BABI NA TALATIN DA UKKU

1.5K 222 19
                                    

"Tukur wallahi baka isa ba, kadai ji na rantse ko? To wallahi ko sama da kasa zasu hade sai Sakinah tayi tuyar awarar nan. Ubana ne kai wai? Yaro ji kake kaman ka haifi uban kowa! To ka fita idona tun ban maka rashin mutunci ba." Inna kenan, masifa take ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Tukur kuwa yayi kasake yana kallonta, dan kuwa yau garas yake babu sauran maye a tattare dashi.

Inna turned her attention back to a crying Sakinah, ita in akwai abunda ta tsana to bayan wannan kukan munafurcin da Sakinah ta koyo yake. Da duk bala'i baka ganin hawayen Sakinah, amma ta rasa gane yadda akayi daga zuwa aikatau yarinya mastered the art of being a lachrymose.

"Zaki daina wannan kukan munafurcin ko kuwa? Let me tell you, Sakinah ko jini zai rika zubowa daga idanunki sai kinyi tuyar awara kofar gidan nan, ko uban wa ya tsaya maki kuwa. Ke, ni bama sai naje naci bashin waken suya ba. Ina kudin aikatau din da suka biyaki? Maza dauko man su kuma inga babu ko sisi kici ubanki cikin gidan nan wallahi!" Cike da hargagi take maganar, har wata kumfa kumfa bakinta yake yi. Sakinah hadiye kukan nata tayi ta nufi hanyar dakinsu jikinta na rawa, dan yan awannin da tayi da safe ya tabbatar mata da zatasha bakar azaba a gidan nan.

Tukur ne ya dan matsa gefenta kadan, yana langabar da kai "Inna kina ma Allah da Annabi? Inna dan girman Allah ki hakura da zancen soya awararnan, wallahi irin haka ba karamar matsala yake ja ma yan mata ba. Kinga dole zatayi hulda da maza, tunda 80% of buyers din duk samari ne, ki taimaka kiyi hakuri a samo wani alternative din, Inna."

"Zaka matsa ka bani wuri ko sai na mauje ka, Tukur? Wallahi billahi ka kiyayeni! Ina ruwanka da hidimar da nakeyi nida ya'yana? Yau da kana kaunar Allahn kai ai da baka abunda kakeyi, ko kai yadda kake shirgegen gardin nan yaci ace kanada sana'ar da zata rika ciyar da mu, amma kabi hanyar iskanci. To bari in gaya maka, dama fita kayi daga gidan nan tun muna shaidar juna da kai, dan suyar awara ce wallahi Sakinah sai tayi ta, su mazan su saceta in sunso. Daga an rage man wahala ma."

Ganin dai da gaske tayi, kuma minti biyar idan ya kara a wajen Allah kadai ne zai iya kwatarshi daga masifar Inna, sum sum Tukur ya fita daga gidan, amma kwata kwata zuciyarshi bata mashi dadi. Ba yadda zaiyi ne amma tabbas daya tsaida wannan kudurin na Inna.

Tana fitowa taga babu Ya T, nan hankalinta ya tashi, dama all her hopes were on him. She knew he has the ability of stopping Inna from whatever it is she has her mind on. Amma rashin ganinshi a yanzu ya tabbatar mata Inna has won. Ta zama mai tuyar awara, not a maid anymore.

"Inna ga kudin," a hankali ta furta hakan tana mai mika ma Inna kudin. Jiki na rawa Inna ta saka hannu ta karbi rapper din yan 500 din tana waige waige.

"Yanzu Sakinah akwi irin wannan kudin a tare dake shine tun jiya baki bani ba? Kai amma wannan anyi yar banza. To yanzu kinga, ga 2k nan jeki siyo tiyar waken suya da mai. Nan zan samu yaro yaje bakin titi ya siyo mana barkonobda kayan hadi, anjima sai a siyo icce ko? Yi maza Sakinah."

Hawaye Sakinah ta kara sharewa, ganin yadda Inna jikinta har rawa yakeyi. "Yanzu Inna duk abunda kike bukata wannan kudin bai isheki ba? Inna dan Allah ki rufa man asiri, wallahi har ga Allah banasan tuyar awarar nan."

Wani irin gigitaccen mari Inna ta zabga mata a left cheek dinta, fuskar nan daure mutuk. "Zaki wuce ko sai na babballaki? Kina alamar ina wasa ne?"

Cikin hanzari Sakinah ta saka hannu ta karbi kudin, dama da hijab a jikinta direct kofa ta nufa, hawaye na zarya saman kuncinta. Batafi minti biyu tana tafiya ba ta hango Ya T fuskarshi bab annuri yayo wajenta, karbar kudin yayi ya lallasheta kafin ya umurceta data zauna saman wani dakali yaje shagon ya siyo ya dawo.

She sat down a saman dakali, crying her eyes out. Ita ta rasa gane wannan wace irin rayuwa ce, fisabilillahi ace duniya mutum mahaifiyarshi bata tausayinshi ko kadan? Ta ma bata chance din da zasuyi wata magana ta jin dadi koda da five minutes ne Inna bata tabayi ba. Tana zaune tana tunaninta sai taji an zaune gefenta, dago fuskar da zatayi taha ashe Ya T ne fuskarshi was glum shima.

