BABI NA TALATIN DA DAYA

1.6K 211 14
                                    

"Hasbinallahu la ilaha illa huwa, me nake gani haka? La haula fi shi'atil lahi! Sakinah?!" Inna ce ke rafka wannan salatin yadda kasan ance mata yau ga gawar Sakinah kwance a tsakar gidan. Kwata kwata ta manta da cewa fada take haikan da Maman Iliya, dan kuwa takowa take har gaban Sakinah yadda kasan taga zombie.

Sakinah wani irin mugun numfashi taja, ita kam shikenan yau taga rayuwa, tasan Inna ko sama da kasa zasu hade bazata taba yarda cewar batayi komai ba, cewa zatayi can rashin kunya tayi masu suka korota. "Ke dan ubanki kiman magana ina tambayarki abu amma sai raba ido kike kamar shege a rabon gado!" Inna ce ta furta da karfi tana ida janyo Sakinah gaba daya cikin gidan, ita kam yau taga rayuwa.

"Inna ki tsaya kiji mana, sai jana kike kamar ance maki nayi sata!" Sakinah na fadin haka tayi shrugging off hannun Inna dake damke da hijabinta kafin ta karasa wajen dakunansu. Juyawa tayi taga Maman iliya ta kureta da idanuwa, harara ta galla mata dan kuwa har yanzu haushinta yana nan fal ranta, kuma da zata samu chance sai ta rama.

"Sakinah wai baki fada man meya faru? Ya za'ayi inga kun shigo gida keda wancan gantalallen, ya ajiye ghana must go dinki ya juya ya fita sannan kuma kiyi man shiru? Wallahi ko kiyi magana ko inci ubanki! Halan wani iskancin kikaje kika masu suka koroki ko? Shegiya me bakin halin tsiya!" Nufar inda Sakinah tayi kamar wata zakanya sai huci take ta rasa inda zata saka kanta.

"Inna kina gani dai akwai minahikai cikin gidan nan, sai mu shiga daki ko? Naga an kuremu da ido yadda kasan mujiya!" Sakinah ce ta bada amsa tana jifan Maman iliya da wani irin mugun kallo, dukda tsoron Inna da takeji cikin ranta, hakan bai hanata masifa ba.

"Ah kwantar da hankalinki yarinya, indai wannan masifaffiyar uwar takice nan tsakar gida zamu tsinci maganar tas! Wama ya sani ko matar miji taga ana neman kwace mata, ko dan hali akayo shine aka gudo gida!" Tafa hannuwa take tana surfa bayani, dan kuwa maman iliya bata taba ji tayi shiru, ba'ayi da itaba ta tanka balle.

"Ke Maman iliya ki kama kanki na rantse da Allah, yo inma mijin ne ai na arziki ne ba kamar naki ba yadda kasan an mikar da jaki tsaye. Sai kija baki kima mutane shiru ai ko?" Sakinah ce ta maida martani, dan kuwa ta dade tanada cikin Maman Iliya, fatanta daya Allah yasa yau Inna bazata tsaidata ba kamar ranar nan.

"Iyyeh! Amma wallahi yarinya kinyi magana, dan ubanki mijin nawa ne kamar an tada jaki tsaye? Aikau yau ba abunda zai hana inci ubanki cikin gidan nan, shegiya wama ya sani ko bleaching kika fara daga zuwanki gidan mutane. Kaida aka tura aikatau ko koma neman maza!" Har wata kunfa kumfa ke fitowa daga bakin Maman Iliya, dan kuwa zagin ba karamin ciwo yayi mata ba. Ita dama har wata rahama taji lokacin da Sakinah ta tafi aikatau dinnan, amma yanzu ta dawo ta tabbata zaman lafiyarta ya kare cikin gidan nan.

"Inma bleaching din nayi ai bada kudinki bane, ke ko mazan na nema fah na isa in nema-komin banza dai ni ba tsaye nike ba kamar pencil, duk inda mace zata shiga zanje, kuma banda nononuwa kamar slippers din tsohuwa." Ita har ga Allah Sakinah ta manta da zaman Inna dake gefenta tana ta jifanta da harara alamar ta daina, dukda alamun Innar ya nuna tanajin dadin abunda Sakinar keyi, dan itama bawai sun gama fadansu da Maman Iliya din bane.

Fas! Kakejin Maman Iliya ta kwashe Sakinah ta mari, aikau in the blink of an eye Sakinah ta zabga mata marin itama, nan da nan suka kicime suna fada. Duk wani bacin cikin da Sakinah ta kwasa tsawan wata hudu saida ta juyeshi tas akan Maman Iliya, da wanda ta mata da wanda bata mata ba. She's tired.

Dakyar Inna ta banbaro Sakinah daga jikin Maman Iliya kafin ta turata dakinsu. Fitowa tayi ta tsaya kan Maman Iliya wacce keta faman sauke numfashi ko mikewa ta kasa yi tsabar buguwar da tayi. Wata irin shewa Inna ta kwashe da ita, "To ai sai a kwashi jiki aje ayita gashi ko? Dan nasan wannan irin dukan kawo wuka sai an hada da ruwan zafi. In halinki ne gobe ma kin kara, ni nagode ma Allah dayasa Sakinah kika ma wannan iskancin ba Habibah ba, tunda gashi ta maki tas ta nakada maki na jaki kuma."

