BABI NA SITTIN DA TAKWAS

1.5K 211 28
                                    

Sati daya har ya wuce, in kaga Sakina da Habiba bazaka taba cewa sun dauki tsawon watanni batare da sanin inda junansu suke ba. Tun kusan last two days Habiba take damun Sakina akan ita tanaso taje gida wajen Inna da Baba, saboda zuwa yanzu Arhaan ya fada masu cewar rehabilitation camp yasa aka kai Ya T, inda ake saka ran Insha Allahu idan ya fito duk wani shaye shaye zai daina zai natsu ya kama sana'ar yi.

Sakina tanaso taje gidan amma tsoron irin tarbar da Inna zata mata yasa ta kasa zuwa, dan haka Arhaan ya saka driver dinshi yaja motar Habiba ya kaita har Kaduna kafin ya hau mota ya dawo gida. Koda Habiba ta tsaya bakin kofar gidansu tafi five minutes batare da ta kara taku koda daya ba. With a heavy heart, a hankali ta fara taku daya daya har ta shiga gidan.

As usual, muryar Inna ta jiyo tana sheka masifa cikin gidan, wai ta shanya dussa awakin Maman iliya sun cinye mata. She put it in mind, zata siyawa iyayenta gida, atleast they owe her that. Daga muryarta tayi ta kara kwada wata sallamar, kamar daga sama Inna ta jiyo sauti kamar na Habiba. Juyowa tayi kafin ta tsaya shekeke tana kallonta.

"Innalillahi! Habiba kece nake gani haka?! Allah mai yadda yaso, Habiba ina kika shiga tsawon lokacin nan ko waya bakiyi?" Tunda Inna take sai yau ta bari damuwar rashin sanin inda Habiba take ta fito fili, dan koda Maman iliya ke cewa sunje sun saida yarinya bata taba bari abun ya dameta ba.

A hankali Habiba ta tako har inda Inna take kafin tayi hugging dinta sai kuka. Baba yana jinsu cikin daki, dan yau bayajin dadin jikinshi ko kasuwar baije ba, koma yahe baida karfin da zaiyi wani dako. Jin shashekar kukan Habiba tanawa Inna magana yasa a takarkara ya fito daga dakin, ilai kau ita yagani tsaye, hannunta cikin na Inna suna magana.

"Beebalo?" Her calls her that sometimes, wani sa'ilin har Sakina ta rika mata dariya wai ita dai duk yanda akayi da sunanta bai taba yin dadi. A hankali ta saki hannun Inna kafin ta karasa wajen Baba, she missed him.

Saida komai ya lafa kafin take fada masu ai ga inda aka kai Ya T su daina damun kansu abun alkhairi ne insha Allahu. Ta fada masu cewar daga gidan Sakina take kuma tanaso zasuje wani waje da ita. Kafin yamma tayi ta samo number din dillalin gidaje, nan sukayi magana akan gobe zataje taga gidan ta siya.

Washe gari da safe haka ta daukesu cikin mota suka nufa inda dillalin ya turo mata address, cikinsu babu wanda ya tambayi inda ta samo mota ko kuma kudin da suka lura tanada shi, saidai ta lura Baba yana san yayi magana amma yana tsoron masifar Inna, dan abu kadan daya fada zatace nema yake ya takurawa yarinya.

Gidan sukaje suka gani, gida ne flat me kyau daki uku sai falo daya da kitchen, kowane daki kuma da toilet dinshi, tsakar gidan kuma ba laifi tana da dan girma. Juyawa tayi ta kallesu tace gidan yayi? A tare suka daga mata kai, da murmushi tabi dillalin kafin taje ta mishi transfer, akayi signing aka bata takardun gida. Motar suka koma kafin ta dauki hanyar rehabilitation center dinnan, dama Arhaan ya bata address din wajen.

Waje ne mai kyau inda sai dan wane da wane ake kaiwa, ba kananun kudi ake kashewa duk wanda aka kai wajen ba, dan kuwa har karatun boko dana addini ake koya masu a wajen. Shiga sukayi suka cika bayani kafin aka kaisu wani waje suka jira bada dadewa ba saiga Ya T an fito dashi, hankalinshi kwance babu alamar wahala a tattare dashi, sai ma wani hankali daya fara yi.

Har kasa ya duka ya gida Baba da Inna kafin Habiba ta danyi hugging dinshi, she missed him. Dan dukan kanta yayi cikin wasa, "Ke kuma wannan yarinyar mara magana yaushe kika dawo?" Dukansu sukayi dariya.

Hira suka taba ba laifi har sunzo zaus tafi yace "Ina wannan rigimarmiyar? Ita bata zuwa ta duba ni ko? Ko dan mijinta ya kawo ni nan? Kice ina missing dinta." Dariya suka karayi kafin Habiba ta tabbatar mashi da ttabbaszata isar da sakonshi wajen Sakina.

Gida ta maidasu kafin ta kallesu tace, "To Inna ku kwaso kayanku, amma dan Allah wanda kadai zamuyi amfani dasu, komai da ake bukata zan siya." Hakan kuwa akayi, kayan sakawa kadai suka dauka suma banda tsummomi. Dillalin daya samar mata gida shi ya samo mata interior designers sukaje suka cika gidan da furnitures, kayan kitchen da kuma sauran kayan kwalliyar gida. Ita kanta batasan kudin dake account dinta ba, all she knows is karamar kyautar kudin da ake mata itace ta five mil, dan akwai wata minister data taba bata 20 mil nan take. Kuma bayan wadda ta daukota duk wacce tayi wani abu da ita sai tayi mata kyautar kudi, it's dirty, she knows.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now