BABI NA SITTIN DA TARA

1.7K 202 35
                                    

Tunda ta tafi ya nemi kwanciyar hankalinshi ya rasa. Yafi awa uku zaune cikin office dinnan amma sam baya gane wake shiga da kuma wake fita. Tun ranar daya fara ganinta a gidan Hajia yake tariyowa, da irin maganganun da take mashi, kukanta, yadda hawaye ke zuba saman cheeks dinta, how he body vibrates as she cries. Karar ringing tone dinshi ne ta katse mashi duk wani tunanin shi, dan karamin tsaki yayi, yana duba wayar yaga Maama ce.

Dauka yayi ya kara a kunnenshi, gaidata yayi kamar yanda ya saba kamar yayi shiru alamun ta fadi abunda yasa ta kirashi. "Saahir zaka kai nan da three hours baka dawo gida ba?" Abunda ta tambaya kenan, ta saba mashi wannan tambayar duk in baya gida, shi bai kawo komai a ranshi ba.

Agogo ya kalla yaga 12pm har ta dan gota, baya tunanin zai iya kaiwa har wajen 3 cikin office dinnan, "Eh Maama zan kai, fita zakiyi ne?" Haka nan yace mata zaikai, dan yanzu idan yace baijin dadi zai dawo gida ta dinga takura mashi da questions.

"Aa ba fita zanyi ba, saidai ka dawo din. Kaci abinci kaje Saahir?" Da toh ya amsa mata kafin ya kashe wayar. Wata duniyar ya kara lulawa, abubuwa ne suke kara dawo mashi kamar lokacin ake yinsu. Duk wasu suspicious abubuwa.

Bai kara cikakkar one hour ba cikin office din ya kulle ya fita, restaurant ya fara biyawa ya siya snacks yaci, dan tunda Beeba ta tafi yake kasa cin abincin kowa. Dama can ko tayi yan tafiye tafiyenta saidai ya girka da kanshi yaci, to yanzu ba karfin da zaiyi wani girki balle.

Gida ya nufa direct, koda yayi parking dakinshi ya fara zuwa yayi wanka yayi sallah kafin ya dade yana addua, shikam baima san abunda yake damunshi ba. Kamar wanda aka ja haka ya fara takawa har zuwa dakin Habiba. Yana shiga ya iske shi a yanda ta barshi, kamar ya kurma ihu haka yaji. Sai yaji kamar one of those moments da zai shigo dakin yace "Yar Baka yau baza'a mun girkin bane?"

Wani sa'in sai tayi kamar bata jishi ba har sai ya shigo ya zauna kan kujera kafin ta kalleshi tace "Dan gayu indai har bazaka ansa ka fada kogin nan ba to fa ji babu girkin da zan karayi maka."

Kullum ansar shi indai baice shi yana bakin gabar kogin ba tofa zaice "Saidai kece kika fada Yar baka, amma ni har yanzu ko hanyar kogin ma ban kama ba." Da haka zai lallaba ta ta fito suje suyi girki, ranar kuma da bayajin yan girki saidai ta girka shi yana zaune yana mata hira.

Kauda tunanin yayi a ranshi, dan inhar ya fara tunanin memories dinsu to wallahi sai ya shekara wajen. Direct bed side drawer dinta ya nufa, yana janyowa kuwa idanunshi suka fada kan passport dinta, jikinshi na rawa ya dauka ya buda yaga kuwa sunanta ne. Visas ya fara gani daga wannan kasa zuwa wannan kasa, hankalinshi bai kara tashi ba saida yaga dan madaidaicin photo album dinta.

It's a tradition to her, duk kasar da taje sai taje gaban wani monumental place nasu tayi picture, not only picture din waya kuma, picture ake fiddo mata dashi. Tace ita bata yarda da picture din waya ba, saboda wataran wayar na iya bacewa, sai tayi yaya kuma?

Pictures dinta yaita gani tururu, wanda ciki kashi 100 ko kashi 5 basu kai ba wanda tayi a nigeria. Ranshi yakai kololuwa wajen tashi, hankalinshi babu inda bai kaiba a gushewa, jikinshi rawa yake. Album din da passport din ya fito ya nufi dakin Maama, yasan tana nan tunda ya shigo yaga motar ta is parked.

A bangaren Maama kuwa, tun ranar data kira Hajia suka gama magana ta nufi gidan wata kawar huldarsu, a nanne ta iske an kawo wata tsaleliyar budurwa. Yau aka kawo mata ita gida, dalilinta kenan na kiran Saahir taji in har zai kai 3 hours bai dawo ba. Akayi dace kuma yace eh, dan da yace Aa tabbas to saidai suje hotel. Hankali kwance suka lula duniyarsu ta alfasha.

Suna cike da alfasharsu taji an banko kofa, duk duniya bata taba tunanin zataji tashin hankali irin wanda taji ba a time. Ita ba ganin da Saahir din ya mata ba, tunano kalmomin malaminta tayi "Ki kula Hajia hauwa, koda wasa karki bari ya kamaki cikin wannan siga. Dan kuwa a yanzu aikinmu da yake kanshi ko duk duniya zata taro tace mashi ga halin da kike cike bazai taba yarda ba, ke koke da bakinki kika fada mashi bazai yarda ba, amma the moment idanunshi suka gane mashi, to fa babu sauran boye boye."

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now