Episode 38

1.8K 103 6
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

Wattpad @Shuwerh Beelkeey22

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 38
19_1_2019
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Falour suka wuce ya zauna akan two seater, tana k'ok'arin zama kusa dashi yai saurin janyo ta kan cinyan sa, kallon sa tai ya kashe mata ido ta lumshe ido tana murmusawa.
     Hannayen sa ya sak'ale ta cikin ta ya tura kansa wuyan ta yana hura mata iska ahankali yana me sa tsigan jikin ta tashi, lumshe idanu ta sakeyi wani mugun kasala na soma saukan mata dan sosai tsumin da aka mata ya soma aiki.
Da wani shu'umin voice yace ”muyi kallon amma ke zaki dinga fassara min cause ni ba gane wa nake ba”.
     Shiru tai dan yadda muryan nasa ya mugun affecting ta bata jin zata iya furta ko wani kalma, ahankali ta d'aura hannun ta kan nasa tana rubbing gently, hakan yasa sa sakin ajiya zuciya yana sake tura kansa wuyan ta yana shinshina ta.
”Baby” ta k'ira sunan sa dakyar.
    ”Umm” ya ansa yana cigaba da abinda yake.
Jin ta kasa magana ya sake shigar da ita jikin sa ya matse hannun sa d'aya na yawo a k'irjin ta, ganin yadda ta sake kwantawa jikin sa tana lullumshe ido ya tabbatar masa sosai take k'arfan sak'on nasa da yake son isar mata.
      Zame ta yai daga jikin sa ya mik'e yaje ya rufo k'ofan part d'in ta cause already d'azun daya shigo ya rufe na babban falour ya dawo yai switching off kallon, in a bride like-style ya d'age ta suka wuce d'aki, bai dire ta ko ina ba sai kan lafiyayyan k'aton gadon ta, yana ajiye ta ya koma ya rufe k'ofan yai switching off hasken d'akin yabar dimp.
Tana kwance tana k'ok'arin saita kanta karya fuskan ta halin da take ciki na mugun buk'atar sa ya k'araso, ba zato kawai taji sa akan ta, murd'ad'd'en jikin sa ta kalla ta had'iya yawu dakyar dan daga yadda yake kallon ta tasan yau zataji maza, moisture lips nasa ya sauke a nata ahankali yana kissing ta passionately yet affectionate, kalan kiss d'in da yake mata yasa ta kasa jurewa ta soma miyar masa da martani, shagala da tayi wurin kiss da yake mata yasa harya raba ta da suturar ta bata sani ba sanda taji lallausan hannun sa na wasa da boobs d'in ta cike da kwarewa.
        Romancing ta ya soma sosai tana miyar masa sanda ya kashe mata jiki lis ko k'aramin yatsan ta bata iya d'agawa ya karanta addu'ar da Manzon Allah _S A W_ ya koyar ya wuce babban aiki, k'aran azaban da ta sake ne yasa ni saurin bar musu d'akin na koma falour, tun ina iya jiyo k'ananun ihun ta da kuka harna daina.

