasu arnan riga da wando na Gucci takalmin shi ma daga kafanin Gucci ne haka zalika agogon shi.

Tsarka yasa a wuya har guda biyu ya taje gashin kanshi yasa mishi oil ya fesa turare se kamshi yakeyi ya fito fes abinshi sedai shirin ne bana arziki ba.

Waya ya dauka ya kira Marwiyya yace tazo ta sameshi a parking lot yana jiranta. Baiwar Allah duk a tunanin ta zance zasuyi saboda haka ta dau wanka cikin wani gown na atampa wanda ya zauna mata das ajiki, sannan tayi simple makeup bata daura dankwali ba se karamin mayafi data yafa a kanta, sosai tayi kyau abinta sannan ta dauki turare ta fesa ta fita.

Duk suna zaune parlour gabadayansu suna kallo suka ganta Amatullah harda tsokanan tana tacewa "matar yaya wurin yayan za'aje ne akaci uban kwalliya haka". Sudai sauran murmushi ne nasu da haka ta fita se parking lot.


Cikin mota ta hangoshi zaune yana dannan waya, gabanta ne ya fadi ganin shirin da ke jikinshi amma seta dake tace " yaya gani", ya dago ya sake mata tsadadar murmushin sa yace "baby ya kike, yau bamu samu mun zauna ba, nayi missing dinki", itama tayi murmushi tace " ina lfy, amma fa seda nayi zazzzabin rashin ka na yau", dariya yayi yace "toh gani yanzu, kuma fita zamuyi nida ke", " ina zamu a daren nan?".

Be amsata ba seya miko mata kaya yace ta shiga mota ta canza saboda inta shiga gida aka ganta da kayan za'a mai fada.

Kallon kayan tayi sosai sannan cike da takaici ta kalleshi tace "skinny jeans da wannan da karamin matsatsen top kakeso nasa", " yes, shi nakeso kisa ko bazaki sa", kai tsaye tace "bazan sa ba, wai ma ina zamu", wani kallo yamata yace " club zamu, in kuwa bazaki sa ba se inyi tafiya ta, bazan rasa matan da zanyi rawa dasu a can ba".


Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga bin kuncinta tace "haba yaya, yanzu kana dan musulmi kace zaka club, inkaje wace uwar zaka tsinana a wurin banda ka daukowa kanka zunubi, bawai fata ba in Allah kuma ya dau ranka kana clubbing me zakaje kace mishi, wlh yaya kaji tsoron Allah, duk wannan abinda da kakeyi se Allah ya tambeya, yaya ka......", bata karasa ba ya daka mata wani uban tsawa wanda seda ta firgita yace " dan Allah  keep quite sayyada uztaziya, sannu malama me tsoron Allah, se aka cemiki bana tsoron Allahn ne, yaushe ma kikazo duniyan zaki wani zo kina gaya min Allah annabi".

Shiru tayi ya nuna ta da yatsa yace "toh wlh kishiga hankalin, namayi babban kuskure danaga kaman zaki iya rakani, na manta cewar ki din bagidajiga ce", ta sauri ta dago da idanunta masu tsaiyayar hawaye tace " yaya ni?", yace "yes u, kedin fa nake nufi ko akwai wata a nan ne bayan ke", girgiza kai tayi cikin muryan kuka tace " yaya Allah ya baka hakuri, ya huci zuciyarka, a dawo lfy", tana fadan haka tayi ciki da gudu shikuwa jikinshi ne yayi sanyi kukan da yaga tanayi sosai yake taba mishi zuciya amma wannan be hanashi zuwa club din ba dan shiga motanshi yayi yaja abinshi ya kara gaba.

Ita kuwa Marwiyya shiga gida tayi tana kuka kaman ranta ze fita duk hankalinsu ya dawo kanta taje gaban Abbanta ta tsugunna ta rike kafanshi cikin muryan kuka tace "Abba nagaji, Abba banzan iya ba wlh bazan iya ba, bazan iya auren Abdul b......", bata karasa ba taji wani gigitaccen mari a kuncin ta da sauri ta dago tareda rike kuncin ta taga Abba wanda idonshi yayi ja yace " bakida hankali ne, ki awa dazaki zo kice ke bazaki iya ba, toh bari kiji in fada miki magana daya wanda bazan kara maimaitashi, kinga Abdul koda ace shine tantirin duniya gabadaya aurenki dashi ba fashi".


