Episode 31

1.8K 87 2
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 31
24_12_2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Lamarin ya soma basu tsoro dan kwata_kwata babu alaman nasara.
     Mutanen Saudiya da Ghana duk sun iso cike da tashin hankali, du wani kafan yad'a labarai sanda aka bada cigiyan amma shiru ba wani cigaba, kud'i masu yawa Abbah yasa kan du wanda ya kawo koda gawan Suwayd ne.
Ammar ne mutum na farko daya zo jaje koda yaga halin da Zee take ciki bak'in kishi yasa ya linka mummunan k'udirin sa kan Suwayd.
    Both Safwah da Zee sanda aka dangana su da asibiti saboda tsantsan tashin hankali.
Sam Arif da Musty basu yarda da Ammar ba amma Sayyid da Haidar suka basu tabbacin Ammar bazai aikata ba, a lokacin sun nuna sun yarda amma du wani motsi na Ammar akan idon su yake, du wani shige da fice na police station Ammar ne kan gaba.  
    Kud'i sosai Ammar ya k'arawa yaran sa dan yasan sukan iya changing mind nasu cause kud'in da Abbah yasa bana wasa bane.
In kaga Mammy da Granny sai ka zubar da kwalla dan yadda suka fice a hayyacin su, bama kaman Mammy da ko gani batayi bacci kuwa rabon ta dashi tun ranan da mummunan labarin b'atan tilon d'anta ya riske ta ya k'aurace ma idanun ta.
     Fannin friends nasu na school sam sun kasa believing Suwayd ya b'ata, majority cewa suke auren dolen da aka masa da Zee ne yasa ya gudu, wasu ma cewa suke asiri tayi masa haka dai kowa da kalan abinda ke fad'a.
Yau exactly kwana goma da b'acewan Suwayd, ranan kuma Ammar ya shirya zuwa cause tunda aka kama masa shi baije ba.
     Tunda ya d'au hanya ya lura da motan Musty dake binsa a baya, murmushi kawai yayi ya chanza kan motan sa zuwa station, cike da takaici Musty ya fizgi motan sa ya wuce.
Sanda Ammar ya tabbata Musty ya tafi yaja motan sa ya wuce unguwan da aka kai masa Suwayd.
      Suwayd na cikin tashin hankali saboda ruwan harya hauro hab'an sa, du k'ok'arin da ya kamata yayi dan ceton kansa yayi amma ina, k'afafun sa sunfi komai matsa masa danjin su yake wane ana daddatsawa da gatari.
D'auke numfashi yayi lokacin da ruwan ya kawo hancin sa, du kuma yadda yaso daurewa ya kasa dole ya sake numfashin a wahalance ruwa ya samu daman shiga.
   D'aga kansa sama yayi wani mugun hasken fitila ya dalle sa, had'uwan fitilan da idanun sa jiyayi wane barkono aka watsa masa cikin idon, fatan fuskan sa kuwa wani mugun ja yayi kaman wanda aka watsa ma soyayyen man gyad'a.
Saurin maida kansa k'asa yayi hakan ya bama ruwan daman cinye sa, yadda kasan kifi cikin koma haka Suwayd ya kasance.
   Dai_dai lokacin Ammar ya shigo, kujera yaja ya zauna yana kallon Suwayd dake a halin fitan rai sam babu imani ko tausayi tattare dashi saima murmusawa yake abinsa, Suwayd kuwa idanun sa har sun soma k'ak'k'afewa saboda azaba.
Sanda ya tabbatar Suwayd ya galabaita ya danna wani guri, k'aramin rariya ta bud'u a k'asan glass d'in ruwan ta soma shigewa, lokacin Suwayd harya sume haka ruwan ya rik'a k'asa, in less than fifteen minutes du ruwan yabi rariyan.
      Yana nan zaune yaran nasa suka shigo, gaida sa sukayi suka ja suka tsaya suna jiran umarnin sa.
Kallon su yayi d'aya bayan d'aya then ya musu umarnin fito da shi, nan take kuwa suka ciro sa suka d'aura kan wani kujeran k'arfe suka had'a hannayen sa da hannun kujeran sukai locking.
     Juyawa yayi yana kallon d'aya daga cikin yaran nasa dake bin Suwayd da kallon tausayi yace ya d'auko masa ruwan zafi.
Cike da rauni ya kalla Ammar yace "Master please..."
     "Just shut up and do what i said" yayi saurin tare sa a tsawace.
