BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

1.4K 221 14
                                    

Ko ya akayi? Oho. Amma haka suka tsinci kansu da kasa sakin juna. Ita kam Sakinah ta lafe saman chest dinshi, while Arhaan was feeling on cloud nine saboda jikinta dake hade gam da nashi.

Can hankalinta ya dawo kanta, dan ganin shima dinnan yama manta da niyar mugunta ya kamota. Dakyar, dan ji take kamar ilahirin sassan jikinta suna narkewa; dan gaba daya kuzarinta ta nema ta rasa.

"Ai sai ka sakeni ko? Bakin azzalumi," maganar kawai tayita ne dan kar ya dauka ko taji dadin kasancewar su a position din da suke. Because it's obvious he's enjoying every bits of it.

Saurin sakinta yayi, itama a hankali ta janyo hannunwanta daga bayan shi data rungumeshi. Tana mikewa tsaye ta kauda kanta gefe kafin ta kara mikar da pillow din daya jingina akai. "Ka kalli gabas kayi sallah, zan dan koma na kwanta." Abunda ta furta kenan without looking into his eyes. God! Only her knows the tons of feeling scattering the floor of her soul. She's confused.

Arhaan bai mata gardama ba. Yadda tace din haka yayi. Niyar sallar asuba yayi a zuciyarshi kafin ya gabatar da sallar duk a zuciyarshi yana hango kanshi a yanayi na mai sallah kamar yadda addinin musulunci ya koyar. Koda ya gama sallar gyara kwanciyarshi kawai yayi ya kulle idanu bawai dan yanada tabbacin baccin zai iya daukarshi ba; saidan kawai ta take away the picture of Sakinah cocooned in his arms.

Yadda kasan an narka kitse haka Sakinah ta malale saman katifar Mama. Ita ba me bacci ba haka zalika ita batayi tunani ba. Abun duniya ne ya taru yayi mata yawa; irin abun nan na jiya takeji yana mata yawo; amma ita bazata iya cewa ga abun ba, dan bata sanshi ba, bata saba dashi ba, zata iya cewa bata tabajin irinshi ba.

Upper part of her body takejin abun. Kota ina yake mata yawo. Duk inda Jikinta ya tabu na Arhaan to lallai takanji abun yabi ta wurin kamar tafiyar kadangaru. Ta cikin kirjinta taji yabi, tanaji ya cunkushe mata lungs dinta har ta kasa numfashi; abun ya fara bata tsoro. Kodai wata cutar takesan kamata?

Idanunta dake rufe kuma babu abunda suke hango mata face yanayin da suka shiga da Arhaan dazu. Tanajin tafiyar abun nan, tanaji ya tsaya daidai saitin zuciyarta, tanayi yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fito daga cikin kirjinta. This feeling is new to her, a stranger to her.

Kamar ana tsinka jijiyon dake hada da zuciyarta da gangar jikinta haka taji, wata irin mummunar faduwar gaba taji kafin a gaggauce taji shigar abun; shigace yayi mata cikin sauri babu ko kakkautawa ko taji saukin raddadin da ruhinta ke mata.

Sakinah batasan lakacin data saki kuka ba, dan ita duk a tunaninta wallahi wata irin muguwar rashin lafiya ce ta shige ta, dan kuwa yanzu ko yatsanta batajin zata iya dagawa. Komai ya tsaya mata cak, jikinta yayi sanyi karara kamar mai shirin mutuwa.

Tana cikin wannan shashekar kuka sai Mama tayi sallama hade da shigowa dakin. Ganin Sakinah kwance saman katifa tana kuka ba karamin daga ma Mama hankali yayi ba. Saurin karasawa tayi ta dago Sakinah hade da dora kanta saman cinyarta.

"Sakinah meya faru? Lafiya kuwa? Ko wani abun ne ya sameshi kuma?" Mama ta tambaya duk a kidime, amma da alamu Arhaan bacci yakeyi; lura da yadda numfashinshi ke sauka a hankali.

Abunda Mama bata sani ba shine tun kafin shigowarta Arhaan yaji sashekar kukanta, amma yadda yakeni shima da zai samu yayi kukan da abun sai yafi mashi sauki. He doesn't want to make Mama curious, that's why tana shigowa ya fara sauke numfashi alamun me barci.

Sakinah dagowa tayi da jajayen idanuwanta tana kallon Mama, dan kuka take rigis bil hakki. "Mama ban lafiya. Kaina yana man ciwo, sannan inajin wani abu yana man yawo cikin jikina, har ya cunkusheman lungs dina kafin daga bisani naji shigarshi cikin zuciyata da karfin gaske. Kila ma mutuwa zanyi ko? Tunda gashi jikina yayi sanyi karara, kuma ko hannuna na kasa motsawa." Kuka take sosai bil haqqi ita duk a tunaninta mutuwa zatayi. Babbar damuwarta bai wuci Habibah data dade bata gani ba. Inna ma tayi kewarta, babansu daya kasance kullum yakan tsaya suyi hira bayan yaci abincin dare, Ya T; shikenan Allah baiso zataga shiryuwar Ya T ba?

Wani kukan ta kara fashewa dashi. Rungume kugun Mama tayi tanajin a hankali yanzu abun yanabin duk wani lungu da sago na bargon jikinta. Wallahi batasan menene ba, amma tabbas abun baida dadi ko kadan. Kodai fitar rai ce toh?

