Episode 32

1.9K 114 11
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 32
25_12_2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Mugun dukan da akayiwa k'ofan ta fad'o yasa Suwayd bud'e ido, idanun sa basu sauka kan kowa ba sai Musty, sanyin dad'i ne ya kamasa daga nan kuma bai sake sanin inda kansa yake ba.
      Kallo d'aya inkawa Musty baraka so ka k'ara ba dan yadda idanun sa sukayi wani mugun ja jijiyoyin kansa du suka mimmik'e, runtse ido yayi lokacin da idanun sa suka sauka kan k'afafun Suwayd, bai san sanda ya fuzgo Ammar daga kan Zee ba ya buga jikin wani mirror dake manne jikin wall.
T_shirt d'in sa ya cire ya cilla mata not knowing that already ta riga da ta sume.
      Komawa yayi kan Ammar ya fuzgo sa ya basa double punchs masu sauya kamanni, nan take kuwa baki da hancin sa suka soma bleeding, the more Musty ya tuno halin da ya riski Suwayd the more zuciyan sa ke burning yana sake bawa Ammar punch ta ko'ina.
Ganin punch won't work ya masa wani mugun shak'a ya had'a da bango.
At that very moment Arif, Sayyid da Haidar suka fad'o wane an cillo su, kan Suwayd Sayyid yayi cike da tsananin tashin hankalin halin daya gansa a ciki, tab'a sa yayi yaji gaba d'aya babu abinda ke functioning ajikin sa, a firgice ya soma jijjiga sa yana wani irin kuka "Akheey please wake up! Open your eyes for me please? Ka tashi dan Allah we are all here for you! Akheey ka tashi mana wasan ya isa haka!"
Jijjigasa yata yi yana kuka like domin shi aka turo sa duniyan, chak kuma ya cika Suwayd ya mik'e idanun sa suka k'afe yai kan Musty dake cin uwar Ammar, fizge Ammar yayi da mugun k'arfi daga hannun Musty ya buga da jikin wasu k'arfuna dake ajiye, idanuwan sa gaba d'aya sun gama rufewa burin sa ya raba Ammar da rayuwan sa inyaso shima a kashe shi.
     Bazaka iya gane Ammar ba dan yadda gaba d'aya hallitan sa ya chanza.
Tunowa da Sayyid yayi yadda ya samu Akheey d'in sa yasa ya sake finciko Ammar ya had'a da bango ya masa wani mugun shak'a da hannu biyo.
       "No Sayyid! let go of him,  don't let anger take over you".
Kojin Abuh dake masa magana baiba ya sake matse wuyan dan iska, had'uwa Abbah da Abuh sukayi suna k'ok'arin kwatan Ammar daga hannun sa amma in sam sun kasa.
       Dpo ne ya taimaka musu suka b'amb'are sa dakyar, fizge_fizge ya soma yi amma dan rik'on da Abuh da Abbah suka masa bana wasa bane yasa ya kasa kwacewa, wani irin nishi yake sosai like an angry hungry lion daya jiyo k'amshin d'anyan nama, idanun sa na sake sauka kan Suwayd ya fizge kansa da k'arfi ya janyo wani k'arfe mai shegen tsini yayi kan Ammar da polisawa ke d'aurawa handcuff ya caka masa a gefen ciki, zarowa yayi zai sake caka masa Arif ya fuzge sa da k'arfi yai baya.
      "Let go of me you son of a bitch" ya fad'a yana tunkud'a Arif gefe har sanda ya kusa fad'iwa, jansa Daddy'n Zee da Daddy'n sa suka somayi zasu fitan dashi dan sun lura sam ba ahankalin sa yake ba.
Ambulance da aka k'ira akai saurin d'aukan Ammar da cikin sa ke mugun bleeding to, and har lokacin da numfashi tattare da shi.
     Haidar ne yayi saurin jan rigan Musty ya runtse ido yasa wa Zee then yaja mata skirt d'in ta sama, d'aukan ta yayi wane Baby ya wuce da ita mota.
Dakyar aka iya gano mukullin handcuffs d'in da akayi locking hannayen Suwayd da tafukan suka mugun kumbura akayi unlocking sa, Arif da Abdul ne suka kama sa aka sanya a mota leading to AKTH..
     Da mugun speed suka ja motocin, ikon Allah ne kad'ai ya kaisu lafiya, su duka emergency ward akayi dasu.
Bayan hour d'aya aka fito da Zee da Ammar zuwa d'akin hutu yayin da lamarin Suwayd gaba d'aya ya zarce tunanin likitocin.
Babu takalmi ba d'an kwali ta fad'a motan ta soma buga uban horn kaman wadda zata yak'i, gaba d'aya ta jeme ta lalace wane ba ita ba, kyawawan idanun nan nata duk sun shige ciki sunyi bak'i, wangale mata gate gateman yayi taja motan a tsiyace.
     Tunda Ya Sayyid ya koya mata mota bata tab'a driving ba saboda tsoro, amma yau ji take kome zai faru sai dai ya faru.
Wani irin gudu take a titi harna fitan hankali du inda tazo traffic bata tsaya wa dan burin ta taga halin da *Amirul qalby* d'in ta yake, so hud'u tana attempting had'a accident Allah na kiyayewa har ta samu ta k'arasa asibitin.
     Da sauri gateman ya bud'e mata ta danna kan motar ciki, wani wawan birki taja lokacin data kusa buge wata mai ciki da nurse ta rik'o ta suna zagawa kanta ya mugun buguwa, bata damu da buguwan da tayi ba fito ko kashe motan batayi ba balle rufewa tai cikin asibitin kaman mahaukaciya dan yadda kanta ya wani irin barbajewa.
