BABI NA TALARIN DA TARA

1.6K 219 28
                                    

Takai kusan minti talatin tana kaiwa da kawowa cikin tsakar dakinsu, babu kowa dakin hakan ya bata damar zubar da hawayenta ba tare da ta takura ma fitowarsu ba. Ita sam bayanin da Alolo yake wa Iya lami bawai ta gama saurarar shi bane, inda ta tsaya shine inda yake fada mata cewar an daura auren. Tasan dukan zuciya bai wuce 80 beats per second, amma tasan for sure tata beats more than 100 per second yanzu.

Tana cikin zarya sai ga Inna ta shigo, fuskarta kamar gonar audugar da ta samu damina mai kyau. Duk wannan masifar ta Inna yau babu ita, sai Sakinah taga ta kara mata wani kyau na ban mamaki. Murmushi Inna ta mata kafin ta janyo ta suka zauna at the edge of the mattress. Magana Inna ta fara mata cikin kwanciyar hankali, wanda hakan did nothing but made her tears intensified.

"Sakinah nasan munyi zaman doya da manja dake amma hakan baya nufin bana sanki kinji? Yanzu duk abunda zaki gani saidai kiyi hakuri, ki taimakeni ki fidda ni kunya, kar inji kar in gani Sakinah. Kiyi hakuri ki zauna dakin mijin ki, nanne rufin asirinki da nawa duka. Dan Allah Sakinah, Allah ya bada saa." Today was the first day da Inna tayi hugging Saking tun lokacin da tayi wayon kanta. Wani mixed emotions Sakinah felt, nan fa kukanta ya kara tsananta, rungume Inna tayi kam, she wants to voice abubuwan dake ranta out; amma it's of no use.

"Inna kiyi hakuri duk abubuwan da nayi maki, dan Allah." Kara rikonta a jikin Inna tayi, tana kuka kamar wacce aka cewa in the next thirty minutes Innar mutuwa zatayi.

"Baki man komai ba, koma kinman na yafe maki Sakinah, nima ki yafe mani. Maza tashi ki daina kukan nan, ki chanza zuwa leshin nan mai red and yellow patterns, nanda ten minutes zasuzo ku tafi sunce akwai walinat da suka hada yau a can Abujar kuma ana bukatar ki."

Bude ido Sakinah tayi ta kara fashewa da wani kuka, slowly Inna tayi breaking hug dinsu ta fita dakin amma Sakinah didn't miss the tears rolling down Inna's cheeks. Sanin halin su Iya Lami yasa Sakinah mikewa dukda tana cikin hawayen taje ta chanza kayan, tana cikin rufe akwatin kuwa saiga su sun shigo. Tanaji tana gani haka aka fitar da ita, ko Baba bata samu ta gani ba balle har su jajanta ma juna akan rashin sanin inda Habibah take.

Cikin mota babu abunda Sakinah takeyi daya wuce kuka, ita bawai auren bane, ko kuma rashin wanda ta aura da batayi ba, babban bakin cikinta bai wuce irin wulakantar tar rayuwar da zatayi a gidan auren ba, dan ta tabbatar daga ranar da yasan cewar she isn't a virgin to kashinta ya bushe. Allah ya isa kuwa cikin kwando tayi ma samarin nan ita.

A haka suka isa cikin garin abuja, dukda cewar ta daina kuka, amma idanunta sun rine tamkar wacce akayi ma dukan tsiya. Hanyar gidan Mama akayi dasu, dan kuwa acan ne za'ayi walimar, Sakinah dai bude baki tayi tana kallon ikon Allah, dama tasan for sure Mama zata hada masu walimar dan haka bata kawo komai a ranta ba.

Koda suka isa gidan saida su Iya Lami suka surfa mata zagi iya san ransu kafin ma ta yarda ta sauko daga motar, side din Mommy abokiyar zaman Mama aka nufa da ita, can wani daki inda take da tabbacin dakin daya daga cikin yaranta mata ne. Kamar wasa sai ga wasu yan mata su biyu sun shigo sunsha ado iya ado, gaisawa sukayi kafin mai fara'ar sosai ta ajiye tray din abinci gefenta.

"Sister, gashi nan Mama tace na kawo maki kuma tace in tabbatar kinci inva haka ba zatazo da kanta. Kiyi sauri ki gama dan by 4pm walimar zata fara kuma tace Muhibbah zata maki makeup." Fara'a gareta sosai, haka kawai Sakinah taji ta birgeta, bata mata gardama ba dan bawai magana takesan yi ba. Kadan ta tsakura cikin abinci kafin Muhibbah tace zata fara kwalliyar.

Sun fada mata sunansu, me fara'ar itace Safiyya amma suna kiranta da Tatiyya itace take bima Muhibbah , dukansu yaran Mommy ne. "Safiyya jeki wajen Aunty Halima kice ta bada kayan nata saboda daurin dankwali."

Cike da fara'a Aisha ta fita sai gata ta dawo da wani bridal gown cikin hanger sai head din wacce Muhibbah zata daura mata. Dan fita sukayi suka bata waje ta saka gown din wacce ta kasancewa peach ce and it perfectly matched Sakinah's skin color. Bayan mintuna kadan suka shigo and they were in awe of her beauty. She was curvy beyond how they imagined, gown din yayi fitting dinta bacin akwai flowing veil da sunsan Mama zatace bazata saka ba dan ya kama curves dinta.