Some hours Later, Koda na koma hango ta nai kwance jikin sa fuskan nan du jirwayen hawaye, sanda 'yar nutsuwa ta saukan masa ya zame ta daga jikin sa cike da tausayawa ja jawo short nasa yai pulling ya wuce toilet, wanka yai cike da mamakin jarumta irin nata compared to Safwah data kusa hargitsa masa tunani ranan, amma daya tuna itane babba sai ya watsar da tunanin but still zuciyan sa na fad'a masa Safwah harda ragwanta. 
     Da kansa ya d'auke ta yakai toilet yai mata warming jikin ta then ya had'a mata wani ruwan ya baro ta tai wankan tsarki, bedsheet ya soma sauyawa ya shirya ya zauna zaman jiran ta, bata wani jima ba ta fito tana k'ok'arin b'oye masa halin da take ciki, da sauri ya k'arasa ya rik'o ta ya zaunar kan stool ya wuce ya d'auko mata simple night gown da bazata takura ta ba, da kansa ya shirya abarsa ya d'auka ya kwantar.
Joining ta yai ya jawo ta jikin sa ya k'ank'ame ahankali cike da neman tsokanan ta yace ”Mummy wallahi ke kika jawo min da....”
    Toshe masa baki tai da sauri cike da kunya, da muryan ta da bai gama dawowa daga dishewan dayai ba tace ”Allah ka dena banaso”.
Janye hannun ta yai daga bakin sa yana murmusawa ya cigaba da tsokanan ta, sanda yaga zatai kuka ya kyale ta ya tofe su da addu'a sukai falling into a beautiful sleep.
    Asuban fari ta farka, fuskan sa da murmushi ya kasa b'acewa ta tsare da kallo tana mai jin farin cikin halin da yake ciki, dan ko ba'a fad'a ba tasan yayi farin ciki da yadda ya same ta, cike da jarumta ta mik'e ta wuce toilet ta sake warming kanta ta d'auro alwala ta fito.
Ganin yadda yake binta da kallo yasa ta sunkuyar da kanta k'asa, ganin bata da niyyan k'araso wa ya mik'e yai pecking forehead d'in ta ya shiga toilet, alwala ya d'aura ya sanya bak'in jallabiya ya wuce masallaci, bai dad'e da fita ba aka tayar da sallah'n a daddafe ta samu ta idar dan yanda jikin ta ke rawa ta nema guri ta kwanta, ko five minutes batayi da kwanciya ba bacci ya d'auke ta.
    K'arfe shida da rabi ya dawo ganin yanda take bacci tana sauk'e ajiyan zuciya akai akai ba k'aramin tausayi ta basa ba, cire jallabiyan nasa yai ya rage daga shi sai 3¼ ya haura gadon ya janyo ta jikin sa ya k'ank'ame not long enough shima bacci ya d'auke sa.
K'arfe sha d'aya ta farka ganin baya nan ta mik'e ta shige toilet ta sake gasa jikinta ta fito, kwalya me kyau ta tsara ta saka jan gown na shaking material daya mugun fitting ta, hot red lipstick d'in data sa sosai ya mata kyau.
     Tana gama feshe jikin ta da turare sai gasa ya shigo, kallon ta yai tayi from head to toe yana admiring mugun kyan da tayi, abinka da mayen ja take ya soma fita hayyacin sa takowa yai ahankali yana k'ok'arin saita kansa yace ”Good morning Very Own!”
    ”Morning Sweetest darling ka tashi lafiya?”
”Lafiya lau Alhamdlillah Sweetheart! How was our first night?” ya k'arasa yana rising mata eyebrow.
    Rufe fuskan ta tai da both hannayen ta bashfully da muryan shagwab'a tace ”kaga halinkan ko?”
Sosai muryan datai using ya saukan masa da kasala, ahankali yakai hannu ya janye kyawawan hannayen nata datai covering fuskan, ta bud'e baki zatayi magana yai shutting ta da hot kisses, hannun sa yasa ya rik'o 'yar kwankwason ta Fulling her more closer to him ita kuma ahankali ta zagaye nata hannayen a k'eyan sa tana miyar masa da martani dan tana matuk'ar k'aunan kiss nasan, gaba d'aya ta manta bak'an wahalan data sha jiya sanda ta jisu akan gado, ture sa ta soma yi cike da tsantsan tashin hankali tana hawaye amma ina Suwayd yayi nisa baya jin k'ira.
    Hannun sa dake k'ok'arin zuge zip d'in riganta ta rik'e k'am murya na rawa ta soma magana ”Ya Suwayd dan Allah kayi hak'uri wallahi mutuwa zanyi, kaji tausayi na wallahi da zafi ban gama warkewa ba”.
Dakyar yana maida numfashi yace ”Am sorry Very Own bazan iya hak'ura ba, ki daina kukan kinji! Ahankali zanyi”.
