BABI NA HAMSIN DA TAKWAS

1.8K 266 66
                                    

This page is for you, Sadeeya Aliyu Batsari, my favorite girl. Fave reader din Sakinah da Arhaan, we love you loads.

Satika sun tafi, tun su Sakinah suna zama gidan Mama har suka koma gidansu, it has been three weeks straight gashi Baba ya barwa Arhaan alhakin juya business dinshi. Kwata kwata ma ba zama gida yake ba, kuma idan ya dawo kullum duk dare sai yasha kuka ya gode Allah. Wani time din ma sai Sakinah ta fara bacci zataji shashekar kukanshi a bayanta, haka zatayi ta lallashinshi, wani time din yayi shiru wani time din kuma sai itama ta fara kukan kafin yayi shiru. Gaba daya ya koma wani sabon Arhaan, dan ko Arhaan din data fara sani yafi wannan san magana, san mutane da human relation. Arhaan din yanzu sai tayi magana tafi dari amma bazai kulata ba.

Gashi kullum idan ya kira Baba ya rokeshi akan suyi video call ya nuna mashi face din Mama sai yaki yarda wai ya zama namiji, kuma idan yace zaije cairo sai yace bai yarda ba. Kwana uku da suka wuce Sakinah ta fara lura da yanayinshi ya kara chanzawa, gaba daya kamar bashi ba, ga wani mugun bacci kamar mai yaron ciki. Idan ya dawo sometimes a falo yake zube mata sai dakyar yake tashi ya shiga daki.

Yau kam abun yafi na kullum, har 11 bai dawo ba, tsaye take cikin falon part dinshi, sai ta kalli agogo sai ta kalli kofa, Arhaan idan yayi nisa a waje to 10 ne, amma yanzu 11 din ma nema take ta wuce 12 tazo. Bataso tunanin da takeyi a kanshi ya zama gaskia, bataso abubuwan da take gani akanshi ya zama gaskia, tasan symptoms, tasan signs din, tasan how they act, duk babu abunda bata gani ba tun tana yarinya.

"Ya Allah banda Arhaan." Abunda ta fada kenan, wani siririn hawaye na biyowa saman cheeks dinta. Itace ta zauna, ta tashi, ta shiga daki, ta fito, amma duk Arhaan bai dawo ba. Sai can wajen 12:47am taji an banko kofa, tankadi yake kamar zai fadi, dama kusan haka yake dawo mata. Ga robar coke a hannunshi, wanda duk bala'in Sakinah bai bari ta karbeta daga hannunshi.

Cike da fushi ta karasa inda yake, kafin yayi wani yunkuri har ta fizge robar coke din ta bude ta, hancinta takai ta sinsina sai kawai ta saki robar ta fadi a kasa, supposed drink din kuma ya zube saman carpet. Kafin kyaftawa da bismillah hawaye sun fara zarya saman cheeks din Sakinah. Wani irin kuka ta saki tana furta "Noo!" Har can kasan ranta. Baya baya takeyi tana kuka tana girgiza kai. Duk wani salo irin nasu babu wanda bata gani ba kuma bataji ba.

Tasan kamshin abunda ya saka cikin drink dinshi a wajen Ya T, tun kafin ya giga ya zama dan daba. Duk halayyar da Arhaan ya fara nunawa saida yayi haka. Tunma yana kwana gidansu, bai dawowa sai can dare. Yazo kullum yana tare da robar drink, ranar tsautsayi ya kaita ta shanye mashi drink aikau ta kwana ta yini tana bacci, nan ne asirin shi ya tonu, daga nan kuma sai ma ya xaina boye cewar yana shaye shaye. Har ta mutu bazata taba manta yadda kamshin abun nan yake ba.

"How can you do this to me?! To Mama?! Me ka rasa, Arhaan? Wannan wace irin rayuwa ce?!!!" Kuka take can can karfinta, kamar ta fasa kirjinta ta fiddo zuciyarta ko zatayi mata sanyi. Yanzu ita wa zata fada mawa? Gashi practically za'a iya cewa babu Mama, gashi last week Aunty Halima da family dinta suka koma Sudan inda mijinta ya tafi yin course din 3 years a can, ita batasan yanayin zamansu da Mommy balle, tunda baka shaidar mutum ta fuska wannan zamani. Infact wa zata tara ta fara fada mawa cewar Arhaan, mijinta, wanda take so da kauna ya fara shaye shaye?!

Tangal tangal yayi yazo inda take sai tayi baya, "Karka kuskura ka taba ni, Arhaan ni nasan ko friends baka dasu, waya jefaka wannan harkan, Arhaan? Nasan yanzu ko kayi magana duk karya ce, innalillahi!" Tama rasa abunyi, ta kama wancan ta saki wancan. Abunda bata sani ba shine, circle din su Arhaan su uku ne, kuma cikinsu shi kadai ne natsatse, sauran biyun dukansu yaran ministers ne, karatun ma koda sukaje an rarraka anyi ne bawai dan anaso ba. Babu irin abunda bai sani ba game da shaye shaye, dan wani time din tare zasuje wajen saidai ya fiddo waya yana game ko wani abu su kuma suyi tatul abunsu sai shine zaiyi driving dinsu back home.

