BABI NA HAMSIN DA BIYU

1.5K 247 32
                                    

Kwance take saman ottoman a kishingide, wani tsaddedden mocktail ne a hannunta, pool din dake view dinta ba karamin haduwa yayi ba, pool ne na daya daga cikin tsaddadun hotels din dake kasar cairo; kempinski nile hotel, garden city cairo. Idan kaga face dinta sai kayi tunanin babu wanda ya kaita farin ciki a rayuwarta, jeans da tshirt ne jikinta, sannan a kan dan table din kuma ta ninke kimono dinta ta ajiye domin tasha iska.

Pool din babu kowa cikinshi, ita kadai ce, ko dan dare ya tsala ne? Amma hakan ya hada da kasantuwar yau din friday ce, kuma babu ranar da takai friday night cikar clubbing. Tasan duk mazauna hotel din suna clubs. Wani nannauyan lumfashi ta sauke kafin tayi gulping down ragowar mocktail din nata.

Tunda tazo yau satinta daya kenan basuyi waya dashi ba, idan akwai abunda yafi auduga yamutsewa to kwakwalwarta ce. Wayarta ta ciro daga aljihun wandonta, tasan yayi mata kiran har ya gaji, dan kuma Maama saida ta tabbatar ta saka number dinshi a black list kafin tahowarta.

Unblocking tayi kafin tayi dialing number din, bata damu da time difference dinsu ba, ita kawai she needs someone to talk to. Wannan rayuwar ba irinta yakesan tayi ba. Of course she loves the luxury, yadda duk wani abu da bata taba mafarkin samu ba ta sameshi, yadda wai ita ce yau takeda makudan kudi a account dinta, amma kwata kwata she knows it isn't right, kawai batasan yadda zatayi bane ta daina. Kamar an saka karafu an tokare ta.

Can cikin tunaninta taji muryarshi kamar yana bacci, "Dan gayu," ta furta a hankali, ba zato sai taji saujar hawaye a kuncin ta. Inba kamar yau da Hajia da matayen banzanta sukaje can meeting dinsu ba, da yanzu bata samu time dinnan ba, tana can ana transferring dinta from one mace to the other. Tama rasa ina mijin yake, sai yanzu ta gane karya Maama tayi mata. Gaba daya kyamar kanta takeyi.

Jin sautin kukanta yana tashi ba karamin daga ma Saahir hankali yayi ba, zaune ya mike daga kwancen da yake, dama baccin ba dadi yake mashi. Ya rasa gane kan Maama, shi bai yarda da wannan yawace yawacen da Beeba takeyi ba. "Yar baka, meya faru?" Ya tambaya cike da kulawa da tausayi.

Cikin shashekar kuka ta fara magana, "Dan gayu na tsani rayuwa ta, banasan ta, kyamar kai na nakeyi. Nace ka rika man addua kana man?" Ta rasa yadda akayi indai tazo zata fada ma Saahir matsalarta to ba tabbas sai taji kamar an dasa mata wani dutse da throat dinta, wani kukan ta fashe dashi.

Cike da kulawa ya fara magana, "Yar baka ki natsu kiyi mani bayani. Gidan ne bakiso? Ba Maama tace two weeks zakiyi ba? Saura week daya ai ko? Menene na kukan kuma? Kodai babu yan gayu a nan ne kuma kinyi missing dan gayun ki?" Ya fada da tone din zolaya, haka kawai ta tsinci kanta da fashewa da dariya ga hawaye kuma a cheeks dinta.

"Kamar ka sani fah, I've been missing you kamar nayi tsuntsuwa. Abincin nan ko na girka babu dadi, idan naci wanda akayi ma ba dadi, nakan nan dai." Hawayenta take gogewa a hankali, murmushi kuma yana maye gurbin su. Ta rasa wane irin matsayi ne tattare da Saahir a rayuwarta, duk yawan damuwar da take ciki in har ta kirashi to tabbas sai ta yaye.

"To zan girka na kawo maki. Ni kuma kinsan me nake missing nake? Wannan sanyin halin naki, your voice, your laughter, ke idan na fara maki listing sai kiyi tunanin na fada kogi ne banda igiyar fitowa, ni kuma har yanzu ina bakin gaba." Ba yau suka fara wasan nan ba, shi bai yarda ya fada ba, ita kuma idan ta dage akan ya fada sai yace bil hakki yana gabar kogin, tukunna dai. Ta rika janshi akan gara tun yanzu ya fada fah, inba haka ba kafin taje siyo igiyar da zata ciroshi dashi kila yayi drowning ciki.

A haka cikin nishadi suka cigaba da wayar su, tayi dariyar data dade batayi irinta ba. Ita kam Saahir shine uwarta da ubanta, komai ya mata.

A hankali ta fara bude idanunta, amma irin tsoron daya darsu a ranta ne ya mata tuni da irin mafarkin data kwana tanayi. Wani irin mugun firgita tayi, dan ita bawai gado ta gani ba, dajin da suka kaita ta gani. Juye juye ta farayi cikin dakin ta kama gown dinta kam, sai matse jikinta take ga hawaye kuma.

