BABI NA SHA SHIDA

1.6K 232 10
                                    

Fira ce sukeyi kamar wadanda suka dade da sanin junansu; dukda dai kowa da abunda yake tunani a zuciyarshi_amma hakan bai hanasu labartawa ba cikin nishadi da walwala.

Ganin ya kammala cin abincin yasa Habiba mikewa tsaye ta dauki tray din, "Toh Dan gayu, bari naje ciki_you eat well by the way," and she smiled warmly at him, before turning on her heals_leaving him rooted on his spot.

Saheer ya dade yana tunani akan yadda rayuwarshi ke serving dinshi fortuitous things_things he never expected. But one thing he knew is_dole ya binciki asalin wannan yarinya, she seems in a grief, and dole ya fiddota daga cikin damuwar da take ciki.

Mota ya koma ya zauna, but still tunanin Habiba ya mashi tsaye a rai_just then; he come to the conclusion that she might probably be an orphan. Da wannan tunanin ya samu hankalinshi yadan kwanta_but fuskarta musamman lokacin da rana ta bugeta was lingering in his eyes.

Can yamma lis Maama ta fito sai baza murmushi take cike da dattaku. Yana ganinta yadan hade rai, alamun tasan fa shi har ga Allah bawai tana kyauta mashi bane. Ta gane sarai abunda yake nufi amma tayi fuska, sallama suka karayi da Hajia kafin ta shiga ya jasu sukabar harbar gidan babu mai cewa komai.

To end the eerily silence in the ambience yasa Maama dubarshi tana murmushi, har ga Allah tana matukar kaunar dan nata. "Saheer nikam kaci abincin ko? Nasan halinka da rike yunwa," ta furta tana kureshi da idanu_dan gano koda karya yake.

"Eh naci," abunda ya furta kawai yana pinching the gap between his eyes, while his attention was fully on the road.

Idan da sabo Maama ta saba, dan kusan kullum yanzu cikin fada suke da Saheer saboda yawan zuwanta gidan Hajia. Kuma shi bawai zuwa dashi ne yafi bata mashi rai ba_Aa, yasan tabbas duk abunda waccan matar take ciki bana alkhairi ba_dan haka bayasan Maama dinsa tayi embroiling kanta into that mess.

Bata kara cewa komai ba, sai ma ta fiddo wayarta ta shiga whatsapp_dan akwai wasu kaya masu nagarta da akace zaa turo mata. A haka suka karasa tankamemem gidansu; horn yayi aka bude kafin ya danna kan motar cikin humongous harabar gidan.

***

Wajen 9am Arhaan yayi diran mikiya a Birnin tarayya. Dan shi idan yan zuwa gidanshi suka kado mashi_to sometimes ma yana sallar asuba yake wucewa_yauma saa akaci yakai har 7 da wani abu.

Cike da dokin ganin Mama yayi parking motarshi a parking lot hade da wucewa direct cikin gidan. Kamar yadda ya saba; dukda kuwa bamai yawan magana bane shi_duk ya dawo sai ya fara shiga shahin Mummy kamar yadda suke kiran kishiyar mahaifiyarsu ya gaisheta. Mace mai kamala da mutunci, duk da kuwa opposite suke da Mama ta fannin halaye. Mama ta kasance mai sanyi hali da gaske_wanda magana kadai sai kuyi awa daya zaune batayi ta ba_while Mummy itace ke dispila yaran gidan; dan baki ne da ita in ta fara magana har gate akan jiyota.

Yana shiga yaga sister's dinsa biyu zaune a parlour suna breakfast. A tare suka dago suna kare mashi kallo; basuyi mamakin ganinshi ba: dan kowa yasan abunda yake maido Arhaan gida.

"Muhibbah, Mummy na ciki?" Ya tambaya, ganin sun tsareshi da ido amma ko wacce ta kasa koda gaidashi ne_not that he cares. Dan yadda yake dan yauk'i kusan zaa iya cewa sunma fishi.

"Ya Arhaan barka da zuwa fah, an dawo ganin Mamar ko?" Safiyya wacce itace autar gidan kuma sai ka rantse da Allah Mama ce ta haifeta saboda kusan halinsu daya; amma itama bata daukar raini idan an tabata.

"Eh na dawo, yan mata ansha kyau sai school ko?" Ya amsa mata da faraa amma.

"Sannu da zuwa Ya Arhaan, Mummy na ciki," Muhibbah ta amsa tana maida hankalinta kan wayarta.

Gaisawa suka dan karayi harda dayar sister dinsu kafin kowanne ya wuce inda zashi_saida suka gaisa da Mummy bayan ta gama mashi tsiyar yaki girma har yanzu yana da kuiyarshi dai; komai sai Mama. Sallama ya mata cikin raha da girmamawa kafin ya nufi sashin other half dinshi_feeling giddy.

"Maamaaaa," he drawled, a yayinda ya karasa dakinta. Can ya hangota zaune kan sofa ta kurawa TV ido tana kallon Zee world.

"Laaah! Dan Mama!" Ai bata jira ya karaso ba ta mike ta nufoshi, gam ya rungumeta yanata murmushi kamar ya tsinci hakori.

"I missed you sooo much, Mama. Kinga yadda kika kara kyau kuwa?" He jested, a haka suka karasa saman kujerar da take zaune.