Yanzu kuwa da damuwa ta mishi kamun kunzugu, baida wanda zai fada mawa sai su, dama tunda suka dawo Nigeria sai ya zare kanshi daga jikinsu dan yasan for sure Mama will be disappointed in him idan taga kalar friends din da yayi a school. Yanzu kuwa da baida wanda zai fadama matsalarshi dole ya nemesu su kuma suka dorashi a hanya, ranar farkon kasa ko bude idonshi yayi dole sukama Sakinah text akan zai kwana gidan Mama. Daga haka har ya fara sabawa, yanzu bai wani cika zama yayi tunanin Mama ba, amma duk dare sai yayi kuka. Kuma da rana in har yana cikin hayyacinshi sai yaita tunanin abun dayake aikatawa yanajin tsanar kanshi amma bazai iya dainawa ba. Ba Mama, me ya rage a rayuwarshi? Fuskarta ma Baba ya hana ya gani.

Zai fada kan kujera tayi hanzarin riko rigarshi, "Muje daki ka kwanta, dan Allah Arhaan." Kallonta kawai yakeyi kamar wani sakarai, shi baiga dalilin kukanta ba, to me ya faru ne? Shi ya kamata ai yayi kuka tunda ta zubda mashi drink dinshi amma baida energy din yin hakan. Hannunshi ta kama, ga hawaye ga wani tukar bakin ciki dake cizon ranta, har daki ta kaishi ya kwanta.

Socks dinshi ta cire mashi da takalmi ta kaisu mazaunin su kafin ta dawo tana kallon fuskarshi tana hawaye, kuka irin mai cin zuciyar mai sauraro, shikam barcinshi yake hankali kwance. Yau ko kukan daren baiyi ba tsabar yadda ya bugu. Kanta saman chest dinshi haka tayi bacci, kuka kuwa babu irin wanda Sakinah batayi ba, sai yanzu take kara kewar Mama.

Sai can har an gama salla kafin Arhaan ya fara bude ido, tun kafin ya sauko daga kan gadon ya bude bed side drawer dinshi ya dauko aspirin yasha dan yadda kanshi yake ciwo kamar me. Mikewa yaso yi sai yaji Sakinah saman chest dinshi, wani irin muguwar faduwa gabanshi yayi. In ba Sakinah na cikin damuwa ba bata taba dora kanta saman chest dinshi. Meya faru? Ko ta kara mafarkin nan nata ne?

A hankali ya dora hannunshi saman shoulder dinta yayi tapping, koda Sakinah ta bude ido taga yana kallonta da curious eyes tasan dalili, ko kallonshi bata karayi ba ta sauka daga gadon gaba daya ta fita daga dakin. Wanka yayi yayi sallah kafin yaga har time din bata dawo da custard din data saba hada mishi ba in her words, tace baya cin abinci sosai gara ya rika cin pre breakfast. Yayi zaman kusan thirty minutes amma shiru, ya fito part dinta amma babu alamar tana kitchen tana hada breakfast ba dukda dai yau weekends amma bata wasa da girki dukda ba wani ci yakeyi ba sosai.

Dakinta ya shiga ya ganta rakube akan gado sai kuka take kamar ranta zai fita, at first wani irin mugun bugawa kirjinshi ya mishi, dan tunani yayi kodai Mama ce ta rasu baa fada mashi ba ita kuma Sakinah bazata iya fada mashi ba? Sai dayaga kwata kwata kukan nata ba wajen yabi ba, kuka take tana magana kamar ranta zai fita. Sam bata lura da shigowarshi ba.

"Why Arhaan? Meyasa zaka maido man da unwanted feelings dinnan a rayuwata? First time da muka gane Ya T yana shaye shaye kamar na dauki wuka na caka ma zuciyata kowa ya huta, he was my favorite, har yanzu ina sanshi amma ko kadan bana respecting dinshi, yayi loosing wannan respect din. I had to walk into the harassment a unguwar mu, kullum mu ake zagi ana nunawa cewar mune kannen wannan me shaye shayen, ko aikenmu akayi gidaje sai iyaye su fara boye yaransu wai kar mu bata masu su. Tun Inna tana aikenmu har ta daina, saboda kullum cikin kuka muke dawowa. Banda kawa ko daya, saboda who would befriend kanwar mashayi? Kawata itace yaruwata, yanzu da nake tunanin na wuce wannan phase din shine zaka maida ni ruwa tsundum? Ya zaka man haka? Indai muna tare dole wataran zamu haihu, me kakeso na fada wa yarana a kanka? Cewar mahaifinsu bai daukar kaddara ko yana da raunin imani akan abunda ya sameshi? Idan bakayi tunanin abunda zanji ba baka tunanin kannenka idan yaran kana ganin yanzu baka dasu? Oh Mama, ko baki fada ba nasan kinbar amanar Arhaan dinki a hannu na, Mama I've failed you...Arhaan dinki is into drugs..." bata idasa ba taji an rufe mata baki da hannu, fargaba da tsoro ne kwance kan fuskarshi, girgiza mata kai yayi yadda kasan a gaban Mamar suke bayaso ta fada mata. Sai yanzu ya lura da baiga bottle dinshi ba wadda kullum sai ya boye ta kafin yake bacci. Yanzu me zai fada wa Sakinah? Yasan dai bai isa ya mata karyar cewa Aa bane, dan duk wani abu na wanda yake shaye shaye ta sani. Ina mafita?

Thank you for reading.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now