BABI NA HAMSIN DA DAYA

1.5K 259 52
                                    

Kuka ne tasha kamar ranta zai fita, ita yanzu duk tunaninta bai wuce abunda Arhaan zai mata ba. Tasan tabbas wannan abun sai yayi triggering back abunda tasa Ya T ya mishi months ago. Ita yanzu ya zatayi? Me zata fada ma Arhaan? Halan ko wajen yan sanda ma zai kaita? Yanzu shikenan sakinta zaiyi kuma ya aika su wajen yan sanda daga ita har Ya T din.

Tana nan zaune tana kuka har aka kira sallar maghrib, saida taji fitar Arhaan ta can kofar part dinshi kafin hankalinta ya dawo jikinta. Jiki a sabule ta mike ta shiga nata dakin, koda ta shiga toilet ta fada tayi wanka ta dan gyara jikinta kafin ta fito ta saka yar loose gown, so take taje ta bawa Arhaan hakuri akan abunda Ya T ya mata, itakam bata taba jin kunyar shi irin ta yau ba. Ai bata tabajin kunyar ba ma.

A hankali ta fara tariyo abunda ya faru tsakaninsu daga fitowar ranar yau har zuwa yanzu da rana ta fadi. The day started as lovely as it ever would, with full of smiles and laughter, as if they were hell bent in love with each other. Sai gashi Ya T yazo ya bata mata yan hours din datayi nurturing cikin farin ciki a rayuwarta. Yanzu da ace soyayyar gaskia suke haka zaizo ya tarwatsa mata farin cikin ta?

Wasu hawayen ne taji sun fara sauko mata. Dama ita tasan wannan abun nasu bamai dorewa bane. Jin an sallame sallah yasa tayi gaggawar tashi ta saka hijab ta nufi part din Arhaan din, jikinta babu inda baya rawa. Tasan what she's doing is not right, amma he owes her an apology ai.

Sai yanzu ta samu damar yima falon kallon kar, ba karamin burgeta yayi ba. Babban falo ne mai kujeru set biyu, yafi nata girma da kadan, ita abunda yaci girma nata saboda dining area shi kuma babu sai wani waje kafin study area ne. Kujerun duka set biyun ba karamun burgeta sukayi ba, haka zalila tv set din da curtains din. Da sauran decorations din. Komai yayi mata tsab kamar ba bangaren namiji ba.

Ta shagalta da kallon tv inda ake nuna masu dawafi a ka'aba. Ashe dama yana kallon islamic channels? She mused and smiled softly. Batayi aune ba taji takun kafarsa gab da ita, wani irin mugun firgita tayi dole tari ya sarketa. Dispenser yaje ya debo mata ruwa ya bata kafin ta samu tarin ya tsagaita.

Ko zama baiyi ba, fuskar nan daure kamar an aiko mashi da sakon mutuwa, ta lura yayi wanka ya canza kaya. "Me kikeyi a nan?!" Ya fada da murya mara taushi balle tausasawa.

Dago da rinannun idanunta tayi kafin ya ankara sai hawaye, rintse idanunshi yayi ya zamu waje ya zauna. Ganin ya zauna yasa Sakinah tunanin kila zata samu sassauci a wajenshi. Kallonta yake babu ko kakkautawa, ita kuwa kuka take kamar da bakin kwarya.

Karshe ma da taga ya furta "Idan kin gama kukan sai ki fitar daga part dina." Ya juya eyes dinshu gaba daya yana kallon tv alamar kwata kwata ma kukan nata baya affecting dinshi. Ya daure fuska tamau babu alamun imani a tare dashi.

Kasa ta sauko, saboda tayi alkawarin bazata taba barin wajen ba har sai yace yayi mata hakuri, bata san yana fushi da ita. Kulawar da ya nuna mata yau da safe yasa taji babu abunda take bukata kamar murmushi da dariyar Arhaan. Ya dandana mata zuma mai saurin sabo da saurin kama zuciyata.

Ganin ta kan guiwowinta ba karamin bawa Arhaan yayi ba, ai ko a mafarki aka ce mashi Sakinah zata durkusa kasa a gabanshi bazai taba yarda ba. Kuka take jina jina. "Arhaan kayi hakuri, dan Allah ba dan halina ba. Nasan I was never good to you, amma abunda yayana ya maka yau banji dadi ba, dan Allah kayi hakuri. I couldn't help it ni kaina, ka yafe man." Ita kanta mamakin kanta take, amma with the intensity she's craving for his soft look babu abunda ba zata iya ba. Ita dai yace ya yafe matan.

"Ki tashi ki fita." He's fighting the urge to kneel down to her level and hug her to his chest, fighting the urge to wipe her tears away and carve a beautiful smile on her face, the kind of smile he saw on her face in the morning while she stretched her body. Kulle idanunshi yayi dan bayasan yana tunanin abubuwan da suka faru da su a safiyar yau.