    Kafin ta basa reply ya sake rufe ta da kisses, du yadda taso yai hak'uri ya kyale ta yak'i sanda ya sake durzan ta san ransa, kukan datai kuwa dole ta baka tausayi k'iran k'arfe d'aya da rabi da aka soma yasa ya kyale ta badan yaso ba.
Itakuwa baiwar Allah tsabar wahala ko motsi ta kasa sai idanun ta da hawaye suka kasa tsayawa kawai ke motsawa, gawani bala'in yunwa dake kwak'ulan ta, toilet ya wuce yai wanka dawo ya d'auke ta, wanka ya mata ya nad'o ta a towel wane jaririya yazo ya kwantar akan gado, falour yaje ya d'auko had'ad'd'en breakfast in daya shirya mata ya dawo.
     Akan stool ya ajiye ya haura gadon ya kwanto ta jikin sa ya soma feeding ta cike da tausayin ta dan bak'aramin murzan ta yai ba, yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya sai yafi komai baka tausayi, haka dai ya cigaba da bata harta k'oshi.
Kwantar da ita ya sake yi ya tattare kayan ya fita dasu ya dawo ya shirya ta yaja su sallah sanda suka idar suka koma suka kwanta dan both suna buk'atan hutu, tana k'ank'ame ajikin sa yace ”Sweetheart please forgive me!”
     Rufe masa baki tai tana nodding masa kai ahankali tace ”stop apologizing Baby ni baka min komai, a kullum buri na bai wuce na farin ta maka ba, indai hakan sai cigaba da farin ta ma i promise a kowa ni hali kayi yanda kake so dani.
K'ank'ame ta ya sakeyi cike da farin ciki, sosai kalamun ta suka bata kyakkyawan matsayi a zuciyan sa, pecking gashin ta yai yace ”Thanks Very Own I love you!”
     ”I love you more Baby”.
”Sai naji kaman Ya Suwayd kika k'ira ni d'azun? Ko du cikin wahalan ne?”
    Murmusawa tai tace ”to me aciki danna ce ma Ya Suwayd?”
Dariya kawai yai yace ”let's sleep Sweetheart am sleepy”, shiru ne ya ziyarce su har sarkin sata yai gaba dasu.
    A daren ranan Safwah kasa rintsawa tayi saboda yadda ranta ke a mugun b'ace which ita kanta bata san dalilin ba, ga bala'in haushin Suwayd data keji bai k'ira ta ba bai kuma zo ya ganta ba and yak'i picking call d'in data ke masa, washe gari ma kasa hak'ura tai ta cigaba da trying amma sam yak'i d'agawa, dan haka tai zuciya ta dena k'iran nasa.
Sai maraice suka tashi, sallah'n la'asar suka soma yi suka wuce kitchen happily sukai lunch, bayan sun gama ci suna zaune falour suna hira abin su Safwah data kasa hak'uri ta sake k'ira, wayan na hannun Zee ta mik'a masa Amman maimakon ya d'auka sai ya ajiye a side har k'iran ya yanke, sake k'ira tayi amman still baiko yi attempting d'agawa ba.
    Kallon sa Zee tai da mamaki tana sake kallon screen d'in ”itace dai! To me ya faru?” tai maganan a zuciyan ta.
Dafatan da yayi yasa ta saurin d'agowa, murmushi ya sakar mata yace ”kina bani labari kuma kinyi shiru”.
   Itama murmushin tai tace ”ka d'aga k'iran mana”.
”Is not important” ya fad'a yana kashe wayan gaba d'aya.
   Kukan da Safwah tai harya wuce na hankali, du wanda ya ganta sai yasan ba k'alau take ba amma tana k'ok'arin basarwa, tun daga ranan bata sake d'aga waya ta k'ira sa ba though bak'aramin damuwa tai ba.
Ta fannin sa ma Allah kad'ai yasan yadda yake azabtuwa da rashin ta amma yana k'ok'arin dannewa dan yadda Zee ke matuk'ar basa kulawa, kwanan ta hud'u kenan da dawowa tayi wani irin fari da kyau saboda hutu da kwanciyar hankali, shima sosai ya k'ara kyau fatar sa ta murje saboda hutu.
     Safwah kuwa harda rama ga rashin sukuni, tana zaune a d'aki tana kuka k'iran Kuwaysah ya shigo wayan ta, jiki a sanyaye ta d'auka sanda suka gama gaisawa take tambayan ta ina taje ta shigo bata nan.
Fad'a mata tai ita fa tunda aka gama biki tana gida then ta fayyace mata du abinda Suwayd ke mata, cike da masifa tace ”Wallahi Baby ni tunda nake ban tab'a ganin doluwa sokuwa irin ki ba! Saboda Sam baki da hankal! ai daidan ki kenan kinga kafin ki dawo Zee ta mallake abin ta sokuwa kawai”.
