BABI NA SHA TAKWAS

1.5K 227 16
                                    

Kadan kadan Sakinah ke jiyo sautin magana kamar a cikin mafarki. Slowly ta fara squinting eyes dinta domin tabbatar da abunda take tunani, alas! Sai idanunta suka sauka a kan fuskar Baban Shaheed-wacce take daure kamar yaga mutuwarshi, ga kuma Aunty Halima a gefenshi ta rike baki kawai_dan daga gani a tsure take.

Niyar motsawa tayi dan ta mike amma sai jinta tayi tsamo tsamo cikin fitsari. Tashin hanklai! Wanda ba'a saka masa rana. Ai kawai komawa tayi ta kwanta sai hawayen da suka fara zarya saman fuskarta. Basuyi magana ba haka kowannensu ya fice yabar dakin_amma tana jiyo sautin muryar Baban Shaheed cikin karsashi alamar yana fada.

Likib ta karayi cikin katifar, kuka ne kawai takeyi me cike da kunci da bakin ciki. Duk laifin Inna ne, yau da bata tilasta mata zuwa wajen aikin nan ba da tanacan asirinta rufe. Amma me yakai wannan bakin ciki? Me gida ya ganka kwance male male cikin fitsarin kwance? Ita ba yarinya ba ba komai ba. Tasan this calls for a huge humiliation.

Das! Gabanta ya fadi, tunawa da tayi tabbas indai Baban Shaheed ya sani to babu shakka sai wancan Dan Shagwaban yaji labari_dan daga gani suna d'asawa sosai ba kadan ba. Dakyar ta samu ta lallashi kanta kafin taje ta tsaftace jikinta ta gyara dakin, amma fa katifar jagab take kamar an mata ruwan sama.

Qur'anin data ganin tun farkon zuwanta gidan_wanda ya kasance dashi take amfani; ta dauko ta fara karanta, dan tasan a fadin duniya babu mai yaye mata damuwarta bayan Allah madaukakin sarki.

Sai can shida na safe ta dan gota ta ajiye ta fita zuwa kitchen jiki duk a sabule_ji take kamar ta rufe ido ta ganta cikin gidansu. Tana shiga kitchen da niyar daukar tsintsiya ta hango Aunty Halima na aiki; dukda dai safiya mutum dama bai cika walwala ba_amma she's sure yau akwai abunda yake damun Auntyn tata.

Karasawa tayi ta gaisheta, saida aka dauki mintuna kafin Aunty Halima ta amsa gaisuwar tana cigaba da aikinta. Ita duk ba abun fitsarin bane yafi damunta, hukuncin da Mama zata yanke a kanta shine ke damunta, dan yadda tasan Arhaan tasan tabbas dole ya fadawa Mama abunda ya faru.

Tunda Sakina take a duniya bata taba yima kowa ladabin da yaci sunanshi ladabi ba, amma yau Sakina ce hada durkusawa kasa kan guiwowinta tana magana cike da tausasawa. "Auntynmu dan Allah kiyi hakuri, nasan abunda nayi ban kyauta-amma dan Allah ki yafe man_Insha Allahu hakan bazai kara faruwa ba. Kuma nasan Babansu Shaheed ya maki fada saboda abunda ya faru dazu da asuba ko? Kiyi hakuri dan Allah_nasan ma kila cewa zaiyi in bar gidan," tana magana ne ciki da kaskantar da kai, idanunta kyam saman tiles din dake malale kasa_ta kasa koda daga ido ta kalli fuskar Auntyn tata.

Dago da ita tsaye Aunty Halima tayi, saida ta goge mata hawayenta kafin ta fara magana "A gaskiya Sakinah abunda kikayi yau da ace watace kika mata haka wallahi kafin kibar gidanta sai ta nada maki dan banzan duka. Kuma ni kinga abunda make gudu bansan hukuncin da Mama zata yanke akan abunda kikayi ba_dan bata yarda komai ya sami Arhaan ba. Maganar Baban Shaheed kuma na rokeshi ya bari ko wata daya kiyi_to yanzu mun daddale akan zaiyi tunani. Karki kara maimaita makamancin abunda kika ma Arhaan, Sakinah, kina jina ko?"

Saida ta kara ma Sakina fada sosai, wanda cikin kwanciyar hankali takeyinshi babu hargagi kafin ko waccensu ta kama aikin daya kamata tayi. Sakinah yinin ranar a d'add'are tayishi, dan kuwa gani take a ko wane yanayi Baban Shaheed na iya zuwa ya mata rashin mutunci; shi gogan ma ko gilminshi bata gani ba.

***

Tukur ne a tsaye tsakar gidansu, sai bulayi yake da alamu yasa yayi nak. Idanunnan kuwa sunyi jaa kamar garwashi, sai surfa zagi yake kamar Allah ya aiko shi. Su kuwa su Maman Iliya da Maman Binta tunda ya shigo gidan suka nufi dakunansu suka gark'e, dan sunsan halinshi sarai yanzu sai ya kamasu ya masu bugun tsiya_in har suka bata mashi rai, kuma koda sun fada ma mazajensu suma zanesu yakeyi.

Tunda ya shigo ya fara balai, Inna dake wanka a toilet kusan kurma ihu tayi, dan tasan yau yan rashin mutuncin nashi ne suka motsa. Koda ta fito da daurin gaba da bucket dinta a hannu bata ko kalli inda yake ba ta karasa tayi alwalla. Tana niyar shiga daki ne taji maganarshi gab da ita_har wani huci yake kamar wanda aka kashema uwa a gabanshi.