"Ni bazan tafi ba sai kace ka yafe man, sai kace kayi hakuri. Dan Allah Arhaan kayi hakuri wallahi ba laifi na bane, ban taba tunanin zaiyi haka ba. Ni koda yace wace unguwa nake wallahi banyi tunanin da gasken zaizo ba, dan Allah kayi hakuri. A da can kace ka tsaneni, I was relieved saboda nasan hakan yana nufin ka yafe man amma ka tsaneni for what I did, yanzu ma kace ka tsaneni amma ka yafe man kayi hakuri dan Allah." Ganin ko kallonta bayayi yasa ta dora both palms dinta saman laps dinshi, wani irin shock sukayi su duka, ya juyo ya kalleta kafin ya kalli hannayenta da suka kan kafafunshi. Tabi idanunshi da kallo amma hakan bai saka ta dauke hands dinta ba, she's doing all she can ta samu ita dai yace yayi hakuri.

"Na tsaneki, tashi ki fitar min daga part, karki kuskura ki kara shigowa inda nake. Abinci ma zan maido da me aiki daya ta rika yi mani nawa daban. Koda wasa karki kuskura ki kara tunanin taba jikina. I hate you, now you can get out of my sight or not?!" Ya fada cikin karsashi tare da ture hannunta daga jikinshi, ko second daya bai kara ba a falon ya shiga dakinshi yayi banging kofar.

Wani abu kamar madaci Sakinah taji ya tsaya mata a rai, sai yanzu ta tabbatar ma kanta duk kukan da tayi dazu ba kuka bane, takaicin data kunsa dazu bai isheta ba. Kalmar na tsaneki daya furta ba karamin dagula mata lissafi tayi ba, duk wata kafa dake zuciyarta saida ta tosheta haka zalika ta bude mata kofifin bakin ciki da tarin damuwa.

Kuka ta saki a nan, har tayi mai isarta tana nan zaune. Karatun kur'anin dake fitowa daga tv din shi yayi silar samun natsuwarta har bacci ya saceta a inda take zaune kasan carpet kanta yana bisa kujera.

Can cikin dare yunwa ta ishi Arhaan, yasan batayi abinci ba itama bataci ba, yoghurt yaje ya dauko da cookies a kitchen saida ya dawo falon kafin idanunshi suka sauka a kanta. Sanyin falon yasa ta kudundune da hijab dinta sai ajiyar zuciya take. Yayiwa kanshi alkawari, dan haka kashe mata wutace da tv din yayi ya rage sanyin ac kafin ya wuce dakinshi ba tare da kara kallon koda inda take ba, dukda kuwa cewar his heart wants him to.

Da asuba yazo zai fita ya ganta a yadda take, mamaki yake wai ya mutum zaiyi bacci a haka ba tare da ya farka ya gyara kwanciyarshi ba? Karasowa yayi inda take a zaune tana bacci ya dafa ta. Firgigit ta farka, sai a lokacin ya lura da kuka take can can ranta tana mafarki, "Kuyi hakuri, kar kuman!!!" Ba kasafai take mafarkin abunda ya faru da ita ba, amma yau tayi. Cikin wannan tsoron ta farka ga kuka, ganinta a haka yasa Arhaan ya durkuso saitinta.

Tana bude idanunta ta ganshi gab da ita sai tayi hugging dinshi ta fashe da wani kukan. "Arhaan kace su daina, kace kar sumin, akwai zafi kuma sunada yawa. Arhaan zaka saka a kamasu ko? Yadda bazasu kara yiman ba, kuma sai su hana nayi kuka. Azzulumai ne bazan taba yafe masu ba." Yarinya ta dawo mashi, kuka take har cikin ranta ta kankameshi kamar shine rayuwarta. Tausayinta yaji ya shigeshi, baisan dalilin kukan nata ba ko mafarkin me tayi amma daga ganin yadda take acting innocently yasan abun ya taba zuciyarta da gaske.

A hankali yake patting batting in a soothing way "Yi shiru ki daina kuka kinji? Babu wanda zai miki wani abu, ai gani ko? Ya T ma yana nan bazasu miki komai ba kinji? Yi shiru."

Jin ya fadi sunan Ya T yasa tayi firgigi ta dago daga chest dinshi "Aaaa! Wallahi idan yaji kasheni zaiyi, dan Allah karka fada mashi. Inna kuwa tsineman zatayi, Arhaan banaso suji!" Shi abunda ya lura ma cikin magagin bacci take amma kuma abun comes from her heart. Daga gani wani babban abu ne ya faru da ita. Shi yasan idan abu yana hunting mutum a rayuwarshi yadda yake, sai ta kara bashi tausayi.

Hugging dinta yayi "To bazan fada masu ba, koma bacci kinji? Ina tare dake." Dan rocking dinsu ya fara a hankali har yaji sauyi daga yanayin saukar numfashinta wanda hakan yayi indicating mashi tayi bacci.

Daukarta yayi ya kaita bedroom dinshi, har ya juya zai fita ya lura hijab din ta takura mata, dawowa yayi ya cire mata hijab din kafin ya gyara mata kwanciya. Dan karamin peck ya mata saman forehead dinta, ya gyara mata gashin fuskanta kafin ya kashe wutan dakin ya fita, zuciyarshi fal da tunanin wannan wane irin mafarki ne tayi haka?!

Ya kukejin littafin? Inaso naji ra'ayoyin ku. Nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now