BABI NA ARBA'IN DA HUDU

1.7K 245 39
                                    

Yadda kasan an bude tap din ruwa haka eyes din Sakinah suka koma, kuka ta cigaba da rizga har cikin kasan ranta, duk wani kunci data dade tana kunsa ta fara saukewa ta hawayenta, karshe ma dai da abun taga nayi ne sai kawai ta kifa kanta da kujera ta cigaba da aikin hawaye. Arhaan kuwa tsaye yayi yana kallonta, dan shi a wajen nan baiga abun kuka ba, amma da alama bawai abunda ya mata kadai bane ya saka ta kuka, danshi duk wani samfarin kuka to ya sanshi. Wannan kukan nata akwai wani abu a kasa.

Daya gaji da tsugunni dan kanshi ya zauna saitin ta ya cigaba da kallonta baice uffan ba, she looks like someone that has thousands of worries with no one to talk to, shiyasa ko yunkurin tsaidata baiyi ba. Irin haka mutum is better yayi kukan if not depression might set in, wanda he doubt if she isn't depressed yarinyar nan.

Ganin kukan nata ya tsagaita yasa yayi gyara murya, wanda hakan yasa ta dago ta kalleshi. "Feeling much better?" Abunda ya furta kenan, kawo yanzu ya fara damuwa da irin dabi'un shi pertaining Sakinah, he thought he promised her life a living hell ko? Why the soft acting toh?

Nodding kanta ta shiga yi kamar wata yar yarinya tana sauke ajiyar zuciya, ita kanta mamakin Arhaan dinne cike fal da zuciyarta, amma sai tayi tunanin may be Mama take saka shi hakan. Baiyi mata murmushi ba balle tayi tunanin akwai kanshin rahama, mikewa tsaye yayi yana mai zura both hands dinshi cikin aljihu.

"Good. Na kyaleki ne kinyi kukanki saboda I know how it feels to be interrupted while pouring your heart out, amma hakan bazai saka na chanza abunda na fada ba. No Tv, kina ji na?" Yadda ya daure tamau kai bakace shi ne yayi magana cikin sanyin rai ba dazu. She gulped down a lump and nodded her head at him, zuciyarta har wani dukan tara tara take, cikin seconds har ya dawo mata a monster din data sanshi. "Naji."

Bai kara kulata ba ya fita, retreating back dinshi ta tsaya tana kallo, how destiny played a role in her life, ita ko a mafarki akace mata zata auri Arhaan ai sai ta yini tana karyata kanta, amma sai gashi yau she's a wife to Arhaan, even though they act nothing like a couple would, she can proudly call herself Mrs. Arhaan Zubayr.

Haka kawai taji wani murmushi ya kufce mata, tunawa da tayi kuma halin da take ciki da ukubar da take fuskanta da wadda babu makawa tasan dole sai ta fuskanta, sai taji hawayenta sun dawo sababbi wadan da sukafi wancan kunci da bakin ciki. Ita yanzu gashi ko wayar arzikin ma bata da ita balle har ta samu ko Inna ta kira taji dadi, dukda tasan Innar ma kanwar ja ce, amma a mother is a mother no matter what. Tunani ta farayi ina zata samu waya ta kirasu, tunda ta taho da book din datake rubuta numbers a ciki.

A bangaren Arhaan kuwa yana fita gidan Mama ya wuce, saida ya fara tsayawa part din Mommy sukasha fira dan har kunu saida yasha wajenta kafin ya mata sallama ya wuce wajen Mama, tana zaune tana kallon zee tv.

"Badai ku gajiya ko, Mama? Salamu Alaikum." Ya furta yana karasowa living room dinta, kallo daya ta mishi ta juya ta cigaba da kallon tv hannayenta saman chest, kunsan indian series yadda suke kaji kamar dakai akeyi. Hakan yana daya daga cikin abunda ya kara rura wutar tsanar indian series a heart din Arhaan, yadda Mama takan share 20 minutes ko fi bata kulashi ba indai tana kallonsu.

Sai can dama episode din yazo karewa, saida ya kare kafin ta juyo da murmushi kan fuskarta tana me furta "Yi hakuri Dan Mama, I was carried away ne wallahi, nidai nasan babu yadda za'ayi Aditya ya...." zata fara bashi labarin yayi saurin katseta "Su Zoya ne da adityan ko? Mama naji labarinsu har nagaji, tun anayi zee world na kalla ta bakinku. Yanzu dai ina kwana?" Yayi tambayar yana kwantar da kanshi kan laps dinta.

