Episode 45

2.2K 120 22
                                    

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
 . ❉ .¸¸.✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ .¸¸.❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆'-
...¸.¤ª '☆'_____________☾_____________-'☆'-
💕💞MAKAHON SO💞

Blinded Love
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯...¸.¤ª☆"˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆"˜¨''¨ '''_*Written By Beelkeey Shuwerh_ ''* "˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆'
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯...¸.¤ª☆"˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆  
¸.¤ª☆"˜¨•。❉ .¸¸.✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ .¸¸.❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ .¸¸.❄*.¸¸*❆

Wattpad @Shuwerh Beelkeey22

*In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*
*THE PAGE IS FOR KHADIJAH SUNUSI AND MARYAM AMIN MAI TURARE MY LOVE FOR YOU GUYS IS LIKE TEARS FROM THE SKY*

Episode 45
12_9_2019
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Neman guri yayi ta gefen Safwah ya tsare ta da ido dan tabbatar da zargin da zuciyar sa take, ahankali ya riqo kyawawan hannun ta yana qurama tafin hannun ta ido, wani irin faria ciki mara misaltuwa ne ya mamaye sa he just can't believe abinda idanun sa suke gani, dagaske akwai cikin sa jikin ta gyaran muryan da Zee tayi ne yasa sa dawowa hankalin sa.

