BABI NA ARBA'IN DA BIYAR

1.6K 221 21
                                    

Zaune suke a garden din gidan, kowacce daga cikinsu tayi shiga irin ta alfarma mai kuma fidda tsiraici daidai misali, ita kadai ce cikin shigar kamala dan har yanzu ita bawai ta sake bane da wannan harkar tasu marar kan gado da dadin yi ba. Da wani mayen kallo Maama ta bita dashi kafin ta maida idanunta kan yar aiken, "Kice nace babu damuwa, zata taho din kamar yadda aka bukata." Sallama sukayi da matar kafin ta ajiye mata bandir din yan 500 masu yawa kafin ta tafi.

Matsawa tayi kusa da Habibah ta zauna tana me kayata murmushin ta, "Haba my Beeba, yanzu kuma miye na damun kanki. Duka duka fah two weeks zakiyi a cairo ki dawo. Wata matar minister ce ta ga picture dinki danayi posting shine fa tace a aika mata dake sunje yawan shakatawa da maigidan ta, menene na damuwa kuma?" Cikin salo na batanci haka take magana tana kuma kara kashema Beeba da jiki.

"Ni banace banaso naje bane, kawai exams din danake yi nake tunani, ya zanyi da ita?" Ta tambaya tana kara tsunduma cikin kogon tunani, wai yanzu har takai lokacin da za'a fara safara da ita kasa kasa yawon madigo? Tasan wannan abun da sukeyi bawai abu bane mai kyau, duka cikin last month taje gari yafi biyar. Taje Abuja, Kano, Taraba, Sokoto, Adamawa, hatta Lagos saida taje, yanzu wannan hanyar tana bullewa kuwa? Ta tambayi kanta kafin ta jiyo saukar hannun Maama a inda dan dole ta dago ta kalleta eyes dinta har sun fara chanzawa.

"Muje daga ciki my Beeba." A rungume jikin juna haka suka karasa cikin dakin Maama suka danna ma kofar key, cikin watsuwar su saida Maama tasan yadda tayi ta shawo kan Beeba har ta amince zata tafi Cairo jibi, exams dinta kuma Maama ce zata biya a ida rubuta mata. Dan tun lokacin da aka fara registration na waec Sahir ya mata itama dan kuwa batasan inda nata yake ba, ko ma ta sani yasan bawai taci bane.

Da daddare Maama taje gidan kawarta, daga Sahir sai Beeba cikin palor suna fira kadan kadan, ita dai jinshi kawi takeyi, amma sam hankalinta yaki kwanciya, bataso tayi ma kanta sabo da wannan dabi'ar da babu inda zata kaita sai hanyar dana sani. Kuma a ranta tanaji kamar idan akace an rabata da wannan dabi'ar to tabbas ranta zai iya tafiya ya barta. Amma can kasan ranta tasan barin harkar is the right thing to do.

"Yar baka, wai meke damunki ne? Are you sure you're fine?" He had been asking her about her wellbeing tun lokacin daya ganta da daren yasan she isn't well but she keeps denying.

"I'm fine, Dan gayu. Just keep praying for me, kana man addu'ar dai ko? Please?" Rau rau tayi da ido, da tana iyawa data fada mashi matsalarta. Rarrashinta ya cigaba daya har ta samu natsuwarta ta dawo mata. Jibin kuwa haka jirgi ya lula da Beeba kasar Cairo, wanda Maama tace ma Sahir zataje gidan wata friend dinta ne ta lurar mata da yaranta zasuyi tafiyar two weeks, ko garuruwan da suka tafi duk karairayi ta rika mashi domin kar ya gane.


Kamar yadda yayi alkawari, five minutes na cika haka yayi kokarin mikewa itama kuwa tayi zumbur ta tashi, cikin rudu ko kallonshi batayi ba ta wuce direct dakinta ta danna key ta fada toilet domin yin wanka. Ko da ta fito wankan saida ta baci lokaci san ranta kafin ta saka kaya ta gabatar da sallar. Har kasan ranta yunwa takeji amma tsoro da kunyar Arhaan sun hanata ta fita, can dai da taga abun ba nayi bane dan dole ta mike ta fice daga dakin ai kuwa ta ganshi falon yana kallo.

Yana jin motsin fitowarta yayi saurin kashe tv din, and Sakinah what he meant by stopping her from watching tv, duk a cikin muguntar ne? Tayi tsaye tana kallon shi batayi aune ba ta tsinkayi wata irin kakkausar karar da dan dole ta rufe kunnuwanta.

"Da kika tsaya kina kallona maida ni ciki zakiyi ki sake haifa ta? Malama zaki daina kallo na ko kuwa?!" Tsoron daga idanunta takeyi, ita dai abubuwanshi sun fara bata tsoro ma, yanzu yanzu he's soft and the next minute yafi dutse wuyar fasawa.

Dining table din ya karasa ya barta nan tsaye, fuskarshi murtuk kamar saukar mutuwa, shi kuwa ba komai yake ji ma haushi ba face tunawa da yayi dazu yadda ya roketa akan yayi hugging dinta. Dama shi sakarai ne bai sani ba? Har yaushe zai roki wannan kucakar wani hug? Yayi me da stupid body dinta? Shi idan ma ba sakarci da ban haushi irin nashi ba there are classy and educated girls a Abuja wanda idan jaye wajensu abunda yafi hug ma Sai sun mashi. Wani tsakin ya karaja hangotan da yayi a tsaye inda ya barta hawaye sun taru a kan idanunta amma sunki sauka.

