BABI NA HAMSIN DA BIYAR

1.8K 268 188
                                    

Asuba batayi ba Sakinah ta farka, babu zato ba tsanmani tajita tsamo tsamo cikin fitsari, wani irin duka da kirjinta yayi kai ka dauka ganga ce. Kallon gefenta tayi taga Arhaan sai baccin shi yake hankali kwance. Kawai daukewar rai haka ta fara bin gadon tana tabawa taji iyakar inda fitsari ya tsaya, Allah ya so ta baikai wajen Arhaan ba, amma tana taba hem din rigarshi taji shi a jika sharkaf.

Wani irin marayan kuka ne yazo mata, yanzu ita wannan wace irin rayuwa ce? She couldn't remember the last time she bed wet, ko dan bata baccin sosai ko yaushe cikin mafarki take tana farkawa? Shikenan yau dan taji full time bacci kuma sai yazo mata? Me yasa ita bazatayi rayuwa irin ta sauran matan ba? Yanzu fisabilillahi me yafi wannan kunya?

Kuka take ta hade kai da guiwa, tunowa da abunda Arhaan ya mata a ranar daya gane tana fitsari tayi, wannan a hakan tana gidan yayarshi, a dakin daya kasance tamkar nata, babu abunda ya hadasu, ya mata haka balle yanzu? Yanzu da yake mijinta, sunyi fadan har sun shirya yanzu kuma ta kwana a dakinshi, ta rasa inda zatayi fitsari sai kan gadon mijinta? Wannan wace irin rayuwa ce?

Kamar a mafarki Arhaan yaji sautin kuka yana fita a hankali, irin kukan nan da maraya yakeyi kullum cikin dare ba tare daya bari sauran mutanen da suke tare dashi sunji ba, dan ko sunji babu wanda zai fahimci halin da zuciyarshi yake ciki. Irin kukan da mata takeyi a lokacin da ta rasa mijinta, ga wace macen ko kuma yabar duniyar gaba daya, irin feelings dinnan ko kayi voicing dinsu out babu wanda zai fahimta sai wanda ya taba dandana azaba da radadinsu.

A kasale ya fara bude idanunshi, dan juyin da zaiyi yaji gefen rigarshi a jike, mamaki ya kamashi, tar ya bude idanunshi ya saukesu akan Sakinah. Ta hade kai da guiwa tana kuka a zaune, irin kuka mai taba zuciya, alamar tana tausayin kanta da kuma halin da zata fada. Meya faru? Ko mafarkinnta karayi?

Yunkurowa yayi da niyar ya tambayeta abunda yake faruwa saidai yaji hannunshi cikin ruwa, hands dinshi yakai saitin hancinshi a nan ne ya fahimci fitsari tayi shine take wannan kukan kamar an fidda mata rai. Tausayinta yaji ya kamashi, dan shi har ga Allah yama manta tana fitsari, kuma yasan wannan kukan da take yana da nasaba da tsoron irin wulkancin dazai mata ne idan ya farka.

Dayan hannunshi yakai ya dafa shoulder dinta, a firgice ta dago daga duken da take saidai ta kasa kallonshi, kukanta kuma yayi intensifying. Ganin bazata juyo ta kalleshi ba yasa ya cire rigarshi dagashi sai vest ya barta a kan gadon kafin ya zagaya saitinta inda babu fitsarin ya zauna.

Ta dago face dinta kam, amma kuma eyes dinta a kulle suke gam, jikinta har wata irin rawa yakeyi tana jira taji ruwan masifar da zaiyi mata, amma batazo ba. Hannu yasa ya dago chin dinta yana karema jikakkiyar face dinta kallo, sai wani tausayin ya kara kamashi.

"Sakinah, kukan me kikeyi?" Abunda ya tambaya kenan cikin sauti mai kwantar da hankalin mai sauroro. Kamar ya tsaga chest dinshi ya sakata ciki yakeji, to hide her from all the evils of this world, all the pains and heart breaks. She looks so innocent he wants to shield her from all harm.

Shiru tayi ta kasa magana kuma har yanzu bata bude idanunta ba, despite her face held up by him. Tambayarta ya karayi, this time yana matsowa kusa da ita, blanket din ya saka saman fitsarin kawai ya zaune a wajen, dab da ita.

Numfashinta har wani seizing yake, tasan wannan mutuncin da yake mata dan baisan abunda tayi bane, may be yayi tunanin ko mafarki tayi halan?  "I...bed..w..e.." bai bari ta karasa ba yayi hugging dinta hade da patting bayanta cike da rarrashi.

"Shhh...it's fine kinji? It's my fault ban bari kinyi ba before ki kwanta right? And now I have to take the consequences. Yalla, tashi ki shiga kiyi wanka and I'll clear the bed kinji? Ki daina kuka sai kace ance maki na mutu kuma?" Breaking hug dinsu yayi yana clearing hawayen dake zarya non stop saman cheeks dinta.

A hankali ta fara bude idanunta kamar tana jin tsoro, saida ta budesu tar a kanshi ta tabbatar shi din daine kafin tayi magana, "Won't you insult me? Bazaka mun waka ba this time around?" So innocent tayi tambayar, still hawayenta basu daina zuba ba.

