BABI NA HUDU

2.1K 250 3
                                    

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Inna ta sauke, she thought she won't agree. But dama sanin da tama Habiba tasan she would never go against her words. Da dai Sakeena ce, toh that's where her problem lies.

"Nagode Hajia, zaki iya tafiya da wannan din; nan da kwana biyu zan kiraki ki tafi da dayar. Kiyi hakuri na bata maki lokaci," Inna ta fada haltingly, tana ta yaken dole. Amma cikin ranta, ta ayyana irin bakar azabar da zata gana ma Sakeena har sai tace zataje wajen aikin nan da kanta.

Under the bloodshot eyes of Tukur, matar steadied herself uncomfortably. "Babu wani abu ai, wannan dinma sai mu tafi da ita. Ita dayar duk lokacin data shirya, I'm a phone call away," tana fadin haka ta fara zira takalmanta, ta kare matse yar karamar purse dinta.

"To muje ko? Yanmata," ta kalli Habiba, offering a helping hand.

Habiba zuwa tayi ta rungume Sakeena tana mai zubar da hawaye, itama hugging dinta back tayi, they both can't stop their streaming tears. Ita Sakeena hada haushi ma Habibar take bata, tunda a chance of helping her out yazo; but she choosed to still work as a maid. Saidai sukasha kukansu kafin Habiba tayi hugging Tukur slightly, yadda taji yayi hugging dinta back ne was astounding; dan she never for once thinks he would be this caring in his life.

But one thing about him da basu sani ba; dukda kasancewar Tukur dan iska, dan daba; dan shaye-shaye, bai hada family dinshi da kowa ba. Dan kuwa he knew how they would rape different girls of different ages, even though he wasn't into the raping aspect, but his heart always pains at the sight of a broken girl being raped by his gang mate. That numerous sights of the girls, made him promised to take a very good care of his sisters, sai yasa ko waje ya gansu sai ya masu dukan tsiya ya korosu gida.

"Any slight thing da baki yarda dashi ba, I'm just a phone call away," yana fadin haka yayi breaking hug dinsu. Kamar ya sani, jiya cikin wayoyin da suka sato, bayan an raba an bashi nashi; sai yaki sayarwa, hakanan yaji he wanted to be nice to his sisters. Dan haka daya ya dauka ya dauko daga aljihu ya mika mata.

"Make sure you take a very good care of yourself," yana mika mata yayi patting kanta hade da yawing gaze dinshi to the other side. Dan seeing how she is crying breaks his heart.

"Na tafi Inna, zan kiraki sai ki bani Saky mu gaisa," ta fada hade da juyawa tabi bayan matar, wanda har takai bakin kofa tana jiranta. Da yake sun haddace Number din Inna da Baba, Tukur ne kam no one knows his real number, dan he can call you yanzu, within seconds ki kira kiji kashe.

Crestfallen, Habiba trudged out of their home___with different thoughts rummaging in her brain. Wani numfashi Inna ta sauke, ganin sun fita lafiya kafin ta juyo ta kalli Sakeena; seething with rage.

"Ke kuma wallahi you will regret it, da kanki zakice a kaiki gidan aikatau dinnan dan ubanki," tana fadin haka ta dunguri kanta ta wuce daki. Yunkurawa Tukur yayi da niyya damko hannu Inna dan ya kashe mata warning, amma Sakeena tayi saurin riko hannun, flashing him a pleading look with pouted lips.

"Karbi kema, nasan that's what you have been pouting for," ya ciro wata wayar daga aljihunshi ya mika mata.

Wani irin tsallen murna ta saki, dama she kept mute ne taga ko zai bata ko bazai bata ba. Saurin sakinshi tayi ta fara taka yar rawarta, tanata dan ihunta. Sauran matan dake gidan duk suka firfito, dan dama azabar tsoron Tukur ne yasa da ya shigo gidan kowacce zata shiga dakinta ta kulle, yanzu kuwa da sukaji ihun Sakeena sunsan baya nan, dan definitely da yana nan da batayi ihun ba.

Maman Iliya, wadda itace dakinta ke kusa da na su Sakeena, ita ta fara fitowa. Yaranta uku duka maza, sai mijinta wanda yake aikin carpentry. Ita kuma Maman binta dakinta ne na karshe a gidan, amarya ce batayi shekara ko biyu ba, Yar ta daya Fatima suna ce mata binta, mijinta yana aikin gadi ne a wato babbar ma'aikata. Dakunan duka a jere suke cikin long veranda din dake gidan.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now