Episode 39

1.6K 103 8
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

Wattpad @Shuwerh Beelkeey22

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 39
24_1_2019
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

K'arfe tara ya shirya da niyyan zuwa d'akin ta, harya rik'e handle ya tsaya ya sake ajiyan zuciya saboda wani idea daya zo masa nan take, tabbas yasan this is the best way ya kamata yabi ya saita ta.
      Koma wa yai ya wuce part d'in Zee abin sa, tana zaune kan kujera da pizza hannun ta tana ci ya shigo, lumshe kyawawan idanun ta tai ta ajiye pizza'n kan plate ta tako ahankali tazo ta shige jikin sa, hugging ta yai back shima yana me sake kyakkyawan ajiyan zuciya, sunfi two minutes ahaka kafin ya zame ta ahankali ya rik'o hannun ta suka k'arasa ciki ya zauna kan kujera ya zaunan da ita kan cinyan sa.
Killer smile ya sake with a husky like-voice nasa yace ”Mi Amour nifa na kasa gane wannan kyan da kike k'arawa me sirrin?”
     Murmushi tai tace ”kai Nurul Qalb!”
Dariya sukai both jin yadda tai maganan, ahankali yasa hannun sa maran ta cike da neman tsokana yace ”Ya Baby na”.
Turo baki tai a shagwab'e tace ”nifa Nurul Qalb bani da komai”.
     ”To naji! Buh me had'in ki da pizza keda baci kike ba?”
”Hafsa ta koyan ci”.
     ”Hafsa ko Unborn?”
K'ok'arin mik'ewa ta soma ya matse ta k'ank'am jikin sa ”Ana asif Ya Farhati”.
    ”You know this isn't fair cause ni ba larabci nike ji ba”.
Murmusawa yai yace ”I mean am sorry my life”.
   Tsaban blushing cheeks nata har wani ja suka koma ”I Love you Nurul Qalb”
”I Love you more Ummun Unborn!" Ya k'arasa yana mata rising eyebrow.
Dariya tai ta tsare sa da ido, kallon ta shima ya soma wane zai had'iye ta dan ya fuskan ta abinda take so cause tunda ya lura tana da ciki ta maida abin wane ibada, matso da fuskan sa yai zuwa nata ya fito mata da tongue nasa, without any hesitation ta chafke ta soma tsotsa wane Sweet, tsaban yadda takejin dad'in hakan har wani lumshe idanu take yi, abinka da mai jiran k'iris take ya soma wasa da du wani sassa na jikin ta.
    Hot romance mai firgita ta ya soma mata nan take su duka suka fice hayyacin su, d'aukan ta yai chak in a bride like-style ya wuce d'akin ta daga nan kuma na basu guri.
Safwah na zaune tana kuka abin duniya ya ishe ta, a d'an zaman da sukayi da Ya Suwayd bata tab'a tunanin wannan son da yake nuna mata zai tafi ba, ga wani mugun fad'uwa da gaban ta keyi dole yau zata je ta basa hak'uri su dawo happiest perfect couples.
     Fuskan ta data mugun kumbura ta d'aurayo ta fito ta zura hijab ta wuce part d'in sa, ta dad'e acan tana zaman jiran sa bai zo ba dan haka ta mik'e ta koma babban falour, tun tara da rabi take zaman jiran sa har sha d'aya da kwata, hak'ura tai zata mik'e tana hawaye ta jiyo alaman bud'uwan part d'in Zee, k'ofan ta tsare da ido gaban ta na tsanan ta fad'uwa har suka fito.
Daga yanayin fuskokin su ta gane suna cikin farin ciki, kwanciyar hankali da annashuwa, kuka ne ya taho mata tai k'ok'arin saita kanta, Suwayd naganin ta yaji du ba dad'i amma ya moze.
     Da hannun sa ne kawai rik'e dana Zee amma dan ya sake b'ata mata rai saiya sak'alo kwankwason ta, runtse ido Safwah tai da k'arfi zuciyan ta wane zata tarwatse saboda bala'in kishi, ganin suna k'ok'arin wucewan su part d'in sa not minding halin da take ciki ta mik'e da sauri tai blocking su, had'e fuska yai yawa pregnant sky a hasale yace ”bamu hanya mu wuce!”
Hawayen data ke k'ok'arin dannewa ne suka zubo mata in crack voice tace ”Amirul Qalb!..” kasa ma magana tai saboda yadda kuka yaci k'arfin ta.