Addu'a mai cikin data kusa bigewa ta mata dan du tunanin ta tana da tab'in hankali.
     K'arasowan ta yayi dai_dai da fitowan doctor's daga gurin Suwayd, da gudu ta k'arasa ta shak'i wuyan sa jin last statement nasa, Arif ne yai saurin fincike ta ya rik'e hannayen ta both.
"Kaci k'arya you brazen bastard! k'aryan ka kace *Amirul Qalby* na zai mutu! sandai inkai zaka mutu asshole kawai, Ya Arif let go of me! Let me kill him first before he kills my *Hubby*, wallahi inhar wani abin ya same sa kaima i must kill you with my damn bare hands Crazy bitch kawai, Ya Arif ka cika ni..." Yadda take maganan ka rantse da Allah ta kora wani abin ne.
   Janta Arif ya soma yi zai bar asibitin da ita ta shiga kwala ihu like a fool, motar Ummy daya hango ya tabbatan masa aciki tazo, danna ta yayi aciki yai saurin shiga yai locking motan ya bata wuta.
Cikin asibitin kuma case ake sosai da Sayyid daya shige d'akin da aka kai Ammar yayi locking ta ciki yana k'ok'arin kaisa lahira.
     Dakyar aka samu aka b'alle k'ofan aka kwaci Ammar.
Ihu ta dinga yi ka rantse da Allah sato ta yayi, ganin bare saurare ta ba ta koma rok'o da magiya ya maida ta bazata sake abin rashin hankali ba, banza ya mata ya cigaba da driving abin sa, ganin haka takai both hannunta ta soma waina kan motan a titi, cike da tashin hankali Arif ya soma k'ok'arin kwace kan motan amma ta rik'e k'am, tura ta gefe yai da k'arfi ya tsaida motan dake ta juyi kan titi, k'iris ya rage basu buga wani range rover ba.
Bud'ewa yayi ya fito yana apologizing mutane, fitowa tayi tana k'ok'arin kwasa da gudu yai azaman cafke ta yana sake basu excuse kan tana da tab'in hankali, kiciniyar kwatan kanta ta soma yi Arif ya tsinke ta da marin dayasa nan take ta dawo nutsuwan ta.
Fad'a sosai yasha gun mutane kan marin daya mata haka dai ya samu ya turata mota tana kuka suka tafi gida.
   Hankali a matuk'ar tashe ya tadda Ammey da Granny nata safa da marwa a gate suna trying numbers d'in su Abuh.
Cike da haushi ya fito daga motan ya finciko ta ya soma janta inda suke,da sauri Ammey ta k'arasa ta rungume ta tana mai sauke ajiyan zuciya.
      Juyawa yayi da niyyan komawa asibitin Granny tayi saurin shiga motan and du yadda yaso ta hak'ura tak'i dole yaja suka tafi.
Jan Safwah Ammey tayi suka k'arasa cikin gida, Ummey na ganinta ta sake ajiyan zuciya tai saurin kawan da kanta Saboda alkunya.
   Lokacin dasu Granny suka isa asibitin basu samu Abuh da Daddy ba cause sun wuce processing Visa ta Suwayd, Abbah da Daddy'n Zee kuma sun wuce station dan a shigar da k'ara kotu.
Haidar, Sayyid, Musty da Abdul dake ta fama da Doctors su barsu suje inda yake kawai suka taran.   
      Kuka tata yi har sanda aka barta ta shiga ganin sa, lokacin data gansa da sauri ta dafe bango saboda mugun jirin dake k'ok'arin kada ta, she just can't believe beloved Grandson nata take gani cikin wannan mawuyacin halin, barata tab'a yafewa du wanda ya masa haka ba, kuka ta fashe tuno last best and sweet moment nasu. 
Fitan da ita akayi dan kukan da take yayi yawa, rungume ta Sayyid yai maimakon ya rarrashe ta sai ya jona ta sukayi tayi.
Musty ma kasa daurewa yayi kawai ya sake kuka, Haidar, Arif da Abdul kuwa kallo d'aya zaka musu kasan yak'e suke dan yadda idanun su suka mugun kad'awa.
Suna a wannan halin gaba d'aya family members d'in suka iso danyin sallama da Suwayd cause a ranan ake son wucewa dashi Cairo.
    Harda family'n Zee ma sunzo, rik'o Zee d'in da already ta farka akai leading to d'akin da Suwayd yake.
D'aid'aiku ne basu yi kuka ba lokacin da sukai arba da Suwayd, Safwah kam sanda Safwan ya rik'e ta saboda fad'uwan data kusa yi, dakyar ta daure ta iya bud'e baki tai masa addu'a then aka janye ta aka kawo Zee itama ta masa addu'a.
D'aya bayan d'aya suka dinga matsowa suna masa addu'a, Mammy kuwa fad'uwa kawai tayi aka wuce da ita, Ya Sadeeyq kuka ya shigayi tsakanin sa da Allah dan shima irin zuciyan su Sayyid gare sa, Ya Omar da Ya Uthman ne masu aikin rarrashi though suma daurewa kawai suke.
Lokacin da akazo fita da Suwayd daga asibitin hauka tuburan Safwah ta dinga yi sai an tafi da ita, dole Granny tace a k'ira su Abuh ayi mata Visa itama, Zee kuma akace a barta tunda bata da lafiya itama.
     Har airport suka raka su sannan suka wuce, Daddy, Abbah, Abuh da Safwah ne kawai za'ai tafiyan dasu, suna acan baya ta d'aura kan Suwayd a cinyan ta tana kuka like never before jirgin ya d'aga.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now