BABI NA ARBA'IN DA DAYA

1.6K 233 41
                                    

Instead ya amsata tsaki yaja kafin ya zauna saman one of the chairs, kallon warmers din yake amma kuma ya kasa magana, yasan dai tabbas ba ita ta dafa abincin ba-shi in baccin Mama rights din data rubuta mashi da wanda ta fada mashi da bakinta na Sakinar dake wuyanshi ai da babu abunda zai zauna yanayi a nan. Mama dai wallahi ta gama dashi.

Mikewa tsaye Sakinah tayi bayan ta goge hawayenta, daga gani kasan daurewa kawai takeyi amma kukan dake cinta yafi karfin hawayen dake zubo mata. Tasan dai zaman da yayi jira yake tayi serving dinshi, not that dan ya dauketa wani abu a rayuwarshi, but because that's what he grew up to. Serving dinshi ake.

Saida ta bada yar tazara tsakaninsu kafin ta tambayeshi "Me zan zuba maka?" Jikinta har rawa yake, tasha jin ance idan akayi raping mutum if she's too sensitive zata koma tsoron maza, sai yau gashi itace ke tsoron maza, mazan ma wai Arhaan wanda ada ko kallon mutunci bai isheta ba.

Ko dagowa daga kan wayarshi baiyi ba balle ta saka ran zai amsa mata, hade hawayenta tayi kafin ta zuba mashi solid food din a plate tayi thrusting gabanshi, kunin gyada ne ta zuba mashi a cup ta mika mashi; daidai lokacin da Arhaam yaji kamshin gyadar ya cika mishi hanci ya miko hannu da niyar ya dauki cup din sai ya hada da nata hannun.

Wani razanannen ihu Sakinah ta saki, batasan lokacin data sakar mishi cup din ba ya fashe a kashe having kunun ya zuba a saman legs dinshi. Baya baya take tana kuka kamar ranta zai fito, hannunshi dataji akan nata ba karamin tuno mata da the most horrific moment of her life yayi ba. Bata ida recovering daga fargabar ba kawai taji ya karaso gabanta hade da sauke mata lafiyayyun maruka guda biyu; hawaye kan hawaye haka suke bin kuncinta a inda har ya fara magana bata sauke idanunta a kanshi ba.

"Baki da hankali ne? Ke dakikiyar inace? Ko yarinya ce ke da zaki saki cup ya fadi ya fashe kuma abunda ke ciki ya zuba? Kuma kukan me kikeyi haka? Kina ciki man kunne kamar wata wadda akayi ma rasuwa. Zaki maido hankalinki cikin kanki ko sai na saba maki da safiyar nan? Sakarya kawai!" Wata irin tsawa ya daka mata wacce tasa dan dole Sakinah ta hadiye duk wani kuka nata amma jikinta babu inda baya rawa, ita gani take shima raping din nata zaiyi, gani take shima zai mata abunda har ta mutu bazata manta ba, tabo zai mata irin wanda ko ruwan duniya zai kare bazata taba wanke shi ba.

Duka hannuwanta takai saman lips dinta domin kare kukan dayake tunkurarta "Kayi hakuri dan Allah, wallahi ban sani ba." Babu abunda take buri daya wuce taga ya wuce ya koma ta inda ya fito.

"Rike hakurinki banaso, abubuwa nawa kika man da suke bukatar hakurin baki bayar ba sai yanzu dan munafunci ko? To ki sani wani sorry face dinki da wasu crocodile tears dinki will never make me pity you, not even a bit. I want you to always have this in mind: I hate you with passion, tsanar da bana tunanin akwai irinta a duniya. Sannan kuma, daga yanzu babu yar aikin da zata kara daga maki ko da tsinke ne cikin gidan nan, kina yar aiki har wani matsayin samun yar aiki kike dashi? Ke ko kunya ma bakiji ba? Ki tabbar kin kara gyara ko ina cikin gidan nan kafin na dawo, wawiya kawai." Yana kaiwa karshen maganarshi ya wice part dinshi daga nan bata kara jin koda motsin rai ba.

Durkushewa tayi kasan bare tiles din palon ta saki wani gunjin kuka, ko kusa marukan daya mata basu mata zafi ba akan kalamanshi. Wai shin ita tace tana sanshi ne? Ko ta taba fada mashi cewar tasan shi Mama zata aura mata ne? Baida tausayi ashe? Duk wannan sanyin ran da sanyin murya na munafurci ne ashe azzalimi ne shima? Abubuwa duk sun hadu sun mata yawa, saida tayi kukanta mai isarta kafin ta shiga kitchen din domin taga wai yama yanayin gidan yake? Gurin ta fara gyarawa kafin ta kwashi kayan ta maidasu kitchen.

Shi kuwa Arhaan ko da ya koma dakinshi briskly ya kara wani wanka, fuskar nan daure kamar tashin bala'i. Ta main door dinshi ya fita bai ko kara waiwayar Sakinah ba. Har yazo zai fita ya tuna da maids din dake gidan, side dinsu ya nufa nan suka gaishe shi kafin ya fada masu abunda ya kawo shi. Sunyi kokarin rokanshi akan ya taimaka masu amma sai ya nuna masu matar gidan ce ta bukaci tafi san tayi aiki da kanta, amma ga kudi nan dan suja jari. Hakan ya kwantar masu da hankali sukaita mashi godiya har ya bace ma idanunsu.