Zama tayi Muhibbah ta daura mata head dinnan, when she saw herself in the mirror dan dole Sakinah ta saki wani murmushi, she never know she could be this beautiful. Safiyya ta dauko veil din ta fara dora mata saman shoulders dinta, nan ne Muhibbah ta samu damar yi mata video daga kasa sai datazo daidai face dinta nan kuma Safiyya ta zagayo dan ta daura mata shi saman head din daga dan baya yadda bazai baci ba.

"Safiyya nidai na tafi, Sister kinyi kyau, Allah ya kawo kazantar daki." Slightly Muhibbah tayi hugging Sakinah kafin ta fita daga gidan gaba daya, dayake a farfajiyar gidan za'ayi walimar duk gidan ya cika babu wanda ya lura da ta fia balle a kira dan a sakata aiki.

Tana cikin driving sai ta tsaya dan siyan drink, a nanne ta kara playing video din Sakinah da yar dariyar ta ta tura ma Arhaan video din with the said message. 'Brother wallahi kayi sa'ar mata, she's beautiful and curvy as well. Allah ya kawo ranar da zan mata makeup din suna." Tana turawa ta kashe data dinta, tasan zagin ta zaiyi.

Sakinah was welcomed yadda batayi tunani ba, Mama da Aunty Halima kuwa kamar su mayar da ita cikinsu, haka akayi walimar duk inda tayi Safiyya nanan tare da ita wanda hakan ba karamin dadi ya mata ba. Sai can wajen 8pm aka tafi kai amarya masaukinta, ganin yanayin gidan yasaka dole gaban Sakinah ya yanke ya fadi, amma sai wata zuciyar tace mata 'Kila dan wani yar uwa ko dan uwan Mamar ne ta aura.'

Tare da ita wasu daga cikin dangin mijin da kuma danginfa suka kwana, amma Safiyya na tare da ita kan gado anan suka kwana. Washe gari da safe kowa ya karya, Safiyya ita taje gidan Mama ta dauko mata kayan da zata saka dan ba'a taho da akwatunan gidansu ba. Simple makeup Muhibbah ta mata nan sai bayan azahar su Iya Lami suka tafi, ai kuwa tasha kuka kamar ranta ya fita, duk yadda bata wani saka su a ranta ba, amma taji ba dadi.

Da yamma lis sai ga Mama da tawagar friends dinta sunzo ganin amaryar dan auta kuma dan mama. Tare da akwatunan Sakinar aka tafi kuma suka aje mata a dakinta. Dinner din da aka kawo mata saida Safiyya ta tabbatar komai is set kafin driver ya maida ta gida can wajen 9pm after su Mama sun dade da tafiya.

Arhaan har Safiyya ta dawo gida bai zo yama Mama sallama ba because bai taba kwanciya ba baizo yama Mama sallama ba. Can wajen 9:30pm sai ga Arhaan ya shigo dakin fuska a turbune kamar zaiyi kuka, ganin haka yasa yan dakin wanda suka kasance kanne a gareta suka fita suka basu waje. Shawarwari ta fara bashi da ban baki da kuma jaddada mashi hakkokin dasuka rataya a kan wuyanshi. Ba abunda yafi bawa Mama dariya saida lokacin datace dole fa yau yaje yaga yadda take kuma wacece, maganar da ya furta was.

"Ni Mama ko naje bansan me zance mata ba." Dariya tayi har ranta kafin tasa ya dauko memo da biro ta fara mashi listing irin questions din dazai tambayar matar for them to know each other. Sai can wajen 10pm ne ta koreshi ya tafi bawai dan ranshi yaso ba.

Part dinshi ya fara shiga a gidan, wanda there was a door linking to the other part idan ka shigo zaka riski falonshi wanda kofar shima tana falon Sakinah. Daki ya shiga yai zaune ya rasa yadda zaiyi, gashi shi ba friends ba, cousins dinshi that offered to help duk ya kashe phones dinshi dan karsu dameshi.

Wayarshi ya ciro ya fara replying congratulatory messages da baisan yadda akayi mutanen suka san yayi aure ba. Can yaga message din Muhibbah na jiya, yana shiga video din automatically downloaded itself, kallo ya tsaya yanayi, suddenly the urge to see her face jolted him, fita dakin yayi amma bai manta da paper din da Mama ta rubuta mashi ba.

Dakyar yayi turning door knob din dakin, yana shiga ya hango ta zaune saman gadon tana karatun kur'ani, kanta a kasa. Sallama yayi amma bata tanka shi ba saida yazo har tsakiyar dakin, feets away from where she was sitting, a lokacin ita kuma ta kammala ayar da take ta kulle Kur'anin.

"Wa'alaikumus Salam," dukda zuciyarta na bugawa, amma hakan bai hana mata dagowa dan taga wai shin waye wannan angon nata?

Tare suka kalli juna, a daidai time din kuma idanunsu ya hadu dana juna, Sakinah batasan lokacin data ida mikewa ba gaba daya shima Arhaan ya tako zuwa gadon dan tabbatar ma kanshi abunda ya gani. Kawunansu ne suka bugu da juna, kowa yaja baya yana kallon dan uwanshi cike da tuhuma.

"What the hell! Me kikeyi a nan?!"


It's time for the real game!

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now