"How would I make fun of my wife? Idan bazamuyi dariya tare ba ai bazanyi miki ba ko? It isn't right, I'm a good man don't you see? Handsome and good, kin samu package me kyau yarinya." Har wani flipping hannayenshi yayi irin bai yadda ba dinnan, he's doing it just so she will free her mind if da chance ma har dariya tayi, and she chuckled softly.

For the first time in her life, Sakinah has someone apart from Beeba. Hugging Arhaan kawai ta karayi sai kuma ta fashe da kuka, "Thank you so much, Arhaan. You really are the best." Breaking hug dinsu tayi sai kuma ta rufe face dinta, dukda dai ya nuna mata it's fine amma still tana jin kunya.

"Tashi ki shiga toilet kiyi wanka, zan dauko maki all the necessities from your room. Ko so kike na rasa jam'i ne wai? Ke kuma ba sallar zakiyi ba balle muyi tare." Batayi tsanmani ba taji ya dagota with her hands har saida legs dinta suka sauka a kasa. Kasa moving kafanta tayi saboda yadda leggings din ya kama jikinta yanzu, sai kawai ta tsaya tana kallonshi.

"Before I count to three, if ba haka ba Sakinah da kaina zan miki wankan nan. 1...2...3..." bai ida rufe baki ba ta zambada da gudu bata tsaya ko ina ba sai toilet dinshi, saida ta rufe kafin hankalinta ya kwanta.

Amma instead ta fara wankan sai da ta tsaya ta dirji kukanta san ranta, bata taba tsanmanin Arhaan can be this caring be, he really is a gentle man. Abunda ya mata yau has touched her heart sosai kuma she felt loved all over.

Saidai ya gama gyara dakin yakai bedsheet da blanket din laundry, mattress din kuma ya bude windows tare da kara fan sannan ya wuce toilet dinta ya dauko mata duk abunda zata bukata da yar doguwar riga. Kayanshi ya dauka ya tafi spare room din dake part dinshi domin yayi wanka daga nan ya wuce masallaci.

Koda Sakinah ta fito ta gama shiryawa tsaf bata ganshi ba, saida ya dawo sallah ya ganta zauna saman sofa tana tunani. Zama yayi gefenta hade da rike hands dinta yana murmushi "Sakinar Mama, zaki araman gadonki nayi baccin safe yau?" Kunya ma ya bata, ta rufe eyes dinta. Dariya kawai yayi yaja hannunta zuwa dakinta, anan sukayi baccin safensu. She had never bed wet and felt this free and almost happy ba sai yau. He is a blessing to her.

Kafin Mama ta tafi saida sukaje suka mata sallama, yau Sakinah sai yan aikace aikace take tana ma Mama snacks dan yau ne ranar dawowar ta, itama yau tayi wanka, ta shirya tsaf dan taje ta karbo magunguna wajen Mama kuma su mata sannu da zuwa.

Throughout days din datayi spending da Arhaan, he had been the sweetest man she had ever known. Dan wani lokacin saidai ta tsaya taita kallonshi har sai ya mata waving, idan ya tambayeta kallon da take mishi kuma sai tace "So nake naga ko face mask ko saka, anya kuwa Arhaan kai ne?" Saidai yayi dariya, dan shi kanshi yana mamakin kanshi.

Kuma tun daga ranar da tayi fitsari a dakinshi da dare yayi yake monitoring shan ruwanta kuma duk bala'i ko ta fara bacci haka zai dauketa ya kaita toilet tayi fitsari har ta saba. Kuma basa bacci babu karatun kur'ani hade da addua a jikinsu, yace mata a girmanta kodai internal problem yake sakata ko kuma sharri ne na shaiduna. Kuma daga ranar bata kara ba. She feels so lucky to have him in her life.

Yamma tayi sosai, tunani take wai kam ina Arhaan ya shiga daga siyo coconut? Batayi aune ba taji anyi hugging dinta ta baya hade da daura kanshi saman neck dinta. Murmushi tayi ta dafo kanshi, planting him a rough peck on his forehead.

"Arhaan din Mama duk murnar dawowar Mamar ce? Nikam ka siyo mun coconut din?" Ta tambaya tana san ta juyo su fuskanci juna amma sai yayi wrapping hands dinshi around her waist.

"Aa, nikam murnata ta daban ce. Yes na siyo tana fridge, naga aiki ya miki yawa, what can I help with? Farin ciki yamun yawa yau dinnan." Ta gano abunda yake nufi, tunda yaga tayi sallar azahar ya isheta da abubuwa, duk da dai she's afraid, but itama she can't wait.

Kafin ta bashi amsa wayarshi tayi ringing, da kamar bazai dauka ba kuma yayi picking ganin Safiyya ce, wani irin gunjin kuja yaji ta saki ga kuma kururuwar mutane da background din da take, bai tambayeta komai ba yaji ta furta "Ya Arhaan...Mamaa...."



Toohhh bismillahi

Nasan zansha complain, amma haka labari yazo saidai kuyi hakuri

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now