Fitowar Arhaan kenan daga toilet yayi wanka, tunaninshi har ya gama shiryawa bata tashi ba, ganin tana juye juye yasa duk yaji ya tsume a inda yake. Sai daga baya ya fuskanci kuka take kuma daga gani a rude take. Mantawa yayi da towel din jikinshi ya tunkari inda take, ai tana ganinshi ta fasa wani irin ihu tana jan baya.

Ita ba Arhaan ta gani ba, dan har ga Allah gani tayi ya koma mata mutum hudu, baya baya take tana girgiza kai kamar ranta ya fita. Karasowa yayi har inda take, mutuwar tsaye tayi, har saida yakai hannu ya dafa shoulder dinta cikin kwanciyar hankali "Calm down, Sakinah. Ni ne, Arhaan ne."

Kallonshi ta tsayayi sototo sai daga baya ta kusan five minutes kafin ta sauke numfashi wasu sabbin hawayen na bin idanunta. Durkushewa tayi a inda take tana dizgar kuka. Ita kadai tasan irin illar da abun nan yayi mata, gaba daya tana yawo ne amma yadda wuta kecin daji haka abun yake cin ranta. Gani take kowa ma cutar da ita zaiyi ya rabata da martabar ta, wace martaba ma tayi saura? Sai ta kara fashewa ta kuka.

Ganin Arhaan ya shiga walk in closet dinshi da niyyar saka kaya sai taji ta bawa kanta tausayi, tasan dole wata rana koda ba santa yake ba ya bukaci hakkinshi, tunda shi dai ba dutse bane, yanzu me zata fada mashi idan ranar tazo? Zata ce mashi she's not a virgin ne ta jira duk wulakancin da zaiyi mata ko kuma kafin ranar zata fada mashi da bakinta? Zai taba yarda da ita kuwa? Tunda dai yanzu ya goga ma duk wata mace bakin fenti?

Tana cikin wannan tunanin Arhaan ya iske ta a inda ya barta, iya kyau yayi kyau kamar ta kulleshi a daki taita kallonshi. "Sakinah me yake damunki?" Cikin lallashi yayi maganar yana kallon kwayar idanunta da take cike da fargaba, tsoro, da kuma tausayin kanta.

"Arhaan ka kaini wajen Mama." Abunda ta iya furtawa kenan, she needs to see Mama, ita kadai ta san matsalarta. Idan irin wannan matsalar ta samu mace mahaifiyarta take nema, to ita tata bata da maraba da matatta. Ko kadan ba zata taba saurarar ta ba.

Mikewa tsaye yayi, "To tashi ki shirya muje, ko sai kinci abinci?" Saurin girgiza mashi kai tayi tana me fita daga dakin, har kusan tuntube tayi. Arhaan kallon bayanta yayi har ta bace ma idanunshi, yasan ko me yake damunta ba karamin abu bane, yana da tabbacin wani babban alamari ne ya faru da rayuwarta.

In less than twenty minutes Sakinah ta gama shiryawa. Wata black jallabiya ta saka irin me zip dinnan ta gefe, tayi mata kyau sosai tayi rolling da gyalen. Ko kwalli bata saka ma eyes dinta ba, amma tunowa da ba Mama kadai bace cikin gidan yasa ta saka kwalli da dan lip balm kafin ta dauko wayarta ta nufi part dinshi.

Tana shiga ta iske zaune yana latsa wayarshi, ta kusa five minutes a wajen ko dagowa baiyi ya kalleta ba, can dai ta gaji da tsayuwa tace "Arhaan muje." Ya lura bata magana daya batace Arhaan, no one is fond of his name like she is.

Baice uffan ba ya mike suka fita tare, tunda aka kawota sai yau zata fara fita, cikin gari babu mai cewa kowa komai, titi kawai take kallo da kayatattun gine ginen dake cikin garin Abuja. She was truly amazed. Suna isa gidan aka bude masu gate, har suka isa parking lot din part din Mama babu wanda ya tanka ma wani.

Fitowa tayi ta tsaya, dan yanzu bata iya cewa ga inda mutum zaibi a cikin gidansu, dama zuwanta daya. Kamar a mafarki tayi ya riko left hannunta da right one dinshi, wani irin zaaam sukaji. A tare suka dago suka kalli juna kafin kowa ya dauke idanunshi. Al'adar shi ce duk saurin da yake idan har yazo gida dole ya shiga ya fara gaida Mommy kafin yaje wajen Mama, part dinta suka nufa with their hands entwined.

Suna shiga falon Mommy suka iske Sisters dinshi suna kallon maimaicin Mahek a zee world, gaidashi sukayi kafin suka gaisa da Sakinah, ita kam kasa amsawa tayi dan duk sun girme ta saidai ta mayar masu da gaisuwar su. Dakin Mommy ya wuce direct tana zaune tana ninke hijabs dinta.

Da hanzari Sakinah ta karasa wajenta ta karbi ninkin ta farayi, "Oh ni diyar su, Allah yayi Arhaan da yar banzar kyuiya yau ga matar shi mai son aiki. Nagode kinji Sakinah? Allah yashi albarka, nanda wata tara muzo wankan jariri." Ita da tayi maganar bataji komai ba, amma su a tare suka kalli juna. Ana aure ne dan a hayayyafa ko? To su are they even ready for that?

Naga comments dinku nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now