BABI NA SITTIN DA BAKWAI

1.6K 231 64
                                    

Zarya takeyi cikin falon gidan, sai kai kawo take ta rasa inda zata saka ranta, masifar da Hajiar take mata ba itace abunda yake tada mata hankali ba, abubuwan da take fada mata sunfi komai daga mata hankali. Kwana biyu kenan da barin Habiba cikin gidannan, amma sam abun bai kawo mata na ta fadawa Hajia halin da ake ciki ba sai yau.

"Haba Hajia hauwa, ban taba tunanin zafin ranki yakai na har ki aikata irin wannan abun ba. Wane kalar kashedi ne ban maki ba akan yarinyar nan? To yanzu dana kira Malam cewa yayi inhar aka bari ta hadu da wani daga cikin danginta to fa asirin mu na kanta wanda zata mance da ko ita wacece zai kare, daga nan kuma wanda kikayi mata dama rawa yakeyi yanzu, har gaba da abada tabar harkar nan tamu. Sai kisan nayi, nidai banda asara, ke kika jiyo." Koda Hajia ta gane cewar Maama ga harkar data saka Habiba ba karamin yaki sukayi ba, dan kuwa Habiba kowa rububinta yakeyi, dan dole Maama ta yanki wasu kudade masu tsoka ta bawa Hajia kafin ta tsaida gobarar.

Maama palming face dinta tayi, duk ta gama rikicewa, "Nasan insha Allahu ma babu abunda zai faru, bazata hadu da kowa ba. Ba kince can cikin garin kaduna aka daukota ba? Inada tabbacin hankalinta bai taba bata kaduna, ko zata buga saidai su lagos ko tabar kasar gaba daya. Yanzu nikam ya zanyi da her excellency? Sai kirana take akan taji in yau din zataje." Hankalinta duk ya gama tashi, taga samu kuma taga rashi kururu.

Wani irin tsakin takaici Hajia ta saki, "Wannan kuma duk mai sauki ce, kice mata yarinyar ce bata jin dadi, ta turo maki kudin jirgin da komai zaki idan taji sauki zaki turota da kanki. Harda new tips duk zaki ma koya mata." A haka sukayi sallama, nan take Maama ta kira matar ta shaida mata, bata nuna rashin jin dadinta ba nan take ta turo ma Maama makudan kudade akan a kaita asibiti da kuma sauran expenses siyayyar da takeso kafin tazo.

Daya daga cikin yaranta dake lagos ta tura ma picture din Habiba akan ta saka a fara bincika mata ita, a nan kaduna ma ta tura, hankalinta kwata kwata bai taba kawo mata Abuja ba. Dama gidan wata hajia zataje, nan take ta sabi gyalenta ta fice. Dukda yanayin da Saahir yake ciki yana damunta, amma she has nothing to do about it.

A bangaren Habiba kuwa, kwananta biyu a cikin Abuja amma kullum cikin gararamba take, ita bata yarda da hotel ba, gani take idan har taje ta kwana a hotel to tabbas dole wani ya alakanta ta da mummunan aiki. A ga budurwa kamarta, ga mota kuma ta shiga hotel? Ita kanta bata yarda da kanta.

Cikin mota take kwana, kuka kuwa babu irin wanda batayi ba, burinta bai wuce ta tuna ita din wacece ba? Dan tawa kanta alkawari ko a kufai iyayenta suke zataje ta zauna dasu. Saidai ta shiga wannan eatery taci abinci ta koma wancan taci.

Wajen 9pm ta tsaya bakin wani eatery, ta sayi abincin amma bata ma iya cin abincin, duk wata damuwar duniya babu irin wacce bata shiga ba. Dakyar taci lomar da bata wuce biyar ba kafin ta biya kudin abincin ta fita ta shiga motar ta. Yau a nan zata kwana, dan she thinks of no where but there.

Ganin yanda mutane ke shigowa suna farin ciki da annushuwa, wasu families ne, wasu newly weds ne, wasu kuma saurayi ne da budurwa, wasu ma friends ne ko abokan kasuwanci, na families din yafi tsaya mata a rai. Haka kawai taji duk wani tarin damuwa ya dawo mata cikin rai, kuka ta farayi kamar da bakin kwarya. Jikinta babu inda baya kyarma. Saahir takeso tayi magana dashi amma ba dama. Duk tunaninta bai wuce inda zata samu matsugunni ba. Babu wanda xai taimaketa a haka yanda take dan kowa zai kawo ma ranshi yar iska ce. Idan tace ta kama gidan haya kuwa nan ma bazata tsira ba, idan tace ta saida motar tayi basaja akan bata da arziki ina iya cutarta tunda ba wai kan dukiyar ta sani ba.

Bata da madafa, haka zalika bata da kowa sai Allah sai kuma Saahir, shi kuma yanzu ya juya mata baya. Ana haka taji an hasketa da fitilar mota, a hankali ta dago rinannun idanunta ta saukesu akan wacce ke gaban motar da kuma namiji wanda shi yake tukin alamar mijinta ne.

Fitilar ya kashe ita kuma ta cigaba da kukanta, no one in this world cares, dan haka itama bata damu da abunda kowa zaice a kanta ba wai dan an ganta tana kuka. Kowa dai tashi ta fisheshi.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now