Wani mahaukacin kuka ta saki a wurin Ummi kuwa tausayin er ta ya kamata haka ma Mom da Dad, Deen kuwa ranshi inyayi dubu ya baci saboda an mari kanwarshi akan Abdul, yaron da beda halin kirki, Amatullah ma har kwalla tayi ganin er uwarta a wannan halin tasan ku ba'a fada mata ba Abdul ne ya bata mata rai amma gashi ita ke facing fadan iyaye, ko ina Abdul din oho.

Marwiyya cikin kuka tace "Abba na kayi hakuri, na butulcewa zabinka, Insha Allahu koda wasa bazan kara ba", tana gama fadan haka seta mike tayi dakin ta Abba jikinshi ne yayi sanyi saboda haka ya kasa zama ya fita waje Umar yabi bayanshi. Parlour kuwa kowa shiru yayi an rasa me magana saboda kowa da abinda zuciyarshi ke raya mishi.


Marwiyya seda tasawa kofanta key sannan ta kwanta tasa wani sabon kukan a zuciyar ta tace " tabbas da matsala a wannan auren, amma iyayena sun kasa gano matsalan, ance yaro bazai iya hango abinda babba ya hango ba amma ni ina ganin na hango abinda su Abba suka kasa hangowa", kuka ne yaci karfinta ta kuwa yishi bil hakki saboda a halin da take ciki kuka ne kawai ze iya sawa radadin da takeji yayi sauki, a haka har bacci ya dauke bata iya tashi ta canza kaya ba.


Kowa ya kwanta rai ba dadi banda Zahradeen daya fito waje yana jiran dawowan Abdul. Shikuwa Abdul yanacan club inda kida da warin giya da warin cigarette kawai ke tashi, yana zaune gefe daya ga kwalban wine da shisa a gabanshi amma tunanin Marwiyya ya hanashi sakat, tabbas abinda tafada gaskiya ne, zunubi kawai yake kwasarwa kanshi dan banda badala da lalata ba abinda akeyi a wurin, ga matan wurin kusan duk tsirara suke, shisan shi ya busa seda ya gama ya tashi ya bar wurin saboda baya ganin ze iya kara minti daya a wurin dan matan wurin sun dameshi, ko wannensu kawo mishi tallan kansu suke yi.


Yana danna hancin motanshi a compound din gidan ya hango Zahradeen tsaye da hannu tankwashe a kan kirji kanshi kasa dagani kasan tunani yakeyi.

Hasken motan ne yasa ya dago kanshi ya maida kanshi kan motan harseda Abdul ya fito, kallon shirin Abdul yayi ya girgiza kai Abdul ya karaso wurin sukayi handshake sannan yace "me kakeyi a nan da uban daren nan", Deen yace " kai nake jira", Abdul a ranshi yace "me kuma ya faru" amma a fili cewa yayi "gani toh, ya akayi", Deen seda ya gyara tsayuwar shi sannan yace " Abdul akan Marwiyya wlh zamu iya batawa dakai, kadaina sa kanwata kuka saboda banzan halin ka, ka daina bari ana hukunta min Marwiyya akan laifin da banata ba", Abdul yace "me kake nufi, waya hukunta ta, me aka mata?", hankali tashe ya jero tambayar.

Deen ya koro mishi duka abinda ya faru, ai in hankalin Abdul yayi dubu toh ya gama tashi jin an marin rabin ranshi akan tace ta hakura da auren shi, wani gumi ne ya shiga tsatsafo mishi duk da iskan da akeyi a zuciyarshi yace " ai in Marwiyya take aurena na kade dagani har ganyena, dan wlh kasheni zatayi da raina", becewa Deen komai ba yayi hanyar shiga bangaren su Marwiyya da sauri Deen ya riko shi yace "ina zaka", " zanje naga Marwiyya ne", "ba yanzu ba dan tayi bacci kabari gobe da safe kun ga juna", kada kai kawai yayi sannan yama Deen seda safe yayi bangaren su, shikuwa Deen girgiza kai yayi dan Abdul ya bashi tausayi saboda barobaro yaga so da tsoro a idon Abdul daya cemai Marwiyya tace ta hakura, haka shima ya shiga gida da tunani kala kala a ranshi.

Nikuwa kuna gani wannan auren ze yiwu?

TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now