     ”Zee kuma?” ta fad'a da rawan murya.
”Eh ita d'in, da alama ma ciki gare ta dan abinci Ya Suwayd yasa na kawo musu ita bazata iya girkawa ba”.
   Ihu ta kwala cike da tashin hankali tai jifa da wayan ta, kuka ta shiga rusawa cike da azaban kishi ta mik'e ta tattare kayan ta taja trolley d'in ta tana kuka taje tai sallama dasu Mammy, driver ne ya kaita sanda ta gama kuka ta danna doorbell amma shiru, tana gwada waina handle taga a bud'e yake saka kan da zatai cikin babban falour'n idanun ta sukai mummunan gani, Suwayd da zee akan kujera sai kissing juna suke.
    Runtse ido tayi da k'arfi zuciyan ta wane zata tarwatse jiri ya d'ibe ta tafad'i, da both hannayen ta tadafe kanta dake barazanar barin ta tana nanata innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un, tafi k'arfin minti talatin cikin wannan mummunan yanayin amma su duka ba wanda ya lura da ita, sanda suka samu nutsuwa suna maida numfashi idon Zee ya sauka cikin na Safwah, dad'i ne ya kamata ta sake shigewa jikin Suwayd tana shafa shi, d'auke ta kawai yai suka wuce part d'in sa.
Suna rufe k'ofa ta sulale a gurin tana kokawa da numfashin ta, ko minti biyar bata k'ara ba ta sume a haka Abdul da yazo jin ko Suwayd yama Zee maganan MieMie ya same ta, cike da tashin hankali ya soma k'iran Suwayd d'in bai shiga, ruwa ya d'auko da sauri ya yayyafa mata taja dogon ajiyan zuciya, tana tuna abinda ya faru ta k'ank'ame jikin ta tana sake fashewa da masifaffiyar kuka, du yadda Abdul yaso tai shiru tak'i dole ya kyale ta ya cigaba da trying number'n Suwayd d'in, dakyar ta iya lallab'awa takai kanta part d'in ta.
    Nan take mugun zazzab'i da ciwon kai suka rufe ta, kuka ta cigaba dayi sosai tana dana sanin abinda tai masa haka har wahalallen bacci ya d'auke ta, ba ita ta tashi ba sai gab da magrib a daddafe ta wuce toilet tai wanka at least ko zataji dad'in jikinta ta d'auro alwala ta dawo, sallah'n la'asar da batayi ba ta fara sauke wa then magrib ta sake neman guri ta kwanta zuciyan ta na cigaba da zafi.
Lokacin da Suwayd ya fito zasa masallaci yasha mamaki ganin trolley ta Safwah a bakin k'ofan babban falour haka dai ya wuce cike da tunani kala kala, a hanyan su na dawowa Abdul yake shaida masa halin daya riski Safwah d'azu, sosai hankalin sa ya tashi amma ya moze, koda suka shiga gidan ko nakan ta baiyi ba ya wuce wurin Zee abin sa.
     Safwah tun tana sa ran zaizo dan tasan Abdul zai fad'a masa harta cire, yunwa take ji sosai amman batajin zata iyacin komai haka ta daure tai sallah'n isha ta kwanta ciwon ta na tsanantuwa.
Zee kasa gane kan sa tai dan gaba d'aya yana zaune da itane amma hankali da nutsuwan sa sam basa kanta, haka dai suka kwanta kowa rai ba dad'i.
Tsayin kwana uku haka suka kasance, Safwah ta gama ficewa hayyacin ta ganin yadda ciwo ke cinta tana k'ok'arin hallaka kanta ta daure ta k'ira Haidar a waya tana masa kuka, yana wurin aiki dan haka ya tura mata Kuwaysah, daga yadda Kuwaysah taji muryan mijin nata tasan da damuwa dan haka nan take ta tafi gidan, gaishe da Suwayd da Zee dake zaune a falour tai ta wuce part d'in Safwah'n.
     ”Lafiya dai ko?” ta tsinkayo muryan Suwayd.
Kallon sa tai taga gaba d'aya ma attention nasa nakan TV cike da haushi tace ”nima bansani ba” ta shige.
     Daga yadda yaji muryan ta yasan da damuwa dan haka ya zame Zee daga jikin sa yabi ta, tana kwance a k'asan tiles cikin mawuyacin hali suka shigo, a firgice Suwayd yai kanta dan bai tab'a tunanin ciwon kishin yakai haka ba and sharetan da yai yana so ne ya nuna mata abinda tai ba dai dai bane, d'aukan ta yai ya d'aura kan gado ya wuce ya d'auko kayan aikin sa ya jona mata ruwa, kallon Kuwaysah da cikin ta yad'an b'ullo yai yace taje ta kawo masa abinci mai ruwa dan ya lura harda yunwa a ciwon.