Juyawa yayi jiki a sanyaye ya nufa wani d'aki, kunno heater yayi yai boiling ruwan then ya tawo kawo masa, harya kawo k'ofa ya koma yad'an sirka ruwan sannan ya kai masa.
Yana saka hannu ciki ya d'ago yana bin yaron nasa da wani mitsiyacin kallo, jiki na rawa yai saurin sunkuyar da kansa yana jiran abinda zai biyo baya.
D'aukan ruwan yai ya juyewa Suwayd a kai, nan take kuwa yaja wani irin ajiyan zuciya jikin sa na mugun rawan sanyi.
   Bud'e idanun sa yayi dakyar ya sauke kan Ammar dake zaune ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya yana binsa da makirin murmushi, lumshe idanun nasa yayi ya sake bud'ewa ahankali.
Cike da rainin hankali Ammar ya soma magana "Halo handsome! What's up?"
Runtse ido Suwayd yayi cike da azaba da zugin da k'afafun sa keyi.
"Are You alright?" Ammar ya sake fad'i yana masa murmushin mugun ta.
     Ganin Suwayd ba kulasa zai ba ya soma da abinda ya kawo sa "Suwayd nasan baraka yi mamakin kawo ka nan dana yi ba cause laifin daka mun bana yafewa bane, so yanzu zan baka zab'i guda biyu inhar kana so ka cigaba da rayuwa, firstly ko kayi abinda nace ta ruwan sanyi ka ceci rayuwan ka, ko kuma nasa ka tak'arfi, secondly ko bayan na sake ka katafi banyarda kowa yasan am behind b'atan ka ba if not baza mu kwashe k'alau ba, now let's go straight to the point, here issa paper and pen inaso ka rubutawa Zee saki d'aya biyu har uku dan dani ta dace bada kai ba, ina binka da lallami dan haka kayi abinda ya dace inba haka ba everything might happen when i said everything i mean har mutuwanka, ka ajiye wannan izzah, tak'ama da jiji dakan naka dan bara su maka amfani ba".
Yana k'arashe kalamun nasa ya jiyewa Suwayd paper da biro akan cinya.
    Kallon you don't bloody know what is wrong with you yabi Ammar dashi then back to the paper, murmushi yayi cike da azaba yace "kace na saki Zee?"
"Yeah nasan kajini" cewan Ammar a hasale dan sosai murmushin Suwayd ya k'ona masa rai.
      "Over my dead body" ya fad'a yana sauke numfashi a wahalance sannan ya cigaba da magana "wallahi ko zaka kashe ni bazan sake ta ba, kuma na tabbata ko bayan raina Zee barata aure ka ba, a shirye nake ma du wani abu da zakayi cause am not scared of you, kuma nasan bazan dawwama acikin gidan nan ba inhar ta hanyan halal aka saman dani stupid bitch kawai".
Tasss Ammar ya tsinke sa da wani gigitaccen mari, bai gama dawowa saiti ba ya sake d'auke sa da wani marin.
"Kace bara ka sake ta ba ko?"
"Yes! Nasan ka jini" ya ansa sa yana binsa da kallo da idanun sa da sukayi mugun ja, fuskan sa kaman ka tab'a jini ya biyo hannun ka dan yadda tayi ja.
       Wani shegen dariya Ammar ya fashe da, sanda yayi mai isan sa ya had'e rai wane bai tab'a dariya ba, fuskan nan nasa sam babu annuri cike da tsantsan mugunta da rashin imani, ya jona ma kujeran da Suwayd ke kai wasu wayoyi then ya saka jikin switch.
D'agowa yayi ya kalla Suwayd daya runtse ido saboda azaban da k'afafun sa keyi yace "Hey evil witch! haryanzu kana akan bakan ka ne?"
     With nod kawai Suwayd ya ansa sa, murmushi ya saki cike da mugun ta yayi switching on switch in, nan take shocking ta kama Suwayd dama gasa kan kujeran k'arfe jikin sa kuma a jik'e, wani mugun jijjiga ya soma yi jini harda guda_guda na fitowa ta bakin sa.
Ammar na gefe yana kallon sa, yaran sa kuwa na gefe gaba d'aya jikin su yayi mugun sanyi cause they never know haka master nasu yake azzalumi.
       Wani mugun sparks switch in yayi Suwayd dake akan kujera ya fad'a akan k'afafun sa goshin sa ta fashe da tiles jini ta wanke masa fuska, tunda yayi wani k'ara kuma bai sake sanin inda kansa yake ba.
