BABI NA HAMSIN

1.6K 236 39
                                    

Dedicated to Aysha Aliyu Batsari (Sholeey) Happy birthday dear🥳❤️ Sakinah and Arhaan loves you and wish you a happy birthday with lots of laughter and love.

"Lallai ma yarinyar nan duniya kika samu shine baki nemana ko? To gani nazo yanzu ai." Ya T ne yayi magana hade da dan dukan kanta kafin yayi breaking hug dinsu, janyo hannunta yayi ba tare da ya lura da yadda jikinta yayi sanyi ba, zama sukayi kan kujera yana kallonta "Ke wai dallah gidan naki ba abinci ne? Alquran yau banci komai ba." Yadda yayi maganar cike da dabanci yayi ta, Sakinah yaken dole tayi ta mike tsaye. Har yanzu idanun Arhaan yana kansu, shi bai koma ciki ba shi kuma bai karaso ba.

"Kai Ya T? Kana da kudi fah shine zaka wani ce bakaci komai ba? Nidai yi hakuri bari in zubo maka." Tsoronta daya kar sai taje kitchen din Arhaan ya shigo falon, tasan ko kule yace ma Ya T dan dole zai ce mashi cas cass cassss, kuma tana tsoron yasa a kamashi.

Kamar wacce kwai ya fashe mawa haka ta fara takawa ta shiga kitchen din, "Ke sakara ga tv amma bakya kallo? Lallai yarinyar nan sai na fada ma Inna irin dolancin da kikeyi, ko ina wannan sakarar da ko magana bata san yi? Dama itama auren taje tayi na hutu na fargabar halin da kuke ciki ku duka." Bai kula da mutum yana kallonshi ba, haka yaje ya kunno tv ya dawo dauke da remote domin chanza channels.

Cikin gaugawa Sakinah ta zubo mashi abincin ta dauko drink din ta kawo mashi, jikinta babu inda baya rawa, tsoron Arhaan ne yayi mata wani irin mugun comeback a ran ta. Ganin Ya T ya kunna tv saida taji kamar ta saki fitsari a wajen, kasa kallon inda Arhaan yake tsaye tayi, Ya T ta aje ma abinci kafin ta raba ta zauna gefenshi.

Fira suka fara sama sama yanacin abincin shi, tambayarshi su Maman Iliya tayi, saida yayi wata irin muguwar dariya kafin ya bata amsa. "Ai ki barni da shegiyar matar nan, wai dan uwarta ni zan koma gidan nan inji tana fada ma Inna magana? Ina mata magana akan tayi shiru kuma ta nemi ta zageni wai nine katon banza tsabar banda amfani an aurar dake bana nan ita kuma waccan sokuwar an kasa getting to her. Aikuwa na lakada mata na jaki, muna zaune a majalisar mu sai ga mijinta yana huci yazo wai zai rama mata, nasa su Gatari da Zarto ranar Kusa yana wajen; suka kusa wulla shi lahira. Yanzu shegiyar tana can asibiti jinya suke." Hankalinshi kwance yake bata labari sai dariya yakeyi, murmushin yake kawai take mashi dan tasan yanzu kam Arhaan yagama cika ya batse.

Sama sama ake hirar, ya lura Sakinah bawai san magana take ba kuma yasan ba haka take ba, "Ke wai lafiyar ki kuwa? Naga tun dazu sai juyawa kike kina kallon wajen labulen can. Wai waye mijin ma dan uwarshi bazaizo ya gaida ni bane? Ko wani abun yake maki? Akwai mai takura maki ne inyi maganin ko wane shege? Ina wannan dan iskan yaron da yayi maki iskanci a gidan aikin ki?" Hannu kawai Sakinah ta dora saman kai ganin Arhaan tsaye gabansh eyes dinshi sunyi jaa tsabar bacin ran dayake ciki, kallonta yayi ido cikin ido kafin ya maida hankalinshi akan Ya T.

"Gani, kuma nine mijinta da kake nema." Bata taba tunanin zataga irin wannan confidence and courage din a fuskar Arhaan ba, tayi tunanin the next time da zasu kara haduwa da Ya T kila sai ya kusa fitsari a wando tsabar tsoro amma she saw nothing in his eyes banda rage, he was angry and thirsty for revenge.

Daga zaunen da yake T ya mike tsaye, wani irin ashar ya saki kafin ya maida kallonshi kan Sakinah "Ke dan ubanki da gaske wannan huhu lahun yake? Ta gidan uwar wa kika fara sanshi?!" Jijiyoyin nan sun taso sunyi rudu rudu, yadda yake kallonta tasan inhar bata bashi amsa ta samu sun rabu lafiya ba toh babu wanda zai hanashi ya mata jan bugu kuma ya zane Arhaan din shima.

"Wallahi ban sanshi Ya T!" Tana furta hakan wasu hawaye suka sauko mata, tasan idan tace tana sanshi wani tashin hankalin ne, a hakan ma bawai ta tsira bane ba.

"To kai bata sanka ta gidan uwar wa ka auro ta? Inna dole ta maki ko? Wannan tsohuwar na rantse da mai busan numfashi sai ta gane kurenta!" Ganin ya chakumi collar din Arhaan yasa Sakinah riko hannayenshi gam, kuka take shara shara tana girgiza ma Ya T kai.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now