BABI NA ASHIRIN DA UKU

1.6K 258 47
                                    

Fitowa sukayi daga office din doctor din kowa yayi jugum banda Sakinah da har cikin ranta wani irin dadi ne male male. Taso ace ma ya karye yadda zaisha zama a asibiti ko kan kujera. Suna nan zaune wata nurse ta karaso wajensu hade da fada masu cewar zasu iya shiga dakin da Arhaan din yake dan komai is set.

Dogon numfashi taja kafin tabi bayan Aunty Halima da har yanzu kuka take, ita batasan me zata fadawa Mama ba idan tazo. Baban Shaheed ya fara shiga dakin kafin Aunty Halima sai kuma Sakinah da saida ta dauki yan mintoci kafin ta murda marfin kofar ta shiga.

Tana shiga idanuwanshi ya sauke a kanta, there was something on her face he couldn't decipher, something like truimp and excitement. Fuskarshi datasha dauri da bandage ta kalla, dakyar ta danne dariyarta ta samu waje a kasan carpet din ta zauna kafin ta kara daga fuskarta, "Sannu, Ya jiki? Allah ya kara sauki." Abunda ta fada kenan ta dukar da kanta, shima din dan kar su Aunty Halima suyi suspecting wani abu ne.

Aunty Halima kuwa zama tayi kusa dashi bisa kujera, dan hannun da baisha azabar ba ta rike tana ta shan kukanta, "Dan Allah Maman Shaheed ki daina kuka, can't you see da raina bawai na mutu bane?" Dakyar yake magana kamar numfashinshi zai fita, dan shi bacin ganin idon Sakinah da shima kukan zai rizga har sai ya gode Allah.

"Yanzu Arhaan ya kakeji? Wai ni me ka masu ne? Gashi Mama nasan ta kusa isowa me zance mata?" Aunty Halima whimpered, hawaye ne kawai ke zarya saman kuncinta-dan harga Allah abun nan ba karamin dakar mata zuciya yayi ba.

"Zan mata magana da kaina idan tazo, and wallahi ni ko ganinsu ma ban taba yi ba sai yau-kawai zalinci ne irin na yan daba." Yana furta haka bai kara cewa komai ba ya lefa saman pillow dinshi yana sauke numfashi dakyar, dan shi kadai yasan azabar da yakeji, cikinshi kuwa har yanzu kamar an hura balloon.

Suna zaune, Aunty Halima ta daina kukan saidai ajiyar zuciya, Baban Shaheed kuwa ya tafi gida saboda yara da suke islamiyya, dukda dai akwai makwabtan da har kwana zasu iyayi a gidansu amma shi sam bai yarda yaranshi su rab'i wani ba kamar yadda bayasan a rabeshi.

Jungum suke zaune, Sakinah saidai ta kitsa wancan ta kwance wannnan. Can sukaji anyi sallama an shigo dakin a hargitse, kallo daya Aunty Halima ta mata ta kara fashewa da wani kukan, "Wallahi Mama da nasan hakan zata faru bazan bari ya fita ba, dan Allah kiyi hakuri." Tasan halin Mama sarai saboda Arhaan sai tayi mata tas wajen nan, and that's the last thing she wants to happen.

A hankali taji Mama ta rungumeta itama kukan take kamar an aiko masu cewar Arhaan din ya rasu. "Ba laifinki bane, Halima-haka Allah ha kaddara, ki daina kukan nan haka dan Allah." Patting bayanta ta rikayi har kukanta ya tsagaita kafin ta taka a hankali ta nufi inda Arhaan yake kwance alamun bacci ma ya daukeshi.

Zama tayi kan kujerar dake kallonshi kawai ta kura ma yadda ya koma ido, bandage ko ina a jikinshi. Ganin ta dan natsu yasa Sakinah ta muskuta a hankali jikinta babu inda baya rawa, dan ita gani take tabbas matar nan sai ta gane itace silar jefa danta cikin wannan halin.

"Mama ina wuni?" Ta furta murya na rawa kamar zuciyarta zata fiti daga kirjinta. Kamannin Arhaan take gani sak shimfide saman fuskar wannan kwakkyawar matar, saidai ya fita haske.

"Lafiya kalau yarinya. Halima wannan fah?" Mama ta amsa tana directing question dinta to Aunty Halima. Dan yadda Sakinar ta rukube fuskarta tayi jugum jugum ya nuna tabbas ta damu da halin da Arhaan yake ciki.

"Itace me mani aiki Mama," Aunty Halima ta amsa tana kallon wajen Sakinar, yadda ta rakube waje daya ya nuna tabbas abunda ya samu Arhaan din ya dameta-nan kuwa basusan tsoron a kamata take ba.

***

Hajia ce ta jefa ma Hajia Hauwa da wani kallon tuhuma, haka kawai all of a sudden zatazo tace tanasan Beeba a matsayin yar aiki? There has to be something fishy. To kodai Beeba din ta fada mata wani abu ne? But that would never happen, dan kuwa sun riga da sun rufe mata baki sun kuma goge mata kwakwalwa bata iya tuna kowa nata. But idan ace hakan ce ta faru, lallai kuwa yarinya takai kuka gidan mutuwa.

"Hajia ya naga kinyi shiru kina jifana da wani kallon tuhuma ne? Kodai akwai matsala ne idan hakan ta faru?" Hajia Hauwa ta tambaya, feeling so veey uncomfortable da irin kallon da hajiar ke mata, dan ita baccin ta daukar ma Saheer alkawarin bazata fadawa Hajiar manufarsu ba da tuni ta fada.

