BABI NA SITTIN DA UKU

1.6K 250 93
                                    

Ko cikakken five minutes baayi ba sukaji kugin motacin yan sanda ba jimawa saiga yan NDLEA. Dan har lokacin dukda Arhaan is certain Sakina ta suma amma Ya T bai daina dukanta ba. Yan sandan ne suka rike Ya T kafin Arhaan a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a jiki ya taka har inda Sakina take kwance cikin jini ya dauko ta.

Juyawa yayi ya kalli ogansu yace su wuce dashi office dinsu zasuyi magana da manyansu. Ganin suna niyar tura Ya T cikin mota Inna babu inda tashin hankalinta bai kai ba. Ita dama bata taba ganin mijin Sakinar ba, koda ta ganshi a tsaye Ya T na jibgar Sakina tayi tunanin kawai unguwar yazo, sai yanzu ta gane relation din.

Gaban idanta babu irin magiyar da bata ma yan sandan nan ba akan karsu tafi da Ya T amma ko gezau, shi kuma Arhaan bayan ya saka Sakina cikin motarshi he waited for Inna ta gama da yan sandan yaje ya gaidata, dan ko babu komai she gave birth to his wife. Dole akwai wannan respect din tsakaninsu.

"Maza ka kirasu su sakar man dana!" A fusace ta juyo kan Arhaan tana kallonshi cike da tsana, dan duk iskancin da Ya T yake mata bata da kamarshi a zuciyarta kowa yasan da wannan.

"Inna ina yini? Ya gida?" Har kasa ya duka ya gaidata kafin ya mike da niyyar shiga mota ya wuce da Sakina asibiti, dama jininshi a kan akaifa yake, tunaninshi bai wuce halin da Sakina take ciki ba.

"Idan da ban wuni ba zaka ganni? Ahaan kake ko wa? Wallahi tallahi ka gaggauta sakar man yaro tun muna shaidar juna dakai. Dan ya daki wannan tambadaddiyar? Ina ruwanka to? Ba nan ka barta wata da watanni ba ko waiwaiyarta bakayi ba? Sai yau kasan ka damu da ita? Ka sakar mun yaro na fada maka, ta mutu ma in taga dama!"

Baki sake Arhaan ya tsaya yana kallon Inna, ashe dai Sakina da gaske take data ce mashi she envy him akan Mama, so this is the person she has as a mother kenan? What a life? Sai yaji ta kara bashi tausayi, ya juya yaga yanda take sauke numfashi daya daya ga juma jinin da bai daina zubowa ba.

"Amma Inna baki tunanin yanzu abu mafi mahimmanci shine nakai Sakina asibiti? Tana iya rasa ranta da abunda ke cikinta fah." Shi bai saba rashin kunya da tuni yama Inna ya shige motarshi ya barta nan wajen tsaye, amma abunda ya lura da matar nan shine indai ya biye mata to tabbas saidai gawar Sakina.

"Wane ciki kuma? Ciki kuma ai tun fitowar jinin farko ya balle, inma zaka daina tada ma kanka hankali a banza ka daina. Ita kuma inta ga dama ta mutu dan wallahi ya fiye mata sauki akan azabtar da itan da zanyi har sai ta fada man su ubanwa sukayi raping dinta."

"Inna kiyi hakuri amma zan wuce da ita asibiti, dama ni na kawota to na dawo na dauketa. Kayanta kuma idan tana bukata zan aiko a karbar mata." Yana fadin haka bai kara jiran abunda Inna zata fada ba ya shiga motarshi yabar unguwar gaba daya, yana kallo ta mirror yadda Inna ke zazzaga masifa yan unguwa duk sun zagayeta, saidai kawai ya girgiza kai.

Harmony hospital ya kaita, suna isa nurses suka tafi da ita emergency, zaune yayi a reception saida ya gama biyan dukkan wani bill sannan ya rasa wa zai kira ya fada mawa, sai a lokacin yaji hawaye sun sauko mashi, yanzu shikenan babu Mama fa ko? Da Mama na nan yasan tabbas abubuwa da yawa basu faru ba. Gashi Aunty Halima bata nan, yasan dole Sakina sai ta kwana a asibitin nan koda kuwa zai iya neman mata transfer zuwa Abuja. Su Safiyya kuma basu nan ma bata gidan ba da ya saka Safiyya driver ya kawota ta zauna da ita.

Kara trying number din Aunty Halima yayi amma to no avail. Sai can wajen azahar kafin doctor din ya fito kallon Arhaan yayi ranshi a bace yace mashi ya biyoshi office. Arhaan na zama doctor din ya far masifa, "Haba malam daga ganinka kana da ilimi na Addini dana boko, kan wane dalili zaka kama matarka kai mata irin wannan dukan? Akan laifin me? Kasan she has the right ta kai kararka wajen yan human rights su karbar mata hakkinta? Haba wannan dukan har ya fita daga cikin na masu hankali."

Masifa doctor din yakeyi, ta inda yake shiga ba tanan yake fita, shi kuma Arhaan yace mashi bashi yayi dukan ba ma ya gagara, duk tunaninshi bai wuce ya Sakinar take ba. Mikewa tsaye yayi dayaga doctor din baida niyyar fada mashi halinda take ciki yace "Yanzu doctor a wane daki zan sameta?" Dan dama ya riga daya biya kudin daki daya, shi bai iya wannan kwamacalar ba.