Koda sukaje yima Sakinah sallama bata nuna masu cewar ba hakan bane, abincin breakfast din ta masu umurni da su dauka sukaima yaransu, godiya suka kara yi mata kafin suka fice.

Arhaan yana isa gida ko kallon sisters dinshi dake zolayarshi baiyi ba, direct dakin Mama ya wuce ya kuwa yi sa'a ita kadai ce tana breakfast. Zama yayi saitin kafafunta kafin ya dora kanshi a laps dinta, batayi auni ba taji hawayenshi a jikanta. Cike da murmushi irin na girma ta dago dashi saida ya zamana suna zaune ne akan cushion din su duka, hannayenshi ta rike duka cike da kauna tana me furta "Meya faru kuma, Dan Mama?"

Tabe fuska yayi yana kallonta, shi ko kunyar hawayen nashi bayaji. Wani kukan ya kara fashe mata dashi "Yanzu Mama dan Allah ki rasa wadda zaki aura mani sai Sakinah? Mama yar aiki ce fah. Yanzu ma da safen nan..." shi har cikin ranshi kuka yake yana fada mata abunda Sakinah ta mishi, ita Mama tasan matsalar ta, tunda Sakinah ai da ba haka take ba.

"Arhaan ban sanka da rashin tausayi da jin kan na kasa dakai ba, dan me zaka mata haka? Yanzu ban isa dakai ba kenan Arhaan?" Saurin girgiza mata kai yayi yana me riko hannayenta biyu.

"Wallahi Mama ba haka bane ba, rai na ne ya baci fah. Kuma ni banga abunda zaisa duk cikin matan duniya ki rasa wadda zaki auraman sai ita Mama, to wai ma meyasa aka mata aure yanzu? Kuma dole sai ni?"

"Nasan akwai tambayoyin da suka fi haka yawa a ranta, amma bazan amsa maka ko daya ba sai ranar da kazo da kanka kace man 'Mama inasan Sakinah' ni kuma na maka alkawari zan fada maka dalilin aura maka ita."

Wani zaro ido yayi cike da shagwaba "Mama so kuma? Me zanso jikin waccan yarinyar? Allah ya kyauta nikam."

Dariya ta fashe dashi tana me janyo shi jikinta, "Arhaan kenan, dan Mamanshi. Kar dai azo ayi dana sani fah, kazo nan kana man wani kukan saboda Sakinah. Kuma ka daina ce mata you hate her kaji? Because I know you don't." Fondling daidai saitin heart dinshi take, babu wanda yasan Arhaan a duk duniya fiye da ita.

"Wallahi Mama I hate her, amma saboda Ke I'll stop saying it to her."

Godiya ta mishi daga nan ta cigaba da bashi baki akan yadda zamantakewar aure take da yadda ake hakuri da jin kai ma spouses dinmu. Shidai jinta kawai yake, amma wasu abubuwan bai zama lallai ya aikata su ma Sakinah ba. Amma yadda yaga ta damu tana rokanshi Allah da annabi, he avowed ko yaya ne dole ya tausaya ma Sakinah saboda Mama.

Har yazo zai tafi ta tsayar dashi, dan tare sukayi Azahar sukayi la'asar sai gab da maghrib ya shirya zai tafi. "Na manta na fada maka, Baba ya baka MD a company shi, amma sai next month zaka fara zuwa saboda amarya. Kuma masu aiki tunda ka kora ni ba ruwana Arhaan wadancan dinma dakyar aka samo man su, duk time din da san matarka ya maka shigar illa kai da kanka zakaje ka nemo mata su dan ji zakayi ka tsani kaga tana aikin nan da kanta. Jeka abunka kaji yarona? Don't forget our promise kuma."

Turbune fuska yayi yana niyar amsa mata yaga ta shige toilet ta barshi nan tsaye. Wajen Mummy ya kuma shiga domin ya mata sallama, nan itama ta jashi da fira tana fadin yaushe zai kawo masu surukar tasu. Sisters dinshi nan sukayo chaaa, akan ya fada mata idan sun shirya sunanan zuwa yini, Muhibbah na niyar maganar video din data tura mashi yai maza ya tashi dan baisan amsar dazai bata ba.

Bai shiga gida ba saida yayi maghrib dinshi da isha, sai can wajen 9 har ya kammala shirin shi yayi wanka kafin ya nufi side din Sakinah, for the sake of Mama. Yana zuwa falonta ya isketa zaune kasa hankalinta kwance, tayi pillow da kujera tana kallon wani series din india. Har ya taka yaje inda remote yake batasani ba, saida remote din ya kufce mashi ya fadi ne ta saki wani razanannen ihu tana juyowa sukayi karo dashi.

Hawayen daya gani ne cike da idanunta ya tunzura shi, abunda bai sani bane dama dauriya kawai takeyi cikin gidan nan, tsoro babu inda bai shigeta ba, dan ita tunaninta wani ne ya shigo masu.

Hannayenta duka biyun ya hade waje daya kafin ya rufe bakin ihun da hannu daya "Wallahi kika kuskura kika sauko da hawayen nan sai kinyi regretting."

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now