"Kai lafiya? Zaka wuce ka bani waje ko sai na bubbugeka?" Tsabar karfin zuciya irin na Inna, bata taba yadda ta nuna mashi vulnerable side dinta. Kallonshi tayi kyar kamar da gaske zata iya bugun nashi.

"Na rantse da sarkin da yake busan numfashi; yau idan baki kira matar da ta kai yarancan wajen aiki tazo ta kaini gidajen ba wallahi za'ayi kanyar da ba dadi_dan aradun Allah sai jikinki ya gaya maki," har wani zillo yake yana daga hannu sama alamar da gasken fa tsaf zai iya nada mata na jaki.

Galala Inna ta saki baki tana kallonshi, ganin zai saida mata hali gaban Alumma yasa kawai ta saka kai ta shige daki, nan ma bata tsira ba dan saida ya kara binta yanata surutai.

"Kai wai baka fita in saka kaya? Ko tsaye zaka man in saka agabanka? Iyeh? Tushen marasa ta ido? Dan banzan yaro sai bakin rashin mutuncin tsiya." Balai ta fara ta inda take shiga bata nan take fita ba, dama abun ya fara mashi nauyi; bacci kawai yakeso yayi_bai tsaya ma ta ida ba yasa kai ya fice yabarta tsaye.

Koda Inna ta gama shirinta tsaf saida ta kira matar nan ta shaida mata akan ta taimaka taje gidajen da takai su Sakinah aiki, tanaso a bata lambobin matan da suke ma aiki. Tasan dan ya fita hakan ba yana nufin karshen maganar ba, dan sarai tasan halin Tukur_ko ba yau ba sai ya kara tado maganar su Sakinah, kuma next abunda zai fara ita tasan bazai mata kyau ba.

***

Habiba ce ke goge goge cikin falon gidan, jin anyi sallama yasa hankalinta ya koma kan matar dake shigowa tana jifanta da murmushi kamar ta santa. Gaidata tayi kafin ta fada mata bari ta kira Hajia.

Koda ta shiga dakin Hajiar, a halin data samesu ita da Ramcy kwata kwata sai taji duniyar ta mata zafi, amma haka ta daure tayi gulping back tears dinta ta fada ma Hajiar cewar bakuwa na jiranta. Kallon da taga Ramcy na jifarta dashi ne yasa tayi hanzarin barin dakin ta koma falo batare da ta jira amsar Hajiar ba.

Tana shiga matar nan ta kara washe hakora "Dama Innarku ce ta aikoni, tace inzo inga ya lafiyarku sai kuma in karbar mata number Hajia," ta furta cike da sakin fuska.

Scrunching up face Habiba tayi, bata gane Inna ba kuma. Ita inama ta san wannan matar balle wata Inna? Gaskia she is mistaking. "Kiyi hakuri baiwar Allah, amma ni banda iyaye, Hajia ce kadai uwar dakina_ko kinyi batan kai ne," duk a daburce take maganar. Wane Inna kuma? Kuma yadda matar take magana irin su biyu dinnan.

Kamar bakinta zai fado haka take kallon Habiba mamaki fal ranta. "Ke yarinya bansan wulakanci dan kin ganki gidan masu akwai. Yanzu Innar taku kike nufin kin manta ko kuma yar'uwar taki Sakinah? Kai kaji man yarinya da wulakanci."

"Kiyi hakuri dan Allah, amma ni bani bace..."kafin ma ta ida maganar sai ga Hajia, yadda taga hankalin Hajia ya tashi ganin fuskar matar yasa tayi hanzarin barin falon ta wuce dakinta.

Hajia zama tayi kusa da matar, kamar yadda ta fada ma Habiba haka ta kara zayyana ma Hajia. Ai nan da nan ta murtuke fuska, amma dayake yar duniya ce sai ta dauko rapper yan dubu dubu har guda biyu ta mika ma matar nan, da mata kashedin ko area din unguwar karta sake zuwa balle gidanta. Sannan kuma idan Iyayen Habiba sun kara nemanta ta shaida masu sun tashi daga gidan data kawota-sunbar garin ma gaba daya. Inma da hali ta chanza layin wayarta.

Ganin dai matar na neman yi mata gardama yasa Hajia sauke mata naira dubu dari biyar da karin kayyaki! Haba! Duniya sabuwa, cikin rawar jiki ta debi abun arziki tana shaidama Hajia ai ba chanza layi ba, har garin ma barinshi zatayi gaba daya ta koma wani garin.

Habiba na shiga dakinta taga wutar a kashe, ita kuma a iyakar saninta a kunne tabar wutar dakinta. Kunna wutar da zatayi ta hango Ramcy haihuwar uwarta shame shame saman gadonta, take kwakwalwarta ta fara yamutsawa, ganin Ramcy na nufota yasa cikin zafin nama-ga hawaye na zuba babu kakkautawa_haka ta nufi kofar fita bawai dan tasan inda take jefa kafafunta ba.

Saheer kuwa wanda Maama ta aikoshi ansar sako wajen Hajia, ji yake kamar ya hadiye ranshi dan bakin ciki_haka ya tako yazo har bakin kofar da jiyar kwankwasawa-amma kafin ya kwankwasa yaga an bude kofar cikin hanzari. Baiyi aune ba yaji an fado jikinshi hade da kankameshi_kuka take kamar ranta zai fita_bawai dan tasan akan wanda ta fada mawa ba. Kawai zuciyarta ta bata cewa she would be safe with whoever it is.







How are you all doing? Littafin kuwa yana dadi? Ina jiran ra'ayoyinku.

Nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now