"Room 25." Abunda ya furta kenan Arhaan ya fita daga office din yayi hanyar amenity rooms. Duk taku daya dayake kusanta shi da dakin da Sakina take ciki wani irin huge blow ne ma zuciyarshi. Ya kusa five minutes bakin kofar dakin kafin a hankali ya murda handle din ya shiga.

Kwance ya ganta tana bacci, fuskar nan tayi fayau ga drip sun saka ma hannunta. Chest dinta ya kalla yaga yadda numfashinta yake hawa yana sauka cike da azaba, wani tightness yaji a chest dinshi. Duk fa shi yaja mata ko? Koma wani hali take ciki, duk abunda ta rasa yasan shi yaja.

Har yakai bakin gadon idanunshi basu matsa daga face dinta ba, shikam abun ya mishi yawa, ga Mama ga Sakina dame zaiji? Zama yayi kan kujerar dake gefen gadon a hankali ya riko hannunta da babu drip din a jiki, yana rike hannunta memories suka dawo mishi wanda sukayi a asibiti, ga dariya ga kuma kuka. Rayuwa kenan tayi jinyar shi bayan Ya T ya dake shi shima yau zaiyi jinyarta bayan Ya T ya daketa.

Bata farka ba sai bayan laasar, ko bude ido batayi ba ta fara neman ruwa, shi yama manta ana siyo abubuwa idan zaayi jinya, cikin hanzari ya fita yaje shagon nan cikin asibiti ya siyo mata ruwa da sauran abubuwan da zaa bukata ya dawo. Lokacin ya sameta tana zaune kan gadon ga doctor dinnan da nurses biyu gefenshi. Yana shigowa Sakina ta juya ta mishi wani mugun kallo kafin ta dauke idanta, kallo ne mai cike da ma'anoni, kallo ne irin wanda aka kashema wani makusanci nashi yake yiwa wanda yayi kisan. Take jikinshi yayi sanyi.

Fita sukayi suka barsu su kadai, ruwan ya mika mata ta karba amma ko kallon inda yake batayi ba, abunda ya lura dashi shine tunda ya shigo dakin hannunta yake kan cikinta, sai lokacin abun ya dawo mashi, Sakina is supposed to be pregnant amma Inna tace cikin ya zube?! A hanzarce ya fita dakin ya koma office din doctor din.

Yana shiga ko zama baiyi ba tambayar daya fara mashi itace "Doctor cikin jikinta, yana nan?!" Hankalinshi a tashe, babu inda baya rawa a jikinshi, sai yanzu ya dawo hayyacinshi, Sakina might not be a virgin when he met her, amma for sure yasan wannan cikin nashi ne. He dread ansar da doctor din zai bashi dan kuwa in har cikin nan ya zube shida Sakina babu zaman lafiya, ta mashi laifi of course amma nashi yafi nata, shi kisa yaja akayi, dan da lokacin da Ya T... bai ida tunanin ba yaji Doctor ya furta.

"I'm sorry but babu cikin, and we couldn't hold it back no matter how we tried." Rawa legs din Arhaan suka fara dan dole ya samu waje a zauna a office din.

Ya kusa five minutes shida Doctor din babu wanda ya cewa kowa komai, Arhaan kuka yakesan yi amma idan abun tashin hankali irin wannan ya faru babu a inda yake iya yin kuka face wajen Mama. Dakyar ya mike ya koma dakin Sakina, kuka ya iske tanayi kamar ranta zai fita.

Ya dade a tsaye yana kallonta kafin ya shiga ya zauna saman kujerar dake kusa da gadonta. So yake ya mata magana, atleast ya bata hakuri amma ba dama, hanky ya ciro a aljihunshi ya mika mata ko kallonshi batayi ba balle ta karba.

"Arhaan, my child, my poor baby. Babu abunda yayi na laifi fah, he was innocent amma tun kafin yazo duniya kaddarata ta sameshi? Shin dama haka ake mayar da soyayya? Dama tsakanin masoya babu yafiya da fahimtar juna? Dama abunda kakeso shi ke wahalar dakai?" Sai kuma ta fashe da wani kukan, Arhaan cannot take it anymore, yadda take kukan yasan koda shi akace mata ya rasu iyakar kukan da zatayi kenan.

Tashi yayi ya hau gadon hade da hugging dinta, tanajinta a jikin ta kara fashewa da wani kukan, bai san yanda akayi ba sau shima yaji hawayen sun fara saukar mashi. Kuka sukeyi mai cike da ma'anoni, kukan rashin babynsu, kukan rashin junansu, da kuma rashin Mama.

"Anina...What should I even say?" Kafin ya karasa magana ta tsaida shi hade da raba jikinshi da nata.

"Don't ever call me that again, Arhaan din dana sani da shine yake kirana da Anina, ba wannan Arhaan din ba mara tausayi da imani, ba wannan Arhaan din ba da yayi silar rashin dana."


Aishatuh is a very good girl😁🎊

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now