Cika Zee yai ya tako gaban ta wane zaiyi abin kirki tana ganin haka ta fad'a jikin ta sake kuka me ban tausayi, a tare both suka sake ajiyan zuciya dan yadda sukai bala'in missing juna, fatan su har wani k'aik'ayin son kasancewa da juna take amma yai saurin janye ta daga jikin sa ya ture gefe, rik'o hannun Zee yai ya juya ya kalla Safwah'n in i don't care manner yace ”i think tunda baki da abin fad'a sai ki bamu hanya” daga haka sukai shigewan su.
    Zamewa tai gurin tana kuka wane zata cire ranta, nan take taji wani irin zafi da ciwon k'irji, dafe k'irjin nata tai tana sauke numfashi dakyar, ta dad'e a wannan halin kafin ta iya tattara kanta ta koma part d'in ta.
Koda ta koma kukan ta cigaba harya saukar mata da mugun zazzab'i da ciwon kai, ga bacci da takeji amma barata iyaba ita tama manta when last rabon ta da bacci, tana cikin wannan halin Safwan ya k'ira ta sanda tai dagaske ta iya saita kanta dan ta gaji da kai masa k'orafi tasan hakan ba k'aramin damun sa yake ba, duk yadda taso daurewa ta kasa dole ta fashe da kuka, cike da tausayin ta ya samu ya rarrashe ta saida ta nutsu ya kashe wayan.
    Yana kashewa ya share hawayen da suka zubo masa ya nemo number'n Suwayd ya rubuta massage ya tura masa.
The following day, Safwah na cikin wannan halin ciwon Suwayd ya shigo, farin ciki ne ya kamata dan ita ta d'au rarrashin ta yazo yi ya bata hak'uri, lokaci d'aya kuma ta nema du wannan farin cikin ta rasa jin abinda yake fad'a.
    ”ki tashi Kije ki had'amana breakfast in kinga dama!”
Mik'ewa tai tana tangad'i wane wacce tai maye ta wuce, tana shiga kitchen ta zauna taci kuka ta gode Allah then ta mik'e ta soma had'a musu though ko fuskan tan me take batayi, shirmen ta kawai ta shirya taje ta jera musu a dinning, k'arasowa tai inda suke ta sunkuyar dakai k'asa dan barata jure ganin Zee kan cinyan sa ba murya na rawa tace ”nagama” daga ta juya zata tafi ya dakatar da ita ta hanyan daka mata tsawa.
   Chak ta tsaya jikin ta na mugun rawa, wucewa sukai tabi su a baya tai serving su sannan ta ruga part d'in ta da gudu tana kuka.
K'amshin abincin na bugan hancin Zee tai saurin turewa jin zuciyan ta ya soma tashi, wane zaiyi kuka yace ”Mi Amour what is it?”
    ”Nurul Qalb bazan iyaci ba noodles nake so!”
”Ohk Farhati ina zuwa”.
    Part d'in Safwah'n ya shiga ya tarar da ita kwance helpless jikin ta sai rawa yake, mugun son da yake mata yasa yaji he can't go on with the plan amma wani sashi na zuciyan sa yai saurin dakatar dashi.
”Ki tashi ki had'a ma Mi Amour noodles and better make it pass”.
    ”Habibi....” bai saurari mai zata ce ba ya fice.
Bata da option dole ta daure taje ta dafa mata cike da bala'in takaicin wai yau itane tama kishiya girki, kuka kuwa tun tanayi da hawaye harta koma na zuci.
    Lokacin data kai taci fad'a saboda chips d'in datai d'azun ta cika gishiri ga kwan ta manta bata sa albasa k'arni bai barsa ba, cike da masifa ya kalle ta yace ”Kuma wallahi kindai ji na rantse baza ayi asaran sa ba sai kin cinye”.
Ba kalan hak'urin da bata basa ba amma haka yasa ta dole saida taci, tana ci tana hawaye amman bai kyale ta ba sanda yaga empty plate.
     Tana koma wa part d'inta ta dinga amai gwanin ban tausayi, sanda taji wane zata amayar da 'yan hanjinta ta hak'ura ta fito daga toilet d'in a galabaice, ji take wane ta had'a kayan ta tabar gidan amma tuno last warning na Abuh yasa ta kwanta tana jin haushin kanta.
Haka ta kasance cikin wahala tsawon sati ga iskancin Zee daya fara isan ta, kullum bata da hutu sai yi mata girki and sometimes sai tayi sau uku tace bai mata ba kuma dole Suwayd yasata ta sake ko tana so ko bata so.
     Ranan da Sayyid yazo yaga halin da take ciki ga raman da tai sosai ta bashi tausayi, kukan da ya dad'e baiyi ba sanda yai a ranan he just can't believe adorable kitten d'in sa ce ta dawo haka saboda wahala, Sayyada taga tashin hankali dan mugun birkice mata yai.

MAKAHON SO _Blinded Love_Место, где живут истории. Откройте их для себя