****..... ****
Safwan tunda ya ajiye Kadsah bata sake sanya sa a ido cause gaba d'aya yabar mata gidan dan shi ya rasa a layin da zaisa auren na sa'ar sa, du tabi ta damu ga tsoro da rashin sabo daya addabe ta.
    D'aukan wayan ta tai tana kuka ta k'ira Safwah, Safwah dake halin ciwon kishi dakyar ta daure ta d'auka wayan, jin kukan Kadsah'n yasa hankalin ta tashi, a rikice ta soma jera mata tambayoyi dan ta dau ma wani abin ne ya samu Safwan d'in dan sosai take mummunan mafarkai akan sa, tana kuka ta fayyace mata abinda yake faruwa.
Ajiyan zuciya ta sake ta soma calming ta sanda ta tabbata hankalin ta ya kwanta sukai sallama, tana kashewa itama Safwan d'in ta k'ira ta soma masa kukan tashin hankali.
     Sanda ta mugun d'aga masa hankali then ta nutsu ta soma magana ”Twiny why? Ashe shiyasa Yayan ta yake wulak'anta ni? Meyasa kake haka? Baka tinanin du abinda kama k'anin wani sai an ma naka? Gashi tun ba aje ko ina ba ya soma rama abinda kake mata akaina...” kukan daya sake cin k'arfin ta yasa ta kasa k'arasa wa.
Jiki a mugun sanyaye Safwan ya lallashe ta ya kuma yi mata alk'awarin bazai sake ba, sun dad'e suna waya kafin suyi sallama.
    Tunda sukai sallaman Safwah ta kasa nutsuwa dan gaba d'aya ta kasa gane ina kalamun sa suka dosa Ji take wane yana bar mata wasiyya, shikuma suna gama wayan bayan ya sallami men's d'in sa ya k'arasa gidan.
Tana zaune kan kujera ta takure kanta ya shigo, sam sai yaji ba dad'i ace ya ajiye ta tsayin sati bai damu da lafiyan ta ba balle halin da take ciki, ahankali ya k'arasa cike da tausayin ta ya zauna, tsaban yadda tai zurifi a tunani ko noticing batai ba sanda taji ta a faffad'an k'irjin sa, kuka kawai ta fashe masa dashi ya samu dakyar ya rarrashe ta ya bata hakuri.
    Tun daga ranan suka zamo happy couple, kullum suna tare in bai fita ba, in ya fita kuma waya zasu tayi gwanin burgewa.
Musty nacan ciwo nata cinsa in kagansa dole ya baka tausayin, gaba d'aya ya fice a hayyacin sa ya rame, tambayan duniya yak'i fad'an damuwan sa sometimes sai yaji wane ya koma ruwa, amma inya tuna alk'awarin daya ma abokan sa saiya watsar da tunanin.
     Abdul haukacewa ne bai ba saboda yadda MieMie ke wulak'an ta sa, kullum cikin yin abinda zai farin ta mata yake amma ina..
Safwah da Suwayd kuwa sam sun gaza samun nutsuwa dan data warke d'auke masa kai tai, du yadda yaso su daidaita tak'i kawai sai ya share ta ya kama Zee though ba a k'aramin takure yake da hakan ba.
    Yauma yana a d'akin sane, jiran duniya ya mata amma tak'i zuwa cause yanzu part d'in sa suke zuwa, haka suka kasance harna tsawon wata biyu, su duka kuma a mugun takure suke amma pride da ego yasa sun kasa daidaita wa.
Yau ya yanke du abinda zai faru saiya karb'a hak'k'in sa, ya gama yanke decision na koma mata ainihin Suwayd nada inba haka ba bara ta nutsu ba.....
    
    

Follow
Vote and
Comment on Wattpad
@Shuwerh Beelkeey22

MAKAHON SO ~Blinded Love~

*'Yar Gatan Miss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Onde as histórias ganham vida. Descobre agora