BABI NA ASHIRIN DA BIYU

1.4K 235 39
                                    

Arhaan ne yake tuki cike da nishadi da walwala, dan tun lokacin da Aunty Halima ta kawo wannan yar rainin wayon yarinyar rabonshi da farin ciki irin wannan har ya manta, but seeing her tears and the painful looks on her face made his worries vanished-it was really worth it.

Har zaisha roundabout din dazai sadashi da unguwarsu sai ya hango wani wajen saida shawarma ga ice cream parlour daga gefe, murmusawa yayi kafin ya karya steering wheel din motar ya nufi wajen, it has been a long tiring day since morning, and su Kamal deserve something good as his token.

Shawarma manya na chicken aka bashi guda goma da manyan jars na ice cream suma goda-yasan sun masu yawa, amma dole ya kashe kudinshi ko dan farin cikin dayake ciki. Passenger's seat ya zuba ledojin kafin yayi hitting on his wheel, driving while rhyming the song of Austin mahoni.

A farkon layinsu, wanda kafin ka isa gidansu it will take you two minutes in kana gudu, dan gidan nasu shine last in the other end-hango wasu kamar yan daba yayi zaune a saman titi ga adda da wasu iccina a gefensu, ko tsoron ma wani yazo ya buge su basayi.

Dan tsaki yayi, ganin yadda ko tausaya ma kansu basayi, dan nan idan wani yabi ta kansu ai sunja ma kansu zaman jinya-nikau a raina nace jinyar takace malam Arhaan. Manoeuvering yayi niyyar yi ta gefensu ya wuce amma abun mamaki sai yaga sunma mike suna neman zagaye motarshi-dole yaja burki ya tsaya, dan cikinshi ba karamar durar ruwa yayi ba, gashi layinsu sai a kasheka wani bai fito daga gidanshi ba.

Wanda ya lura da kamar yafi sauran fushi ya ga ya nufoshi, babu arziki yayi winding down glass din motar zuciyarshi na dukan uku uku. "Malam lafiya naga kun tare man hanya?" Ya tambaya yana neman daura fuska kar suga tsoronshi dake neman daukar ranshi tun kafin su mishi wani abu.

Ai baiji amsa ba sai wani irin azabataccen mari da aka sauke saman kuncinshi da yaji kamar an zuba mashi narkakkar dalma saman fuska. Bude kofar T yayi kawai ya ingizo shi waje bai jira komai ba ya cigaba da lakada mashi na jakki, tun Arhaan na niyar kwacewa har yaga ba sarki sai Allah ya fara ihu, dan ta ko ina suke jibgarshi babu zallar imani a kwayar idanunsu.

"Wai me na maku ne? Nifa ko taba ganinku banyi ba!" He exclaimed cikeda azaba yana daddaga hannu yana kare fuskarshi gudun kar suyima yar kwakkyawar fuskarshi illa.

Har T ya bude baki zai fadi sunan Sakinah sai kuma ya fasa, dan yaga text din data turo mashi dazu akan karya nuna hada ita, inba haka ba yan sanda zaasa su kamata. "Dan uwarka tambaya ma kake ko? Yau zakaci ubanka kuwa na rantse da Allah. Kai kafin ma na aikaka barzahu sai na lakada maka dukan da akewa jakkai irinka!" T roared yana kara shurinshi, Arhaan banda ihu babu abunda yake, yau hawayen daya saba wasa da hankalin danginsa dashi ma sunki zuwa balle yaji sa'ida.

Ganin har yana fitar da numfashi dakyar yasa suka dan tsagaita bawai dan zasu gyaleshi haka nan ba, "Gatari, duba man miye cikin ledojin can!" T ya fadawa daya daga cikin wanda suke tare. Dauko ledojin yayi ya buda yaga uwar shawarma ce da ice cream, irin dariyar nan ta yan daba yayi, which sent a quiver down Arhaan's spine.

"Wallahi in fada maka wannan abunce wanda mukasa wadannan mutanen cinta kafin suka wulla lahira, sai kuma as kirim," ledojin ya ajiye gabansu yana dariyar mugunta, dan kuwa shi kadai yasan yadda suke ma duk wanda suka samu da abinci.

"Kai, tashi dan uwarka sai ka cinye wannan abincin tas kafin na yankar maka ticket din lahira!" T ya furta cikin muryar da babu digon imani a cikinta, yana ingizo Arhaan wanda yakejin duk wata mahada ta jikinshi to sun balla ta, dan ba karaman mahaukacin duka suka mashi ba, ga jini sai fitowa yake daga jikinshi.

Dakyar ya tashi zaune suka turo mashi ledojin gabanshi, in badda zalinci irin na dan daba ina zai iya shan ko ruwa cikin wannan yanayin? Amma haka ya daure yana scrunching up face dinshi with so much pain ya fara cin shawarmar nan yana jinta kamar magani.

Dakyar yaci daya ya dago yana kallon T, wanda daga gani duk ya fisu rashin imani, "Ka taimaka kayi hakuri, wallahi bazan iya cinye shawarma har guda goma ba." Zuwa yanzu hawayen Arhaan suka gangaro, saukar shawarmar nan a cikinshi kamar wani dutse haka ya jita, ga wani azababben ciwo da ilahirin jikinshi ke mashi.

