BABI NA ASHIRIN

1.7K 251 52
                                    

Gam ta runtse idonta, jinta finally ta dira a kasa, dama tasan rikonta da yayi was on reflex, amma da zarar hankalinshi ya dawo dole ya saketa ta fadi kasa, kuma abunda ya faru kenan. Wincing in pain tayi, tama rasa wace azaba zatayi acting upon; azabar ciwon mararta ko kuwa faduwar da tayi? Dagowa tayi da rinannun idanunta tana galla mashi wata irin muguwar harar, long forgetting Aunty Halima's warning.

"Wai kai dan Allah wani irin mara imani ne? Inda kasan bazaka rikeni ba ai basai ka fara ba," ta furta cike da tsiwa tana flashing mashi kallo me cike da rashin kunyar data saba.

"Ke har ni zaki kira da rashin imani? Na rantse da Allah in baki kama kazamin bakinki kinyi shiru ba, sannan kuma kinja dirty body dinki out of this place ba sai na saba miki, idiot," he wasn't yelling, nor was he talking to her in a soft tone-kawai abunda ya fahimta, baida lokacin dazai kara batawa tare da wannan sakaryar yarinyar.

She sat upright and glared at him, "Kai wai nan har zaka iya bude baki ka kira wani kazami? Dallah malam ja gafe kabar masu tsafta suyi magana. Kuma naga dama bani na kawo kaina ba, janyo ni kayi." Har cikin ranta ji take inama ace zata iya lakada wa Arhaan mugun bugun dazai kasa tashi, rainin wayonshi ya fara mata yawa.

Ganin yayo kanta yasa tayi ignoring ciwon tayi hanzarin mikewa, idanuwanta na falling on the floor-taga stains of blood almost duk inda jikinta ya rab'a. Arhaan zaro idanu yayi yana kallonta yana kallon stained floor din, "Ke menene wannan?" He clamoured, tsabar kyama har cikin throat dinshi yakejin wasu kuraje na neman fito mashi.

Kallon kasan tayi kafin ta hadiyi wani yawu me azaba, suppressing vulnerable part dinta tayi kan ta galla mashi wata hararar "Nasan dai kai ba karamin yaro bane, kai ko yaran yanzu ma indai sukaga wannan sunsan menene. Amma considering yadda kake, zan iya yarda idan kace bakasan menene ba. Amma indai haka ta faru, na rantse da Allah dan guntun mutuncinka dake idona har ya zube ya gama. Shagwababbe kawai." Ai bata jira taji me zaice ba kawai tayi hanyar fita.

Muryarshi ta jiyo yana fadin "Ke kizo ki kashe abunnan, dan you won't expect me to eat anything after seeing this trash!" Da alama ma shi maganganun data fada mashi ko registering basuyi a brain dinshi ba, dan ji yake kamar ya rasu wannan abun daya gani.

"Kanka akeji, dama bakin iyayi yasa kaki cin leftover din mutane, kai ala dole ga dan gata!" She yelled back and entered her room-wanka ta fada direct ta gyara jikinta hade da wanke kayan kafin ta fito ta koma kitchen din domin ta gyara wajen, yadda ta fita haka ta samu wajen, saidai ya kashe gas din, amma kuma dankalin yana cikin mai tsamo tsamo.

Wani irin dogon tsaki taja, "Allah wadaran naka ya lalace, sai kace yaga kashi. Yanzu shikenan zai kara rainani wallahi." Daga nan ta cigaba da aikinta tana kunkuni. Dan ita gaba daya alamarin Arhaan ba karamin takaici yake sata ba.

***

Habiba ce zaune saman daya daga cikin kujerun dake zagaye da garden din gidan, hawaye ne ke zarya saman idanunta-ita dai har ga Allah abunda Ramcy take mata bata kaunarshi ko misali, wai haka kawai kullum tana bacci is either taji ana tattabata ko kuma mutum makale da ita. Harma ta gaji da kulle dakin, dan da alama tanada spare key din dakin.

Bata hangoshi ba saida handkerchief din dataji saman hannunta, dagowa tayi da streaming eyes dinta ta sauke su akan nashi, he was intensely staring at her, with his orbs bored into hers. She looked away, for his gaze was too fierce for her fragile heart. She could see something through those plaque orbs of his, something she couldn't decipher.

"Dan gayu," she slurred, tana kai handkerchief din saitin idanuwanta tana gogewa. Ita abun har mamaki yake bata, duk yadda take kuka dayazo take tsintar kanta da dainawa, wanda in da ita kadaice, har sai ta gaji da kokarin daina kukan bacci ya kwasheta. He surely have something different in him.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now