Kallon ta yayi a tsanake yana son karantan yanayin ta jin motsin Safwah yasa sa saurin kallon ta, surprisingly ta soma binsa da kallo ganin dai time in dawowan sa baiyi ba, maidan da kallon ta kan Zee tayi with questioning expression.
Kafin takai da bata amsa husky voice nasa ta tare su " *Flower*!! Are you alright?"
Kallon sa ta tsayayi da mamaki kafin ta soma jera hamma not long enough kuma bacci ya sake daukan ta dan sosai take jin sa, "sleeping sickness" ya fada ahankali yana shafa fuskan ta.
Murmusawa Zee tayi ahankali tace "Baby ni gani nake kaman *Flower* is pregnant".
Murmushin ya miyar mata batare da yabi takan zancen nata ba yace "Sweetheart wanka zanyi".
Ahankali ta miqe taje dan hada masa ruwan.
Kafin ta dawo ya maida Safwah d'akin ta ya kwantar, komawa part d'in Zee yayi dan yin wanka, yana gamawa ta tayasa shiryawa suka fito falour suna kallo suna hira jefe_jefi, gaba d'aya hankalin sa yana kan Safwah lura da haka da Zee tayi yasa ta miqe jiki a sanyaye ta tafi part d'inta, bayanta yabi da kallo cike da tausayin ta kafin ya miqe ahankali ya nufa part d'in Safwahn.
Farkawan ta kenan taji alamun shigowan mutum wanda ko ba'a fada ba tasan waye cause tun kafin ya qaraso qamshin sa ya mata sallama, lumshe kyawawan idanun ta tayi son sa na qara fusgarta harya qaraso ya zauna a gefen ta.
Hannayen su ya had'e guri d'aya batare da yayi magana ba ya zaro wayan sa dake faman ringing, kafesa tayi da ido tana jin yadda yake bayani a nitse da alama da ogan sa yake magana, jin yanda cikin ta ke kukan yunwa yasa ta zame hannun ta ahankali ta wuce toilet, wanka tayi ta d'auro alwala jin an soma qiran sallah ta fito sai dai bata same sa ba da alama ya wuce masallaci, kaya marasa nauyi ta sanya ta d'auka hijab d'inta ta tada sallah, tana idarwa ta fito dan tsaban yunwa ji take wane taci babu, duba warmers da Zee ta jera a dinning tayi taji du k'amshin abincin bai mata ba saima tashin zuciya da suka sata.
Juyawa tayi ta koma part d'inta ta bud'o fridge inta ta d'auko _Abu bilal yoghurt_ daya zama favorite inta ta zauna akan kujera ta soma sha, tsaban yanda take jin dad'in sa har wani lumshe ido take, kafin ta farga harta shanye amma ji take kaman ba abinda taci.
Haka taita ciro abubuwa kala_kala a fridge in tana ci, jin qiran sallah yasa ta komawa d'akinta dan sauke farali, kafin ta idar da Sallah zuciyan ta ya soma mugun tashi.
A daddafe ta samu takai ta wuce toilet da sauri ta shiga kwara amai, dawowan Suwayd da Little Safwan kenan daga masallaci suka wuce part inta, ganin bata falour suka wuce d'akin ta, cike da tashin hankali Suwayd ya qarasa toilet d'in jin yanda take kakarin amai da alama ya dena fita ne, iya galabaita ta galabaita dan gaba d'aya ta fice hayyacin ta ga wani mugun zazzab'i da ciwon kai da suka rufe ta, a tsugune take amma jiri take ji Little Safwan ganin halin da take ciki yasa sa fashewa da kuka dan bai tab'a ganin Ammah'n tasa a wannan halin ba, rikicewa Suwayd yayi yama rasa yane zaiyi riqo hannun sa yayi in sorting tone yace " Je gurin Mummy kaji! Ammah will be fine".
Kasantuwar sa yaro mai ladabi yasa ba musu ya gyad'a kai ya wuce jiki a sanyaye, thought shikad'ai yasan halin da yake cikin ganin beloved Ammah'n sa ahaka, yana fita ya koma toilet d'in ya kamata harya samu aman ya lafa ya had'a ruwa ya mata wanka ya nad'o ta da towel yazo ya kwantar sannnan ya koma toilet d'in ya gyara gurin, bayan ya fito ya same ta still yadda ya barta, da kansa ya shirya ta sannan ya wuce ya had'o mata lipton ya dawo wanda ya samu tasha dakyar sai dai kuma kusan rabin sa saida ya dawo ga temperature nata daya mugun hawa.
Taimakon da zai iya bata yayi inda ya samu bacci ya d'auke ta, zama yayi ya tsare ta da ido cike da tausayin ta ya shafo cikin ahankali ya furta "Allah ya albarkaci abinda ke ciki".
Mik'ewa yayi yaje ya samu Zee dake ta faman rarrashin Little Safwan yaqiyin shiru, yana gano Dad in nasu ya taso da sauri ya qanqamesa yana sake fashewa da kuka, d'agesa sama yayi ya rungume yana rarrashi harya samu yai shiru then suka wuce dinning dan cin abinci sandai Zee da Little Safwah ne kawai ke iyaci dan su banda juya spoon ba abinda suke, du tunanin Suwayd bai wuce halin da Safwah take ba gashi yana ji yana gani a d'akin Zee zai kwana abinda ya hargitsa masa lissafi kenan dan yasan dole tana buqatar kulawar sa a wannan halin da take ciki, wane Zee ta karanci zuciyan sa ta miqe ahankali taja Little Safwan da Safwah ta wuce ta kimtsa su kowa ya wuce d'akin sa ta dawo agurin sa, zama tayi tana qoqarin mayar da kwallan da suka taran mata a ido ta riqo hannun sa ahankali ta soma magana " Baby kaje gurin ta har lokacin da zata samu sauqi nasan ayanzu tana buqatar ka fiye dani" tana gama fada ta miqe da sauri saboda kwallan data zubo mata yai saurin riqo hannun ta ya miqe ya qanqame ta qam ajikin sa sonta da tausayin ta na ratsa sa, kuka da take ta riqewa ne ya samu daman kwace mata ta soma yi ba qaqqautawa, kasa rarrashin ta yayi sai bayan ta da yake shafawa ahankali sanda tayi mai isan ta ya d'ago ta without uttering any word suka wuce part inta, da kansa ya mata wanka ya shirya ta ya nema guri ta gefen gadon ta ya zauna ganin ta kwanta ta juya masa baya, hannu yasa ahankali ya juyo da ita kafin ta fuskanci abinda yake shirin yi yai shutting ta da hot kisses, du yanda taso qin basa had'in kai ta kasa dole tai giving in wa kiss nasan suka shigayi passionate yet affectionate, sunfi minti goma kafin yai pulling out ya gyara mata kwanciya ya fice.
Yana fita ta fashe da masifaffiyar kuka sanda tai mai isanta tayi shiru wahalallen bacci yai taken over nata.
Yana komawa wanka yayi ya shirya ya kwanta ya qanqame ta ajikin sa zafin da jikin ta ya d'auka na ratsa sa, ga wani bala'in tausayin Zee da yake matuqar ji na mamaye zuciyar sa duk yadda yaso bacci ya d'auke sa abin ya faskara dan haka ya kwantar da ita ahankali yaje ya d'auro alwala ya dawo ya soma jera nafila.
Har uku baiyi bacci ba yana addu'o'i lokacin ne kuma jikin Safwah ya rikice banda rawan sanyi ba abinda take, haka suka kwana dan sai da sukayi Sallah'n asuba ya samu bacci ya d'auke ta, qiran gaggawa da aka masa a office yasa ko karyawa baiba ya fice, koda yaje kasa aikata komai yayi saboda tunanin halin da *Flower* d'insa take dakyar dai ya daure.
Acan kuma koda safiyan ciwo tayi sosai sai dai sha biyu nayi ta nemi komai ta rasa harta fito suka sha hira da Zee, qarfe uku ya dawo ganin ta dayai cikin qoshin lafiya ba qaramin farin ciki yai ba, wanka yayi yaci abinci ya zauna cikin su aka cigaba da hiran dashi.
Yamma nayi zazzabi yace salamu Alaikum haka ta kasance cikin mugun laulayi ga sleeping sickness,ga morning and evening sickness har tsayin wata zuwa lokacin duk ta gama fita hayyacin ta dan ma tana samun kyakkyawan kulawa, both dangi kowa yasan batun cikin wane akan cikin aka soma musu haihuwa haka suka dauko so da qauna suka daura masa.
D'aki guda a part d'in Safwah yasa aka soma gyarawa, wani irin gyara yasa akama d'akin na ban mamaki dan gaba daya yanda akayi decorating insa ne zai shaida ma saboda d'iya mace aka tanade sa, haka nan jikin say ke basa *PureLamp* insa mace zata haifa.
Luckily Abdul da Musty sun samu sun dai_daita da matan nasu har ankai kudi an tsaida rana sai jiran lokacin biki idan Allah ya nufa.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now