Juyowa yayi ya kalla yaran sa dake hawaye yace "Ka kunce sa and stay with him, wallahi kaji de na rantse inhar yayi escaping i won't spare you" daga haka bai sake cewa komai ba ya ware abin sa.
      Rogowan ukun ne suka jona sa suma suka wuce yayin da d'ayan yai saurin nufan Suwayd cike da tsantsan tausayi yana kuka, d'ago sa daga kifawan da yayi yai then ya cire masa handcuffs d'in, wani d'aki yaje da sauri ya d'auko farin kyalle yazo ya d'aurewa Suwayd kansa dan hana zuban jinin dake zuba.
Zama yayi a gefe yana tuno kyakkyawan fuskan Suwayd data koma wane ta Zombie, ko wani horror'n da ake gani a TV ya fisa kyan gani.
      Yana a wannan halin wayan sa yai k'ara, yana dubawa yaga Ammar nan take ya d'auka dan gudun matsala.
"Ka fito mu tafi" kawai akace aka datse kiran, kallon sumammiyar jikin Suwayd yayi ya fice jiki a sanyaye.
Kowa ka kalla cikin falour'n sai ya baka tausayi dan du basa cikin kwanciyar hankali, Zee na zaune a side tana kukan fitan rai yayin da Sadiya keta aikin rarrashin Granny dake ta kuka.
     Wani bala'in k'ara Safwah dake kwance kan sofa ta kwala hakan zai tabbatar maka mummunan mafarki tayi, abinka da siririya ta sake zabgewa kaman ba ita ba, fuskan nan ta wani irin kumbura saboda jaraban kuka.
A firgice Mummy tayi kanta dan kwana biyu kenan sun kasa gano kanta, ita kuwa ihu take tsakanin ta Allah tana ex claiming zasu kashe shi, addu'a Mummy ta soma tofa mata amma ina abin ya ta'azzara dan sai wani fizge_fizge take.
Fizge jikin ta tayi daga na Mummy da k'arfi tayi hanyan fita daga babban falour'n da gudu, kanta du ya barbaje wane mahaukaciya.
Cike da tashin hankali Kadsah da Mummy suka bita amma sam sun kasa taddo ta, tana isa gate Sayyid na shigowa cike da tsantsan tashin hankali ya damk'e ta, sai ihu take tana k'ok'arin kwacewa amma ta kasa.
     Janta yayi yaje yasa ta cikin dak'in su ya rufe, Buga k'ofan ta dinga yi tana kuka amma sam yak'i ya bud'e, zame wa bakin k'ofan yayi yanajin yadda take surutai wane tab'ab'b'iya ya fashe da kukan da shi kansa baisan ko na meye ba.
Can babban falour kowa hankalin sa a tashe yake dan du tunanin su k'ara haukacewa Safwah tayi.
     Abbah, Abuh, Daddy na zaune tare da Dpo suna sake tattaunawa kan matsalan Ammar ya shigo, idanun nan nasa sunyi ja alaman yaci kuka ya gode Allah, daurewa Abbah dakeji wane shima ya sanya kuka yayi ya rungume Ammar yana rarrashin sa.
Kuka sosai Ammar yai tayi wane k'aramin yaro, dakyar Abbah ya samu ya rarrashe sa yayi shiru suka wuce dan magrib tayi.
     Washe gari 'yan sanda na nan suna investigating case d'in yayin da su Abuh ke akan hanyan zuwa duban sa, tun safe suke yawo har goma na dare sannan suka hak'ura suka koma gida.
Abu kaman wasa gashi har ana neman cin sati biyu da b'atan Suwayd, sosai kuma hankula suka sake tashi.
   Yau kwanan sa uku a sume bayan izayar da Ammar ya masa, ahankali ya soma motsa hannayen sa jikin sa na wani irin rawa, runtse idanunwan sa yayi cike da azaba dan yadda k'afafun sa suka mugun kumbura, ga zugi da rad'ad'in da suke masa burin sa bai wuce du wani mai k'aunan sa ya cire masa suba ya huta, hannayen sa da yake ji kaman ba ajikin sa suke ba yaja dakyar ya dafe kansa dake azaban sarawa, du addu'an data zo bakin sa kawai yi yake, ya sani bakomai ke faruwa dashi ba sai alhakin Safwah da Zee dake bibiyan sa.
      Hawaye ne suka zubo masa tuno kalan mugun ta dayawa Safwah da wulak'ancin dayawa Zee a rayuwa.
