BABI NA SHA BIYU

1.6K 201 34
                                    

Kamar daga sama haka taji muryarshi, saurin dagowa tayi tana kallonshi kafin ta tuno abunda ya faru shekaran jiya. Gulping back tears dinta tayi tana share hawayenta, but the tears were so stubborn to abide.

"Can I have a seat?" Ya tambaya, dan ganin yadda ma ta rude ta kasa ma tsaida hawayen balle ta amsa mashi tambayar shi ta farko.

Koda ya zauna Habiba kallonshi kawai tayi ta kauda kai, dan ita kanta batasan what she's feeling in her heart ba, all she knew is she doesn't need any feeling of empathy towards her; she has lost that from the incipient.

Koda ya zauna shi ya rasa abunda yake mashi yawo cikin kai, he is supposed to be angry at her for spilling a drink on him, but here he is; feeling as if a droplet of fire being dripped on his heart with every tear she shed.

"Bazaki man magana ba? Ko tsoro na kikeji?" Shi kanshi mamakin kanshi yake, all he knew is he hates seeing a girl crying, dan kuwa bayasan ma tunanin abunda zai sakata kuka. Babban abunda ya tsana bai wuci ganin mace na kuma ba, dan yasha ganin macen da yafi so a rayuwarshi na kuka; kuma it wasn't a feeling to remember.

A hankali ta juyo tana kallonshi, tana goge hawayen amma stubborn ones din were still streaming in oceans. "Ni bana tsoronka, amma aren't you still angry at me? My feet still hurts uno?" Ta tambaya tana dago kafarta mai ciwo tana dan jujjuyawa, she could welcome hundreds of this pain than what she's feeling in her heart.

Ganin yadda take juyo kafarta tana kallo ga wasu hawayen na zuba a idanunta yasa yaji tausayinta ya kamashi, "Ni bana fushi dake, kece ya kamata kiyi fushi dani; nine silar ji maki ciwo ko? Was that the reason you were crying?" Ya tambaya a hankali, dreading to hear her answer, dan he would be angry at himself if shine silar sakata wannan kukan mai taba zuciya- dan the last abu da yakesan yi a rayuwarshi shine ya saka mace kuka.

Saurin girgiza kai tayi with a fleeting smile on her lips, "Aa fah, wannan ai is a minor pain, I could welcome thousands of it than what I'm feeling in my heart. Kasan irin feeling dinnan, wanda abu yana damunka amma bazaka iya cewa menene ba? But you surely knows that something is definitely wrong with you?" ta fada tana langabar da kai, wasu hawayen na kara zarya saman kuncinta.

Ji yayi kamar ya tayata kukan, he could relate to this feeling more than anyone in this world. Haka kawai yaji zuciyarshi na karyewa, dan yasan irin abun nan babu abunda ya kaisa paining. "I tagged that as the worst feeling one could ever feel. Had it been kasan abunda ke damunka da sauki, I can relate to your pain. But you know what? Idan kikayi voicing out abun zakiji dadi sosai ba kadan ba; I was once a victim," ya fada in a soothing way, yana kallonta-kallo me cike da tausayi da wani feeling da shi kanshi bai sani ba. Sai yanzu yake lura da yanayin skin colour dinta, ga sanyi halinta wanda kallon farko ma zaka iya ganewa.

Leaning back on the chair tayi da dan murmushi wanda yake sabo a gareta, "Sunana Habiba, but you can call me Beeba," haka kawai ta samu kanta da furta sunan da Ramcy ta rada mata.

"Toh Beeba, sunana Saheer. Nasan fadin abunda ke cikin ranki zai maki wahala, why not ki kira gida ki fada masu?" Yayi offering again, dan yasan not everyone like confiding in strangers-he is a testifier on that.

Kalmar gida ta tado mata da wata irin maguwar faduwar gaba, dan ita har ga Allah tasan tabbas dole tanada iyaye, amma dan yanzu ace ta fadi koda sunansu ne bata iyawa balle har tace ga inda suke zaune. Lalube ta farayi cikin kwakwalwarta, amma iyakar tunaninta babu wanda zata iya pointing tace gashi shi dan-uwanta ne; kawai dai tasan ita yar aikin Hajia ce.

Wani kuka ne kawai ya kwace mata, fadin tashin hankalin data shiga bama zai iya faduwa ba. Wani irin zugi zuciyarta ke mata, ga wani tashin hankali da ciwan kai daya ziyarci kwakwalwarta. Girgiza kai ta shiga yi, hawaye wani nabin wani. "Wallahi bansan su ba, bansan kowa nawa ba, Hajia kawai na sani-sannan kuma nasan ni yar aiki ce."

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now