BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

1.6K 230 35
                                    

Mama kallonta tayi sosai, ita kam hankalin yarinyar nan yana burgeta. Dukda ta kasance itace babba, amma batama kawo tunanin yadda Arhaan zaiyi sallah ba. "To nima Sakina bansan yadda zaayi ba, ko mu jira in nurses din sun shigo morning round sai mu tambaye su yadda zaayi?" Mama ta fada, sounding clueless.

Sakinah idanunta ta juya between Arhaan and his carbon copy as a mother. "Mama ayi haka toh? Saifa wajen 8 suke shigowa morning round din nasu. Ko a mishi alwallar a kwance in yaso yayi sallar da niya a zuciyarshi? Kinga fah as per as hankalinka na kanka, musulunci bai yadda ka jinkirta sallah ba." Sakinah reasoned, only if she knew how her words made an impact in Mama's heart, the woman suddenly got fond of her.

"Allah yayi maki albarka Sakinah, eh hakan ma yayi. Maza kiyi taki sallar toh." Mama ta amsa tana flashing ma Arhaan wani smile kafin ta wuce ta shimfida darduma ta tada sallah.

Saida Sakina ta fakaici idon Mama kafin ta kara matsa kafar Arhaan, tana kallo ya runtse ido; ba damar ihu balle yayi ko ya zageta ma. Hada ido sukayi ta jefa mashi one of her heart warming wink kafin ta wuce ta shiga toilet din.

Rasa me zaiji yayi, that wink stroke something beneath the layers of his heart, amma what she did to his leg? Yasan confirm dole sai ya rama. Yana nan zaune yana tunani ta fito daga toilet din, gefen fuskarta ya dan jike da ruwa alamun saida ta gama alwallar kafin ta maida hijab dinta.

Kallonta taga yanayi,hakan yasa ta galla mashi harara kafin ta karasa gefen Mama ta kabbara sallah cike da natsuwa. Yana kallonta, intently har ta gama raka'atanil fajr kafin ta dora da subh. Yadda take sallar kai kace diyar wani shehin malami ce, Arhaan duk kallan dayake mata bai taba tunanin tanada ilimi haka ba. Because when she opens her mouth, the words that erupts out of it says otherwise.

Koda Sakinah ta gama sallarta saida ta gama azkhars dinta kafin ta kalli gefen Mama taga ta janyo wasu books din azkhar tayi. Batace komai ba ta koma toilet din ta ciko wata yar roba data gani da ruwa. Ta tako har gaban Arhaan sai kuma ta tsaya tana kallon mamarshi. Shidai ba maharraminta ba balle ta kamashi tana mashi alwalla.

"Mama ga ruwan Alwallar," ta furta tana kokarin ajiye robar saman table din da was meant for his injections and medicines.

Mama mikewa tsaye tayi tana gyara hijab dinta, "Sakinah ki tayashi yayi alwallar, nikam I'm going out on a walk_jiki na duk yamin ba dadi inaji wannan katifar ce." Tana fadin haka ta karaso tayi side hugging Arhaan, pecking his forehead.

"Be well soon kaji Dan Mama?" A fully etched smile yayi flashing mata kafin tayi reciprocating itama kafin ta fita daga dakin.

Sakinah kallonshi tayi taga itama kallonta yake. Dauke ido tayi, bracing herself for the worst. "Sai ka gyara kwanciyar taka ko? Ka wani sharbe saman gado kamar ana narka kitse." Cike da tsiwa take magana, dan wani mugun kallo dataga yana jifanta dashi tasan tabbas rashin mutunci zai mata.

Baice da ita komai ba ya gyara zamanshi ya mike zaune. Oh, that was really out of Arhaan's behavior. Wani irin triumphant smile ne ya kubce ma Sakinah, dan ita duk tunaninta ta dauka matsa mashi kafa da tayi dazu yasa azabar ciwo taki barinshi ya tanka mata.

Toilet din ta koma ta dauko wani karamin bowl, dawowa tayi ta ajiyeshi kan laps dinshi kafin ta kalleshi alamun ya miko hannun. Arhaan baice mata komai ba yayi out stretching hands dinshi towards her. Oh, this is frightening kuma! She thought. For she assumed him insulting the living daylights out of her, but he didn't.

Saida ta rufe idanunta kafin ta bude, reluctantly ta fara zuba mashi ruwan akan hannunshi but he stood there not moving a muscle. Which irked her! "Wai Arhaan miye haka? Dan girman ka wanke hannunka, ka wani miko man hannu kaman karamin yaro." Harararshi take, ita ta gwanmace ya zageta amma ya wanke hannunshi da kanshi, dan har yanzu bata manta wannan abun dataji yana mata yawo ba bayan ta goge mashi kunu saman chest dinshi. Saiyasa bata san tabashi.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now