Kwana biyu yayi acikin wannan mawuyacin halin ana ukun Ammar da yaran sa suka dawo.
        D'aga Suwayd yasa yaran nasa sukayi suka maida kan kujeran, suka sake locking hannayen sa both ajiki.
Jawo kujera yayi ya zauna yana fuskan tan Suwayd daya runtse idanu yana ji wane Ammar ya shak'e sa ya huta da azaban da yake ciki.
      "So Mr arrogant ya kaga salon nawa? Shin zaka sake ta ne ko kuma haryau baka shirya ba?" Cewan Ammar da alama he is capable of doing something.
Cije baki Suwayd yayi dakyar yace "What i want you to know is that Suwayd baya magana biyu, no matter what baran sake ta ba sai dai kayi duk abinda zakayi".
     Murmushi Ammar yayi yace "taurin kankan nan na burge ni, I so much like people like you that don't give up easily".
Wani leda ya k'arfa hannun d'aya daga cikin yaran sa, ya ciro wasu guntayen nail masu faffad'an kai sai hammer.
      Umarni yama biyu dasu bank'are masa tafin hannun Suwayd na dama, yi sukayi kaman yadda ya buk'ata ya dai_daita nail d'in a tsakiyan tafin hannun Suwayd ba tausayi ba imani ya buga hammer d'in akai, har fitsari sanda Suwayd yayi saboda azaba ya matse lip d'in sa na k'asa da hak'ori har sanda lip nasan ya fashe.
    Ammar kuwa sanda nail d'in ta b'ullo ta bayan hannun Suwayd ya kyale, karkuce haka yabar sa saida yama left hand nasa the same thing yama na hagun.
Zuwa lokacin Suwayd wani irin numfashi yake fitarwa na tsananin azaba da wahala, burin sa bai wuce Allah ya d'auka rayuwan sa ya huta ba.
      D'aga hab'an Suwayd Ammar yayi da mugun k'arfin da yakeji dashi yana binsa da wani makirin murmushi, da wani shegen murya yace "So haryanzu kana kan bakan ka ko zaka yi abinda ya dace?"
Murmushin yak'e Suwayd yai yace "Over my dead body man".
     Damk'an gashin kan Suwayd yayi wane zai tsinke su daga kan yana wuci yace "Haka kace ko?"
"Yes nasan kaji ni" ya amsa dakyar jijiyoyin kansa duk sun mimmik'e, idanun nan jawur wane garwashin wuta, hannayen sa kuma sai zuban jini suke.
"Good I like that then" cewan Ammar a fusace, kallon yaran sa yayi a tsawace yace "I need ice in less than fifteen minutes".
     "Yes master" d'aya ya ansa da sauri ya fice.
Bai d'au lokaci ba ya dawo ya mik'a masa, k'arfa yayi ya umarci d'aya ya kawo masa ruwa a roba, zuba ice d'in yayi ciki sanda ruwan yad'au mugun sanyi ya d'aura akan cinyan Suwayd, girgiza kai Suwayd ya dinga yi cike da tashin hankali meaning ya d'auke dan shi kad'ai yasan azaban da yake ji a k'afan sa.
   Kafin ya fuskanci mai Ammar yake shirin yi, ya d'amki gashin kansa ya danna cikin ruwan, sanda ya tabbata Suwayd yasha ruwa sannan ya d'ago shi, wani irin tari Suwayd ya shigayi ba k'ak'k'autawa amma taurin rai irin nasa yak'i barin sa yai abinda Ammar ke buk'ata, haka Ammar yata tsoma masa kai cikin ruwan harya suma sannan yai tafiyan sa.
Haka Suwayd ya kasance cikin azabtanwan Ammar har wata d'aya yayin da d'ayan side d'in kuma yafi kowa zak'ewa kan neman Suwayd.
     Addu'a kowa ya rik'a dan ita kad'ai ne mafita, Safwah kuwa kullum cikin mummunan mafarki take da Suwayd yana kuka yana cewa ta cece sa.
Zee na zaune ta buga uban tagumi taji k'ira na shigowa wayan ta, tai niyyan ignoring wani zuciyan ya raya mata d'auka, d'auka tayi tai sallama dan du tunanin ta 'yan jaje ne.
     "Ke kad'ai zaki iya ceton sa" daga haka aka datse wayan, cike da mamaki ta bi numban back amma switch up, batasan when ba ta kunna data nata.