Dan dukan kanshi tayi cikin wasa kafin ta tsaya tana kallonshi cike da so da kuma kaunar da babu irinta inba tsakanin uwa da d'a ba. "Kai Dan Mama ka rame Allah. Meya faru? Halan abinci ne bakaci ko? Ita kuma bata tursasa maka ko? Sannan ga damuwa nan kwance cikin idanunka. Akwai abunda yake takura ka probably." Duk wadannan maganganun tayisu ne without taking her eyes off him.

"No wallahi tana kula dani sosai, abinci ma da kanta takeman ta kawo man har sai naci kafin take barin bangarena. And babu abunda yake damuna, I was just missing you!" Shi ko giyar wake yasha ai bazai taba fada mata ga wanda ya takurashi ba, kawai ya saka a ranshi dole Sakinah ta gane kurenta.

Sun dade suna fira kafin Mama ta saka aka kawo mata breakfast dinta_dan dama bawai ta saba cin abinci da wuri bane. Gaba dayansu kasa suka sauka. Arhaan kuwa sangargar yayi kamar yaro dan shekara 5 Mama na bashi abincin, har irin 'Aaa wululun wulun ammmm' dinnan take mashi. Shi kuma ya saki baki babu kunya ya amshe. Duk duniya ba'a halicci abunda yake so ba sama da Mama. She is his world.

***

Sakinah ce zaune cikin dakinta, yau Alhamis duk basa gidan sun tafi Islamiyyar marece. Kukane take rairawa cikin sauti mara dadin sauraro, amon muryarta na tashi cikin ko wani sashe na gidan_dan kuwa it was as quit as a graceyard.

Tun bayan wannan incidence din nasu da Baban Shaheed, zaman gidan nan bai kara mata dadi ba_saidai idan basu hadu ba_amma confirm sai yayi abunda zaisa tayi feeling unwanted, tayi feeling worthless and nothing but a looser in life.

Yanzu zamanta a gidan ya koma indai yana gidan to dole tayi kuka. Takai ta kawo ma da su Kamal, Hafsah da Shaheed na ganin mutuncinta amma yanzu babu mai gani_musamman Kamal da Shaheed and Aunty Jamila doesn't have a say in that.

Koda ta zauna yanzu tunanin rayuwarta kawai take; babban abun takaicin ma shine wai duk kan d'a namiji take wannan wahalar da rayuwar kaskancin. Namijin ma da bata sanshi ba, bata san kamanninshi ba, sannan batasan wether if he will be worth it.

Wani marayan kuka ta saki a lokacin da brain dinta ta tuno mata da Habiba_Allah sarki Habibi, ko wace irin rayuwa takeyi? Tanajin dadin gidan koko itama a takure take kamar ita? She missed Habiba so bad, koda sau daya ne tana so suyi magana_dan ba lallai bane su hadu koda sunje gidan-baima zama lallai ba zuwansu gidan anytime soon.

Duk Inna ce ta ja masu wannan abun, da bata jajirce ta fi karfin Baba ba da yanzu suna can gidansu cikin mutuncinsu da kwanciyar hankali.

Batasan da shigowarsu gidan ba saidai kawai taji maganar Kamal cikeda rashin kunya da rashin ganin girmanta. "Sakinah kije Daddy na kiranki," ya furta kafin ya ruga ya fita dakin. Ita kuwa hab'a ta rike, dan da duk wulakancinsu sundai kirata da Aunty Sakinah. Ganin abunda ke gabanta is worst more than this yasa kawai ta mike tana salati ta fita parlour din.

Tana fita ta ganshi zaune saman daya daga cikin sofas din, fuskar nan a hade kamar saukar aradu_wanda saida yan cikinta suka yamutsa. Matsawa tayi ta duka kafin ta furta zuwanta.

Yafi karfin minti goma kafin ya fara magana cike da gasaita da mulki irin na masu kudi. "Wane irin sakarci ke damunki? Baki ganin Habu mai gadi bayanan kuma baayi sharar harabar gidan ba? Tashi ki wuce ki share wajen tas!" And he left no room for argument, baima jira ta gama scuppering words dinshi ba kawai ya tashi fuuuu ya wuce part dinshi.

With a heavy heart Sakeena ta dauki tsintsiyar kwakwa ta fita tsakar gidan. Girman farfajiyar ya wuce tunaninta_hakan ya haifar mata da wata mummunar faduwar gaba. Ta ina zata fara share wajen nan duka? Gata dama da san jiki when it comes to shara, and Habiba was always at her rescue_amma yanzu there wasn't anyone to save her-dole ta duka ta fara sharar daga inda taga zata iya.

Sharar take tana rhyming sad songs din India, Hausa da Turanci duka, babu ruwanta da tayi daidai ko bata yi ba_gwamutsa su kawai take.

Wani irin himilin ganyen flowers ta gani, can iyakar karfinta ta saka kafin ta hankadi sharar wajen yan uwanta_and fitarsu a wajen basu sauka akan ko'ina ba sai kan kafar da she wasn't doubting ta namiji ce. Amma namijin wane cikinsu? She couldn't risk looking up at the face.






Just finished ny exams today! 
Shower me some love!

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now