Suna cikin firar jin dadi sai ga Baba ya shigo da sallama kan lips dinshi, ba kasafai yake shigowa parts din matanshi ba sai idan da wani abun, sororo ya tsaya yana kallon Arhaan sai kuma yaja siririn tsaki, "Wallahi bazaki taba dainawa ba, yanzu wannan yaron harda auren nashi? Haihuwa bana ko bad'i amma shine yake kwantawa kan laps dinshi? Kai dallah tashi, ni karma na sake ganin kazo gidan nan idan ba on fridays ba, fridays din ma da daddare sai anyi month da bikin ka tukunna. Yaro girma kake amma bakasan kanayi ba? Ita diyar mutane daka bari can gidan dan bata da uwar da zata hau kan laps dinta ne ko me? Arhaan wallahi ka fita idona." Ganin Baba ya rufe ido ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba yasa Arhaan ko sallama baima Mama ba ya wuce ya fita, yasan dai yau Mama zatasha mita. Duk san da Baba yake mashi bai cika nuna mashi kamar yadda Mama take yi ba, dan tsab sai ya rufe ido yai mashi tas, yanzu gashi ance sai fridays da daddare.

Bashi da wajen zuwa, shi ba wasu friends din arziki ba, su dinma yasan yanzu suna wajen aiki, gashi yawo da rana a abuja baida dadi, dan dole ya koma gida kuma direct part din Sakinah ya nufa. Badai Baba yace ya daina barinta ita kadai ba? Here we go, sai ta kirasu tana kuka akan su barshi ya rika zuwa wajen Mama tsabar azabar da zai mata.

Yana isa ya jiyo sautin muryarta saman dining din, waka take a hankali tana kurza carrot ko lura da ya shigo batayi ba. Cikin murya mai sanyi mai cike da dumbin damuwa haka take rera wakar, kan kujera Arhaan ya kishingida, tun yana jiyo sautin muryarta har bacci ya daukeshi, dama jiya baccin rabi rabi ne.

Sakinah saida ta gama hada lunch dinta da komai har tazo zata rage lights din falon taje tayi wanka da sallah sai ta ganshi kwance sai bacci yake hankali kwance. With so much hesitation ta taka ta isa inda yake, dan tun dazu taji an gama sallah gashi yanata bacci, moreover; she doesn't trust har ta shiga tana wanka shi kuma yana bacci a falon, he might enter her room bata sani ba.

Wannan tunanin yasa tayi hanzarin karasawa wajenshi hade da patting kujerar da yake, baiji ba; hakan yasa ta dan taba shoulder dinshi. What she didn't know was that Arhaan yana cike da mafarki mai ban tsoro, aikau sai yaji ta dafashi kamar da gaske, wani irin kukan kura da yayi ya finciko ta dan dole ta fada jikinshi, jin ya rike abu yasashi rungumeta kam cikin jikinshi kuma ya koma baccin.

Dama haka yake, yana da yawan mafarkan tsoro tun yana yaro kuma duk lokacin dayayi to a haka zasuyi bacci yana kankame da Mama, lokacin daya girma ne zai kirata a waya duk a rude haka zata rinka mashi addua har sai wani baccin ya kuma daukarshi. Wannan shine dalilin dayasa duk idan ya fara bacci to kamar an zare ma mutum rai haka yake, magana mai karfi ma baya santa dan gudun kar ya koma baccin yayi mafarki, kuma hakan ya bishi har girmanshi.

Gashi dai a kwance ita kuma ta rufa mashi baya kuma ya kankame ta kamar ance za'a kwaceta yasa jikin Sakinah ya fara bari. It's not like batasan miye aure ba, Aa, saidai duk wadda akayi raping a rayuwarta balle ita at her age dan ko wata biyu ba'ayi ba dole duk wani kusancinta da da namiji ya sanya ta cikin tashin hankali, balle ita raping din nata ba mutum daya ba har 4.

Kici kicin kwace kanta takeyi amma ta kasa, nan take sai ga hawaye suna sauka directly saman chest din Arhaan, cikin shashekar kuka ta fara magana "Arhaan dan Allah kayi hakuri, wallahi tunda ka tafi ban kunna tv din ba, dan Allah ka rabu dani sallah zanyi." Tama rasa dame zata rokeshi ya rabu da ita, itadai burinta ya kyaleta.

Cikin bacci ya bude eyes dinshi wanda yayi sanadiyar saukarsu daidai cikin na Sakinah, with his hands wrapped around her waist, wani tsoro ya shigeta dan dole ta kulle nata idanun. "Babu abunda zan maki kinji? Mama does this to me, I'm having a bad dream, hold on for a moment please." Bakinshi rawa yake cike da tsoro, dan har yanzu jinshi yake tsundum cikin mafarkin shi.

"But..." she tried to protest, but he cut her off with a pleading tone she had never imagined Arhaan to have.

"Please Sakinah, just five more minutes I promise, I just need to calm down if not I might pass out." Yayi maganar a hankali yana mayar da kanshi hade da rufe eyes dinshi.

Sakinah had no choice, dan dole ta dora kanta comfortably saman chest dinshi and closed her eyes too, she needs to calm down her nerves as well.

Hey guys! How's the book going?!

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now