"Aa Hajia babu komai. Kawai ina mamaki ne, ganin yadda bakisan ko maganar me aiki a maki." Hajia ta kare kanta tana wayencewa da duk wani tunani dake ranta.

"Kinsan dama duk aikin gidan Saheer ke yinsu kafin ya tafi office, abincin ma na safe shi yakeyi, na rana kuma yana office yaci, da dare idan ya dawo yayi, idan kuma ya gaji sai kiga ya mana order_tunda nayi nayi ya bari ko girkin in rikayi amma baya yarda. To yanzu dai dakyar na samu na shawo kanshi ya yarda, shine nikuma naga tanada hankali dai nace bari na maki magana."

"Ah to indai hakane babu wani abu, bari yanzu na mata magana sai ta shirya ku tafi ko? Amma kinsan dai sai kin bada wani abu ko? Gwamnati ta hana aikin banza," hajia ta furta hade da wata shewa irin tasu ta yan duniya kafin ta shige cikin gidan domin kiran Beeba dake dakinta tana jiran tsammani-dan Saheer ya mata alkawarin duk ranar dataga ya dawo to da ita zai bar gidan.

Hajiar ce ta shigo da dan fleeting smile dinta tana kallonta, "Sannu ko Habiba? Ki tashi ga Hajia can tazo da bukatar tanasan ki mata aiki to na amince, zaki bita yanzu, ina fatan babu matsala dai?" Ta tambaya tana zama saman edge din gadon, dan kuwa ta lura da Habibar kamar zata danyi taurin kai.

"Babu komai Hajia, kece uwata kece ubana, duk abunda kikace shi zanyi." Har wasu hawayen farin ciki saida suka zubo mata, dan yau zatayi bacci cikin kwanciyar hankali babu fargaban zuwan Ramcy dakinta.

Kayanta ta tashi ta hada tsaf, dama bawai a watse suke ba kafin ta fito hajia rike da hannunta har suka karasa falon. Gaida Maaman Saheer tayi kan ta fita waje da ghana must go din kayanta daga nan su kuma Maman Saheer ta Sallami Hajia ta fito suka kama hanya-zuciyar Saheer fes, dan yau ya cika alkawarin da ya daukar wa Yar baka.

***

Cikin bacci yake jiyo murya kamar ta Mamanshi, a hankali dai ya fara squinting eyes dinshi with so much pain har ya saukesu akan idanuwanta data kafeshi dasu. Mantawa yayi da ciwon dake cin jikinshi ya yunkura cike da farin ciki-amma azabar ciwo ta dakatar dashi dole ya koma ya kwanta.

Kanshi Mama tayi tana faman jera mashi sannu, ai Arhaan baisan sanda ya saki kuka kamar dan karamin yaron daya fadi yaki kuka saida yaga mahaifiyarshi. Rungumeshi tsam tayi a jikinta yana ta dizgar kuka kamar an aiko mashi mutuwa.

Sakinah kuwa dama abunda take jira ta gani kenan-kukanshi. Burinta ya cika tunda har shima yayi kukan daya saka tayi. Kanta ta cusa cikin kafafunta kamar mai kuka nan kuwa dariya take har jikinta na rawa_su kuma su Aunty Halima sunyi tunanin kukan Arhaan dinne ya bata tausayi.

"Ki daina kuka kinji Sakinah, zai tashi ai ba wani abu bane, haka yake indai yana tare da Mama." Aunty Halima ta dafo kafadarta harda squeezing lightly irin ta lallasheta dinnan. Ai dan dole Sakina ta kakulo kukan karya dan karsu gane abunda ake ciki-dagowa tayi shar da hawaye, shi kuma lokacin ya tsagaita kukanshi sai idanunsu ya hadu_shidai yasan wannan yarinyar bazata taba mashi kuka ba, tabbas something is fishy.

"Allah sarki Sakinah kiyi shiru kinji? Kaga Arhaan ka ruda yar mutane tayi tunanin duk zafin ciwon ne ya sakaka kuka. Lallasarta Halima." Mama ce ke magana cike da kulawa, haka kawai yadda Sakinar ta nuna ta damu da lafiyar Arhaan yasa taji tana kaunarta-ita kuwa Sakinah mamakin wadannan mutanen take, kila dai dabi'arsu ce ririta mutane.

Shiru sukayi su dukansu, Mama tana fada mashi yadda gaba daya gidan kowa ya rude yana kuka. Lokaci zuwa lokaci idanunsu sukan hadu saidai kowa ya dauke kai-dan kowa da abunda yake sakawa a ranshi.

Lokacin sallah nayi Mama da Aunty Halima suka mike a tare, sai kuma suka tsaya suna kallon Arhaan, ganin hesitation dinsu yasa Sakinah yin magana. "Auntynmu kuje kuyi salar ku dawo sai inje inyi, in yana bukatar wani abu sai in taimaka mashi."

Hakan da tayi ba karamin siye zuciyar Mama yayi ba, dama me san da, idan kana neman zuciyarshi to kaso danshi. Rungumeta Mama tayi, "Nagode maki sosai kinji? Allah ya baki miji nagari." Amin ta furta can kasan ranta kafin suka fita ta juyo da niyar sauke mashi ta cikinta.






Ya kukejin littafin?

Ku turawa kawaye da abokannan arzikinku dan suma suzo su karanta, inhar yana maku dadi.

Nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now