Daga haka Inna ta kara kwashewa da dariya kafin ta shige dakin da Sakinah take zaune tayi tsuru. Daure fuska tayi tamau kamar ba ita bace take dariya minutes ago. "Dan ubanki zaki gaya man abunda ya barako da wajen aikinki kafin inci maki uwa ko kuwa?" Wata irin cakuma Inna tayi ma Sakinah saida ta saki yar kara. Hijabin Inna ta fincike ta yada saman katifa tana kureta da idanu.

"Inna dan girman Allah ki tsaya kiji. Wallahi wai kawai dan na manta ban share bayan gidan ba shine fa mijin ya fara dukana-sai akayi sa'a Ya T ya yaje zai masu gyaran famfo shine fa ya kwatoni hannunsu muka taho gida!" Ganin Inna zata iya mata lahani yasa ta fara magana jikinta har rawa yake, dan kuwa duk iskanci Sakinah tanajin tsoron Inna musanman ma lokacin dataji ta shiga hannunta.

"Dan ubanki yaushe Tukur ya fara gyaran famfo? Sakinah ko ki gaya man gaskiar abunda kuka aikata keda munafukin dan uwanki wallahi ko in balla ki cikin gidan nan." Hannu ta fara kaima Sakinah tana jibgarta, tun Sakinah na kokarin kaucewa taga dai da gaske Inna lahani take niyar yi mata.

"Inna bari kiji dan Allah; wallahi kullum mijin sai ya zageni ya wulakanta ni saboda fitsarin kwance. Dakin da suka bani in rika kwana cikin falon gidansu yake, to zaurin yana fito masu falo-shine yau ya zageni ya jefo mani kudi yace gobe in dawo gida!" Kuka Sakinah take sosai, dan kuwa Inna babu inda bata jibga a jikinta.

"To ta gidan ubanwa yau ta zama gobe?" Inna ta dan sassauta dukan amma wani irin huci take kamar yunwataccen zaki.

"Inna bayan na kira Ya T a waya nace yazo, to shine mijin ya ganmu tare da Ya T yayi hugging dina yana ban hakuri, shine yace wai ni yar iska ce zan bata mashi tarbiyar yara in fita in bar mashi. Sai na kara kiran Ya T dinfa muka taho gida."

"Hugging Sakinah? Dan ubanki tabe taben naku har yakai kuyi gaban mutane? Aikau yau zakiga hugging! Na rantse da Allah na kabari sai ya fiki jin dadi dan ubanki, gara ma tun wuri kisan nayi cikin gidan nan."

"Na shiga uku, Inna ki rufa man asiri."

Dare ne sosai, dare ya tsala ko ina shiru babu abunda yake tashi. Bacci take cikin kwanciyar hankali, amma yadda kasan zuciyarta tana kan hannu; domin irin baccin nan ne wanda rabi kana bacci rabi idanunka bude. Cikin baccin taji kamar an bude kofar dakinta, shiru tayi domin jin in da gaske ne zataji taku; amma Habibah bataji komai ba.

Maama ce rike da kaskon turaren wuta, amma hayakin dayake fitowa daga garwashin nan baiyi kama dana turaren wuta ba. Kayane jikinta kamar na jiya, haka take tafiyar maciji kamar bata taka kasa, tana zuwa daidai kan gadon ta bude ledar maganin da aka bata ta barbada ma Habibah kafin tabi turaren tana kanga mata hayakin saman jikinta.

Firgigit Habibah ta mike, amma suna hada ido taji duk wata fargaba ko tsana ko wani sanin ya kamata ya gushe daga zuciyarta. Murmushi tama Maama fully kafin ta mike zaune daga kan gadon, "Maama lafiya?" Babu alamun tsoro ko fargaba a zuciyarta, dan haka nan ta tsinci kanta da admiring kayan da Maama din take sanye dasu cikin daren.

Murmushi Maama tayi ganin irin kallon da Habibah take bin ilahirin jikinta dashi, ajiye kaskon turaren wutar saman bed side drawer kafin ta zauna kan gadon dab da Habibah. "Beeba gidan naji yana man wani iri shine fa na tashi nake saka turaren wuta ko ina. Kai kayanki sun mani kyau, halan wanda Saheer ya siyo shekaran jiya ne?" Hannu takai saman chest din Habibah tana tabawa cikin wani irin salo wanda da da ne tabbas Habibah sai ta mike amma yanzu sai ma melting tayi under Maama's touch.

Abu kamar wasa ya koma ya zama intense abu, wanda a halin yanzu Maama na bada almost 80% na alfashar amma itama Habibah ta tsinci kanta da contributing with almost 20%. Wani irin gayataccen murmushi Maama ta sauke dan ganin hakarta ta cimma ruwa, a haka ta riko hannun Habibah ta mata jagoranci zuwa hanyar bata da la'ana.

Sakinah kwance take saman katifarsu babu abunda take banda kuka, inba karar motsawar agogo ba babu abunda yake motsi cikin daren. Tayi mugun buguwa wajen Inna, dan dakyar Baba ya kwaceta hannun Inna. Amma abun mamakin shine, dukda tanajin ciwo a ilahirin jikinta, zuciyarta tafi mata komai ciwo. Haka nan takejin kamar ma zuciyar na mata kumburi, ciwo sosai kamar akwai abunda zuciyarta take begen gani ko ji amma babu.

Kukan ne yakesan cin karfin, toshe bakinta tayi da hannu tana furta "Ya Allah kaddarar daka dora mani kenan? Ko da ban sani ba nasan wannan ciwon zuciya ne ya kamani. Allah ka yaye man."

Thank you.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now