Kafin Mama ta bata amsa ta cigaba "Mama idan na mutu ko? Dan Allah a maidani wajen Innata taman wankan gawa, a roki Ya T kar yasha komai yaje shida Baba su binna kabarina su rufeni. Ita kuma Habibah ace mata ina kaunarta sosai, Allah baiyi zamu rayu tare ba ko? Kice mata nace ta roki Inna ta koma gida tabar aikatau dan Allah. Ai zaki man wannan Alfarmar ko?" Tana kuka tana jijjiga Mama take magana, sosai dan zuwa yanzu Mama ta gama kidimewa, cikin hanzari ta zaunar da ita da niyyar kiran doctor.

Sakinah bayan Mama ta zaunar da ita, daga idon da zatayi-Arhaan wanda ya kasance tun bayan ta fara maganar mutuwa ya mike zaune a kidime ya kura mata ido-hada ido sukayi, nan take taji gabanta ya wani tsinke ya fadi kamar fitar rai, sai ta saki kara.

"Shikenan Mama yanzu zasu tafi da raina!" Kuka sosai tana runtse ido alamar tsoro da fargaba, abun ya kidimar da ita.

Ganin yadda take yasa Mama tayi tunanin ko shafar aljanu ce, hakan yasa ta dawo ta zauna kusa da Sakinah hade da fara tofa mata addu'o'i tanayi Sakinah na kuka, wadda idanunta a yanzu suke a rufe sai girgiza kai take alamun bafa tasan ta mutu da gaske.

Ganin kukan ma Sakinah ya tsagaita yasa Mama tallabota, "Sakinah kiyi shiru kinji? Ba mutuwa zakiyi ba da izinin Allah. Yanzu fada man me kike gani?" Mama ta tambaya cike da kauna da kulawa, dan yarinyar ta tsoratar da ita ta kuma bata tausayi.

Saida Sakinah ta sauke numfashi kafin ta kara kulle idanunta, amma babu abunda take gani face fuskar Arhaan; wanda hakan ba karamin kidimar da ita yayi ba. How can she tell Mama that the only face she could see is Arhaan's? Wai shin miye ma'anar hakan ma? Koma duk wannan abun saboda shi ne? No way! Tayi saurin dakatar da kanta.

"Ba komai." A hankali ta amsa da muryar da taci kuka har ta gode Allah. Saida Mama ta kara tofa mata addu'o'i kafin ta umurceta akan ta kwanta ta samu bacci kafin su Aunty Halima suzo sai taje gida ta huta.

Hakan take da bukata, babu musu ta matsa can karshen katifar ta cunkushe kanta into a ball. Tanajin lokacin da Mama ta mike ta nufi gadon Arhaan, sama sama takejin firarsu har bacci yai awon gaba da ita.

Cikin bacci Sakina taji kamar ana mata magana sama sama, a hankali ta fara squinting eyes dinta kafin ta saukesu kan Aunty Halima dake kallonta with eyes full of concern. Tasan daya daga cikin rashin hankalinta ne ta tafka ma Mama dazu, hakan yasa wata kunya ta lullube ta.

"Sannu Sakinah, ya kikeji yanzu? Zaki iya motsa hannun ko?" Wayyo kasa bude ta shige, wata irin kunya taji da Mama ta tambayeta hakan.

Murmushi tayi cike da kunya kafin ta duke kanta, "Wallahi Mama dazu ciwon kan nan kamar zan mutu; ni bai taba man irin haka ba ma. Amma yanzu banajin komai." Ta furta tana kokarin mikewa don karbar plate din da Aunty Halima ke niyyar kawo mata.

"Koma ki zauna mana, keda baki da lafiya." Aunty Halima ta furta tana me kin bata plate din.

Komawa tayi ta zauna tana fadin "Kai Auntynmu, naji sauki fah." Umurtarta Aunty Halima tayi akan taje ta dauraye bakinta kafin ta fito taci abincin, tunda dai yanzu basu da brush anan sai taje gida.

Har taje toilet dinnta dawo bata ko kalli inda Arhaan yake zaune ba yana jifanta da kallo sama sama. She wants to clarify something, and doing so; is estranging herself from Arhaan completely.

Tanaji suna firarsu amma ko uffan batace masu ba har ta gama ta zauna tanata tunanin yanayin data shiga dazu. Can ta jiyo muryar Aunty Halima tana fadin.

"Sakinah ga makullin gidan kije ki hada mana abubuwan da babu dan Allah. Baban Shaheed in ya taso aiki sai ya kawo. Sai kuma ki gyara gidan, amma fa in kinji zaki iya; in baki iyawa ki kwanciyarki anjima in nadawo mayi tare." Tana fadin ta miko mata makullin hade da kudin napep kafin Sakinah ta mike ta gyara hijab dinta.

Saida Sakinah ta kara jaddada mata akan ta warke amma Aunty Halima bata yarda ba saida tace da ta koma gidan zata kirata da wayarta. Har Sakinah tazo zata fita dakin amma bata kalli ko karfen gadon da Arhaan yake kwance ba.

Ganin da gaske tafiyar zatayi ba tare da sun hada ido ba, shi kuma after moment dinnan na dazu; kawai ya tsinci kanshi da san kallon her doe like orbs. Tarin karya ya farayi, wanda hakan yayi daidai da dagowarta idanunsu ya hadu. Wani irin lopsided smile yayi flashing mata, ita kuma she pouted her lips at him and walked off. That pout, if only she knew!

Thank you!

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now