Episode 12

1.9K 86 1
                                    

.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*❤
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

® *REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

    # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

   *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 12
October, 2018

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Koda Sufyan ya fito daga masallaci motan sa ya shiga ya nufa gida,  a k'ofar gida ya tsaya ya kira abu mai aikin su ya umarce ta taje d'akin Sadiya ta kawo masa passport nata.

Ahankali take duban falour'n ganin babu kowa ta shige d'akin Sadiya dake nan kusa da na Hajiya Ruk'ayya.

Kasancewar ita ke gyara mata d'akin yasa tasan inda take ajiye wa, nan take ta d'auko ta fito.

Hamdala tayi ganin har ta fita daga falour'n babu wanda ya ganta, da saurin ta tanufi gate ta fita, Sufyan ta kira dan bata ga inda yayi parking ba.

Hasken motan data gano ne ya sanya ta nufan gurin, mik'a masa tayi yayi godiya ya tafi ita kuma ta koma gida.

Tun a hanya zazzab'in sa ya dawo dakyar ya iya ya k'arasar da kansa, yana parking ya nufi d'akin nasu nan ya tarar da ita kwance a k'asan tails ta rik'e kanta da but hands nata, jikin ta banda rawa babu abinda take tana kuka helplessly.

Duk halin da yake ciki haka ya daure ya nufa inda take da sauri ya zauna sannan ya d'ago kanta ya d'aura a laps nasa, ahankula ya cire hannayen nata ya sanya nasa yana mata kamun kai.

Ahakan wani wahalallen bacci yayi taking over nata, yana son ya mayar da ita d'aki amma ya rasa ta ina zai soma dan yadda jikin sa ke rawa ga wani irin sanyi dake ratsa sa ta ko ina.

Kwantar da kansa yayi kan kujeran dake bayan sa ahakan shima wani wahalallen bacci ya d'auke sa.

Duk rashin imanin ka inka gansu saika tausaya musu dan gaba d'aya jikin su banda rawa babu abinda yake yi hakan ne zai tabbatar maka ba k'aramin jin jiki suke ba.

_4:30 am_
Ita ta soma farkawa addu'a tayi sannan ta mik'e zaune, kallon Sufyan dake bacci a wahale ta tsaya yi, tausayin sa ne ya mamaye mata zuciya, bazata iya yafewa wanda ya jefa rayuwan su cikin k'uncin haka ba.

Duk dalilin ta d'an uwan ta mai k'aunar ta ya shiga wannan hali wasu siraran hawaye ne suka shiga zubo mata yayin da zuciyan ta ke raya mata ta gudu ta barsa at least ita kad'an ta zata sha wahalan rayuwa babu shi.

Again kuma wani sashi na zuciyan ta ke hana ta dan yadda yayi sacrificing happiness, family, jin dad'i da komai saboda ita.

Hannun ta takai ta share masa zufan dake goshin sa nan taji wani mugun zafi da jikin sa ya d'auka she just can't tell how much she love her twiny, mik'ewa tayi ta nufa toilet ta d'auro alwala sannan tazo ta tada sa.

MAKAHON SO _Blinded Love_Onde as histórias ganham vida. Descobre agora