"Haka Allah ya jarabceni ko, Ya T? He wants me to live like this without getting any form of love or compassion from my mother? Wallahi abun nan pains me alot, ji nake kamar duk dunia nafi kowa rashin sa'a Ya T. Kaga ko? Abu yana damuna dani kaina bansan menene ba amma I have no one to voice it out to, bansan exactly abun ba balle na fadawa anyone. She was the one meant for that, to depict our worries and ease them off with words. Amma Inna will always be a reason for my tears, she has never consoled me or shown any form of affection towards me. Duniya bata da dadi Ya T, gashi Habibah ma bansan inda zan fara nemanta ba, I need her."

Numfashinta har wani sarkewa yake, kuka take kamar ranta zai fita, so take even for a second to cut off her heart so she could feel at ease. Ji take gaba daya rayuwarta babu wanda ya kai ta shiga cikin kunci da tsananin damuwa, abun takaicin ma bazata ce ga ginshikin damjwar ba, ta san dai Inna has almost 40% a ciki.

Hannayenta duka biyu ya riko, if looks could cry, Tukur would've been crying by now. But she could see he was trying to suppress his sadness to be able to console her. Magana ya fara mata cikin natsuwa da kwantar da hankali kamar ba Ya T dinsu ba wanda babu wanda zaice akwai sauran hankali a tattare dashi banda shashanci.

Kallon kasko da itacen dake gefenta takeyi, gashi dai ta zauna saman kujera, and everything she might need was supplied by Inna, amma ta kasa koda motsa hannu daya ne. Adding more salt to the bleeding wound, yan unguwarsu had been giving her weird looks, dan har kiran abokansu suke azo aga kanwar T zata fara saida awara.

"Na tsaneki." Muryar dataji kenan cikin kunnenta that was doing all it takes to block away the hushing voices na mutanen dake gefenta.

Yace ya tsaneta, yes she knew that from the first day they met. Amma yau tuna kalmomin nan biyu had stirred up an adorned wound in her heart. Tunda ya tsaneta ai kowa ma zai iya tsanarta, dan gata ne shi, duk abunda yake so yana samunshi, babu mamaki shi yasa kowa ya tsaneta a rayuwar ta. Miye amfanin barin kunci a zuciyarta? Why would she let herself drown into an ocean of depression when she has no one waiting for her at the shore to even realize she has drowned?

"It's over from today." With a new form energy, a new determination, she set to work. She's done doing things to please anyone, zata koma Sakinar ta ta baya, Sakinar da kowa ya sani, wacce ko duniya zaka daura mata saman kanta bazata taba bari hawayenta su sauka a gabanka ba, Sakinar da ta addabi kowa, Sakinar da bata gani tayi shiru, Sakinar da kana ce mata kule zata ce maka cas! She's back to that Sakinah, the old Sakinah Abdullahi Bello.

Waka ta fara rerewa cikin sautin da kunnenta kadai ne zai iya jiye mata, tanayi tana hada wutar har saida ta tashi kafin ta dora kaskonta ta kuma zuba mai tana jiran yayi zafi. Ta kauda damuwar komai, dan barin kanta ciki ma baya da amfani, amma ta kuduri niyyar sai ta kuntata ma kowa kamar yadda suka mayar da rayuwarta rana zafi inuwa kuna.

Tana cikin suya wasu yara sukazo, su uku ne kowanne da naira ashirin hannunshi, mika mata sukayi ta karba fuskar nan babu yabo ba fallasa. Bayan ta zuba masu tana cikin kwashe wani kaskon ne wayarta dake gefenta ta fara ringing, dubawa tayi taga Aunty Halima ce, and a smile instantly broke her lips.

"Auntynmu ina yini?" She greeted, har fikin ranta taji dadi.

"Haba Sakinah ai ni nayi fushi, wai ace har yanzu ko ki nemeni kice ya nike? Ya aikin gida da komai?" Fara'a ce kwance under Aunty Halima's tone.

"Wallahi ba haka bane, ban samu natsuwa ba ne sai yanzu. Auntynmu ya gida? Yaso Kamal da Hafsah?" Akwai wanda take san tambaya amma tasan as much as weird it sounded to her heart, it will be much weirder to Aunty Halima's ears.

"Kowa lafiya lau Sakinah, duk muna lafiya. Baki tambayeni abokin fadan ki ba." Sosai Aunty Halima take dariya, harda saka speaker dan kuwa suna zaune a falon part dinta da yara sai Arhaan.

"Haba Aunty wannan ai na bar gidan sai ya huta kuma ko? Tunda mun bar fadan." There was a twinge in her heart at the mention of him.

"Aikau yana nan tunda kika tafi ya koma old self dinshi, ni dama bamusan yana fada ba saida kikazo, magana me karfi ma ba yinta yake ba, to yanzu dai the old Arhaan din Mama is back."

"To kice nace mashi aita shawagaba lafiya, yanzu babu mai gaya mishi bakar magana har ta sakashi yin fada." Komai a kan kunnenshi akayi, kalmar aita shawaga lafiya hakanan ya tsinci kanshi da yin murmushi. Sakinah Abdullahi Bello will never change.

I'm soo sorry dan Allah

I was hooked up with abubuwa ne wallahi.

Ramadan kareem and Juma'at mubarak.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now