"Kai Gatari, Zarto, kuzo kuyi mashi dure, dolene ya cinyesu tas dan uwarshi! Bamu saba aika bako lahira da empty stomach ba!" Wata irin shewa suka saki cike da mugunta suka nufo Arhaan da idanunshi suka raina fata.

Cikinshi Zarto ya kaima wani irin naushin dayasa dole ya saki ihu, kafin Gatari ya bude bakinshi wangalgal kamar zai ci dan saniya. Katuwar shawarmar nan sai an rabata biyu, rabi sai ya tura mashi ciki, idan yaki tauna kuma Zarto ya naushi cikin_cikin kuka da azaba sai dayacinye shawarmar nan tas, yana shan ice cream roba ta biyu sukaji kamar karar mota zata shigo layin, in the blink of an eye-suka hau machine dinsu suka falle, dukda dai T yaso ya hallaka wanda duk ya wulakanta mashi Sakinarshi.

Arhaan kuwa zubewa yayi a wajen yanata uban amai kafin daga bisani ya suma. Baban Shaheed na shigowa layin yaga mota kamar ta Arhaan parked in the middle of the road, kalla yayi sosai yaga dai tabbas ita dince dai. Parking tashi motar yayi kafin ya sauka, idanunshi suka sauka akan Arhaan da yake kwance male male cikin jini, amai ga kuma ledar shawarma da robobin ice cream watse gefenshi.

Swiftly, he was beside him, lifting him into his hands. Bai damu da jinin ba balle aman dan ya kasance mutum mai tsananin kyama. Ganin dai da gaske Arhaan ba motsi yake ba yasa dakyar ya daukeshi ya saka mota daga nan ya juya sai asibiti.

***

Sakinah na zaune idanunta sunyi suntum saboda kukan data yini tanayi, Aunty Halima tayi ban hakurin harta gaji, amma haka ta share yinin gaba daya tana kuka. Tunda taji an fara kiraye kirayen sallar la'asar gabanta ya fara fadi, dan tasan confirm kila ma Ya T ja iso-and wajen 4:30 Arhaan ke dawowa.

Tana zaune deep in her thoughts, sai ga Aunty Halima ta shigo dakinta rude hijab dinma a wani jirkice ta saka ta ga wayarta a hannu sai hawaye take kamar ranta zai fita. Gaban Sakinah wani dukan uku uku yayi kafin ta mike ta nufi Aunty Halimar, "Auntynmu lafiya? Meke faruwa?" Ta tambaya, kamar bata da tabbacin aika aikar Ya T ce ta bayyana.

"Sakinah Arhaan, innalillahi. Suna asibiti da Baban Shaheed, bansan me zan fadawa Mama ba Sakinah, ta kirani tace sai neman wayarshi take bai dauka ba!" Kuka take sosai tana rike Sakinah kamar her life depends on her, and for a second, Sakinah felt a slight feeling of guilt.

"To mu tafi asibitin ki ganshi mana Aunty, ita kuma ki fada mata gaskia dan Allah, kar tayi tunanin wani mugun abun ne," Sakina cajoled, tana janyo hijab dinta dake saman kofar dakin. Nodding kai Aunty Halima tayi alamar ta yarda da maganar Sakinar kafin suka fice dakin gaba daya, zuciyar Sakina har wani tsalle take ta kosa taga irin jina jina din da aka mashi ko hankalinta ya kwanta, ganin ta dauki hanyar ramawa. Dan wannan kadan ta mashi.

Mota suka shiga Aunty Halimar ta tada ta debi motar nan da uban gudu ga hawaye saman fuskarta. Suna kaiwa karshen layi sukaga motar Arhaan-dukda dai Baban Kamal ya rufe ya tafi da makullin-amma ga jini nan male male da robobin ice cream and remnants din shawarma-ganin jinin dake wajen yasa Aunty Halima sadakarwa, ita kuma Sakina cikinta ya duri ruwa gudun ace Ya T kashe dan mutane yayi, gashi dole ayi bincike kuma dole a gano su.

Suna isa asibitin suka iske Baban Kamal a waiting room sai safa da marwa yake ga wayarshi ya kura ma ido alamun yanzu ya gama wayar. Da gudu Aunty Halima ta ruga wajenshi ta rungume shi tana fashewa da wani kukan, lallashinta yayi dakyar ya samu tayi shiru kafin ya fada mata Mama ta kamo hanyar Kaduna. Itama tasan hakan zata faru dama.

Suna zaune sai ga doctor din ya fito ya kirasu office dinshi, harda Sakinah kamar jela haka ta bisu suka shiga office din. "Amm...wato Alhaji gaskiya yaroncan yaji jiki, bayan dukan kawo wuka da suka mashi-sai da suka kunsa mashi uban abinci I think shawarma ne, saboda saida muka fitar da dukkan abincin dake cikinshi-dan akwai internal injury a cikinshi, da alama sun dakar mashi cikin sosai. Yanzu dai babu wata karaya amma bazai taka ba sai munga yadda hali yayi, saboda duk wani joint na jikinshi saida suka buga. Yanzu yana resting room ne, zaku iya ganinshi nanda awa hour biyu haka. Allah ya kara lafiya."







Allah sarki Arhaan😭💔

Ya T ba sauki😂 ina zai iya tusa shawarma har 10?

Sakina buri ya cika💃

Nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now