53

1K 82 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

  

                5⃣3⃣

      Likitan ne ya fito a hankali ya furta "sai dai kuyi hakuri munyi iya yinmu mudin bai ga abinda yakeso ba baza'a iya shawo kan matsalar ba", su dukkan su jikinsu ne yayi sanyi kowa da abinda yake rayawa a ranshi kafin suji Ama tace " sister ", su dukkansu kallon inda take kallo sukayi sukaga Marwiyya tsaye kanta a kasa.





      Wani hamdala Deen ya sauke kafin ya juya wurin doctor yace " ga wacce yakeson gani nan tazo", juyawa yayi ya kalli Marwiyya yayi murmushi yace "zoki shiga idonshi biyu, amma banda hayaniya", gyada kai tayi ta karasa ta tura kofan dakin tareda shiga ta kulle.




       Abdul na ganin ta ya tsaya yana kallonta dan ya tabbatar cewar ba gizo take mishi ba, murmushin karfin hali ta mishi ta karasa ta zauna kan gadon tana kallonshi tace " sannu, ya jikin", murmushi ya mata tareda sauke wani wahallalen ajiyar zuciya ya mika mata hannunshi ba musu ta kama dan ta tausaya mishi bata taba tunanin haka ciwonshi yayi tsanani ba se yanzu.




     Idonshi cike da kwalla, murya na rawa yace "tinda na ganki naji sauki", girgiza mishi kai takeyi tace " yi shiru karkayi magana tinda maganar wahala take baka, yi shiru ina nan har ka warke", da ido yamata alamar "da gaske kike", ta kada kai tana son mayar da hawayen da ke kokarin fitowa.





     Murmushi ya mata ya kara damtse hannunta dake cikin nashi sannan ya rufe ido, sosai ta tsorota da taga ya rufe ido saboda duk wanda ya ganshi bazesa ran ze kai gobe ba, da sauri ta kira sunanshi tace " Mine",  bude ido yayi yana murmushi yace "nayi missing wannan sunan", murmushi ta mishi tareda sauke ajiyar zuciya tana kallo ya kara rufe ido kafin numfashinshi ya canza alaman yayi bacci.






        Deen ne ya leko yaga tasashi gaba se kallonshi takeyi yayi murmushi yace " mu zamu koma gida tinda kina nan, da daddare zan dawo seke ki koma", gigiza kai tayi tace "a nan zan kwana, in zaka dawo ka taho min da abinda zamu bukata", beson mata musu kuma yasan Abdul ma zeso hakan saboda haka yace " shikenan sena dawo", ta kada kai ya fita.






       Tana nan zaune ruwan da ake kara mishi ya kare wata nurse tazo tasa wani duk tana kallo, Allah ya wadar da hanlinta kawai takeyi a zuciya saboda koda ace ba abinda ya taba shiga tsakaninsu dan uwanta ne amma tayi biris da wannan tana zaune hankalinta kwance, shi yana nan yana kokawa da mutuwa. Wasu hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta goge, alwallah takeso taje tayi ta roka mishi sauki wurin Allah amma ya rike hannunta kaman za'a sace mishi ita, da kyar da wayo da dabara ta cire hannunta taje tayi alwallah tayi sallah.






      Se yamma likis Abdul ya tashi doctor yazo ya duba shi, yayi mamaki dayaga ciwon shi cikin 100% 50% ya tafi, murmushi yayi yace "sauki ya fara zuwa, ba mamaki mu sallameku zuwa gobe", godiya suka mishi ya fita sannan Marwiyya ta taimaka mishi yayi brush ya sha tea, yace mata yanaso yayi sallah, da taimakon ta yayi alwallah ya biya bashin sallolin da ake binshi.






       Da daddare Deen ya dawo ya kawo musu abinda zasu bukata da abinci sannan ya musu sallama ya wuce gida, da kyar ta samu yaci abincin kadan sannan taje ta shirya sukayi shirin kwanciya. Hannunta ya kamo yace " baby ki yafemin abinda nayi, wlh da nasan ranki ze baci bazanyi ba", murmushi tayi tayi pecking din goshinshi tace "na yafe ma, an na yarda zan koma gidanka", ware idanuwa yayi yace " da gaske", ta kada kai, ai murna a wurinshi ba'a magana, kissing dinta yayi kafin yace "nagode, bansan ya zanyi ba da baki koma ba, baby kece rayuwata, kece komai nawa, da sonki nake numfashi a doron kasa", murmushi tayi tace " base ka fadaba, idonka ya riga ya fada min komai", murmushi yayi yace "I love you, karki kuma cewa bana sonkin kinji", kai ta kada tace " kwanta, doctor yace ka huta sosai", kwanciya yayi ta gyara mishi blanket yace "ke bazaki kwanta ba", tace " sallah zanyi".






       Binta kawai yayi da ido har ta tada sallah da haka bacci ya daukeshi, itama tana idarwa ta kwanta a nan wurin batasan sanda bacci ya dauke taba.






      A gida kowa Deen na komawa ya dauki Amatullah suka koma gidansu tareda bude sabon shafin soyayya.






        Washegari doctor na duba Abdul yaga komai normal ya sallamesu tareda basu magunguna da shawarwari sannan Marwiyya ta kira Deen tace yazo ya kaisu gida.  Yana zuwa suka shiga mota Deen nata musu tsiya wai da Abdul bega Marwiyya ba da yanzu ya margaya.






         Abdul ganin sundau hanyar family house yace "ina zaka kaimu?", Deen yace " gida mana, bakaso kaga su mommy ne?", fuska ba wasa Abdul yace "ba yanzu ba, gidana zaka kaimu", Deen ganin bada wasa Abdul yayi magana ba ya sashi juyawa kan mota suka nufi gida, yana saukesu shima ya shiga gida.






TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now