Episode 15

1.9K 97 1
                                    

.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*❤
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆


® *REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

    # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

   *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*
   Hia ix d second page Sweetheart really appreciate your love and supports no need for long essay you know​i❤you💯 #one love 💞

*HAPPY BIRTHDAY SWEETHEART FATIMA ABUBAKAR MANGA _AZLAND_  AM TRULY SORRY FOR THE LATE WISH*

Episode 15
October, 2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

A haka Abuu yazo ya tarar da Granny, hotunan ya tattare yayi keeping aside sannan ahankali ya soma wiping mata unstoppable tears nata yana kwantar mata da hankali.

Hulan sa ya cire ya mik'a mata kansa yana neman blessings nata, cike da so da k'aunar sa ta mik'a hannunta kansa ahankali ta bud'i baki tace " Allah ya ci gaba da yi muku albarka kai da 'yan uwan ka da zuri'ar ku ".

Cike da jin dad'in addu'an nata yace " Amin Mummy Allah ya k'ara nisan kwana ki ga auren mai gidan naki dana takwarar ki ".

Murmusawa tayi tace " Amin " hira yata janta dashi harya samu ta saki ranta sannan ya mata sallama ya mik'e ya fice.

D'akin Sadiya dake yanzu a matsayin nasu Safwah ya shiga dan duba jikin nata, nan ya iske su da Mammy suna hiran su with so much adoration.

Gaida sa Mammy tayi sannan su Safwah ma, ya jiki yayi mata kawai ya fice dan he has a lot to do.

Kallon su Sayyid Kawai Suwayd ya tsayayi ganin yadda suka hau manyan kaya wane masu shirin d'aurin aure, faran shadda suka sanya wadda tasha aiki da bak'in zare, sai hulan da suka sanya ma bak'a mai kyau.

Sai da ya dai_daici sun gama shirin su yayi saurin mik'ewa ya nufa falour yayi locking su acikin bedroom d'in.

Ba kalan rok'on da basuyi masa ba amma yak'i bud'e su dan ya riga da yayi promising kansa indai yana raye bare tab'a barin su suje duban wannan jakan yarinyar ba.

Ganin ma zasu takura sa ya fice daga falour'n again nanma ya sa ma k'ofan lock ha ya wuce site ta Ummy.

Tana zaune a falour yayi sallama ya shigo, amsawa tayi sannan ya k'araso ciki ya kwanta akan kujeran da take kai yayi placing kansa akan cinyan ta kaman wani k'aramin yaro.

Murmushi tayi takai hannun ta kansa ahankali tana shafawa " d'an gidan Ummy da alama yau rigiman ce ta motsa ko? "

Turo baki yayi kaman mace yace " dan Allah Ummy kisa baki Abuu ya barmu anan muyi karatu ni wallahi I don't wanna miss you guys more especially Baby ".

Murmusawa kawai tayi dan ta d'au Baby'n budurwan sa ce, shikam yana sane ya linke ta bai_bai dan yasan bara ta tab'a kawo Safwah yake nufi ba.

" Don't worry Son ai kaman yau ne zakuje ku dawo, wait ma who is the luckiest Queen data sace mun zuciyan handsome har bai so yayi missing ta haka? Ko Zee d'in ce? "

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now