"Will you come over and serve me or not?! Aren't you maid or is it that you don't know what maids do?!" Wata tsawar ya kara daka mata wanda batasan lokacin data karaso kan dining din ba, dan kuwa har tuntube ta kusan yi da kasan skirt dinta.

Idanunta fixed on the warmers ta tambayeshi abunda zai ci, dan gudun kar ta kalle shi kuma cibi ya zama k'ari. Bai amsata ba sai ma wayarshi daya dauka ya fara latsawa. Fried rice da coleslaw din ta zuba mashi ta tura gabanshi kafin ta zuba mashi zobo drink din.

Plate ta kara daukowa zata zuba nata yayi wani tsakin, hakan yasa ta tsaya cak dan jin wani umurnin kuma zai bata? "Duk inda nake karki kuskura ki rika exceeding more than 5mins a wajen ba, karki kara gigin cin abinci dani ko zama falo while kinsan ina gida. Just make yourself unseen by me unless it's a matter of do and die, kinaji na?" Nodding kanta tayi dan kuwa she can't bring herself to answer this, but wata tsawar daya daka mata yasa dole tace toh jikinta har rawa yake ta juya ta tafi dakinta. Tana shiga ta ajiye plate din a bed side drawer ta fashe da kuka.

Kuka take har cikin ranta ta rasa mai lallashinta, ita wai batace sai sunyi rayuwar aure da Arhaan ba, but he should atleast treat her like human, wannan wulakancin dayake mata wallahi ya fara mata yawa, gashi ita duk wani strength din fada ya bar ranta, bama ta jin a halin da ake ciki she can fight him back. Tsoronshi take kamar ranta.

Saida taci kuka a gode ma Allah kafin a hankali ta fara cin abincin, sai kuma sai ta fara tunanin ya Baba yake? Inna tana bashi abinci ko? Ta rage mashi masifa ko? Ya T ya dawo? Were they able to locate gidan da Beeba take aiki? Dan ita wallahi abun nan ya far bata tsoro. She wants to speak to him, amma ko giyar wake tasha bazata taba iya tambayar Arhaan akan ya ara mata waya ba.

Sai lokacin la'asar kafin taji karar fitarshi daga part dinta, cikin hanzari ta fito dan kwashe kayan, saida ta tattara komai ta kai kitchen kafin ta ruga dakinta domin gabatar da sallar itama. Bayan ta gama sallah ne she thought to start making dinner idan ba so take suyi artabu dashi ba, hakan kuwa akayi, taje tana dinner ta jiyo sautin maganarshi a falon, dan dole ta maida kofar kitchen din ta rufe dan batasan ya ganta abun kuma ya zama bala'i.

Zafi ne ya isheta, amma tasan ko giyar wake tasha bazata bude kofar ba dole ta jira yabar part din nata. Ita wai meke ma kawoshi? Hawayenta ta goge kafin ta cigaba da aikinta, koda ta gama dan dole ta zauna aikin jira saida ya tafi maghrib kafin ta jera su kan dining ta tafi da nata daki.

Can bayan isha'i Sakinah ta tuna tanaso ta wanke underwears dinta har ma da kayanta, babu abunda ta tsana fiye da wanki ya tarar mata, sai yasa anan gara kwana biyu biyu ta rika yi, kar bakin ciki ya taru ya mata yawa. Toilet dinta ta shiga ta fara wanke kayanta, bataji shigowarshi ba saida taga mutum tsaye yana miko mata waya.

Wata irin zabura da tayi saida spinal cord dinta ya amsa, zatayi ihu kenan amma ganin rashin imanin dake kwance kan face dinshi yasa ta kumtse bakinta. "Karbi Mama zatayi magana dake." Ya fara with a soft tone amma his face says otherwise.

Karba tayi with hands full of foam kafin ta fita daga toilet din, gaisawa sukayi sosai cikin girmama juna kafin Mama ta fara tambayarta ko akwai abunda take bukata, har Sakinah tayi shiru kuma sai can tace "Inaso ne nayi waya dasu Inna." Murya can kasa ta furta.

Sallama Mama ta mata kafin ta mikawa Arhaan wayar, har tazo zata koma toilet din taji ya fincikota ya hada bayanta da bango yana jifanta da kallon da dole yan hanjinta suka kada, yanzu ita me tace? Wani kyakyawan mari ya sauke ma cheeks dinta kafin ya furta "Ke munafukar ina ce? Kin san kuwa maganar da Mama ta fada man saboda wannan? Wayar ce baki iya tambayata ko kuwa?! What are you after ne about my life? Ko so kike nayi maki wani abun kuma ki kirawo man mashayin yayanki ya kasheni this time around? Eh?!" Cikin wani karsashi da tsantar tsanar daya mata yake magana hade da shaking shoulders dinta violently, with a dare look in his eyes.

Thank you for reading.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now