Hoto taga an tura mata da wani number sai rubutu a k'asa kaman haka,, _rayuwan sa na hannun ki du kuma wanda kika fad'awa zaki samu gawan sa_ cike da tsoro ta bud'e hotunan, zaro ido tayi a tsorace tana kallon yadda mijin ta abin alfaharin ta ya koma nan take wani jarababben kuka ya kwace mata tai saurin toshe bakin ta da hannun ta dan kar a fuskanci halin da take ciki.
      Zamewa tayi ta fad'a toilet crying like never before tana tunanin azzalumin dayawa Suwayd d'in ta haka, babu abinda yafi d'aga mata hankali irin k'afafun sa data gani, dole ta ceci rayuwan Suwayd kota wane hali, d'auraye fuskan ta tai ta fito pretending as nothing happens dan tayi alk'awarin bazata fad'awa kowa ba.
Daren ranan kasa rintsawa tayi tana kallon hotunan tana aikin kuka.
      Washe gari Ammar yazo inda Suwayd yake, kallon k'afan Suwayd yayi cike da kyankyami Saboda ruwan da take zubarwa yace "A yau basai gobe ba zan rabaka da abinda yake da matuk'ar muhimmanci a rayuwan ka, tunda naga baka son ciwon kanka ba bakuma kasan abinda ya kamace ka ba wawa kawai, am now asking you for the last time shin zaka sake ta ko bazaka sake ta ba?"
"Bazan sake ta ba" ya fad'a yana sauke numfashi wane mai asma.
Murmushi yayi ya jawo gatari dake kusa dashi, then ya kalla yaran sa biyu yace su bud'a masa k'afafun Suwayd.
Ihu Suwayd ya shigayi gwanin ban tausayi, shiba wai tsoron abinda Ammar zaiyi masa yake ba, k'afafun sa da aka rik'e sunfi komai birkita masa lissafi, d'aga gatarin Ammar yayi ba imani ya saita manly part na Suwayd, yana k'ok'arin sauke masa akai yaji wuk'a a wuyan sa.
Juyowa yayi surprisingly yana bin yaron sa dake hawaye jikin sa na rawa da kallo, in crack voice ya soma magana "master bazan iya bari ba, I just can't live... " bai samu daman k'arasawa ba dan yadda Ammar ya shammace sa ya d'amke hannun sa ya soma murd'awa har sanda wuk'an ya fad'i k'asa.
Suwayd daya gama cire rai da rayuwa dakyar ya bud'e ido yana kallon abinda ke faruwa, tausayin yaron ne ya kamasa dan yasan mawuyacin abune Ammar ya kyalesa gashi duk cikin yaran shikad'ai ke tausayin sa dan har abinci yake kawo masa a b'oye.
        Yana wannan halin yaji yaron ya saki wani irin k'ara, d'aga kan da zaiyi yaga Ammar ya soka masa wuk'a, zaro wuk'an yayi ba tausayi ya sake sokawa yaron har sanda yakai k'asa, binsa yayi k'asan still ya cigaba da lumawa yaron wuk'an harya daina motsi.
A firgice abokan yaron suka sake Suwayd suna bin gawar d'an uwan su da kallo cike da tausayi da tashin hankali, Suwayd kuwa kuka ya soma yi tsakanin sa da Allah dan bai tab'a tsammanin zaluncin Ammar yakai ya iya kisan rai ba.
      D'agowa yayi yabi sauran yaran nasa da kallo a tsawace yace "make sure ka k'ira ta tazo gidan nan gobe".
Daga haka ya cire rigan sa data b'aci da jini ya goge hannayen sa ya tafi.
     Zee na kwance cike da jiran k'iran su k'ira ya shigo wayan ta, tana ganin numban data ke jira ne ta mik'e da sauri ta fad'a toilet, kallon mamaki su Mammy suka bita dashi.
Tana shiga jikin ta har rawa yake ta d'aga kafin tai magana akace "zaki ga address d'in inda mijin ki yake muna umartar ki da kizo ke kad'ai inba haka ba zaki tadda gawar sa" bata samu daman reply ba aka yanke kiran.
     Kuka ta zauna yi soasi sannan ta fito, tambayoyi sosai su Mammy suka shiga yi mata amma tace ba komai, tana zaune address d'in wurin ya shigo mata ta massage.
Kallon rashin yarda Musty ya shiga binta da dan shi sam baya sonta, suna had'a ido tayi saurin duk'an da kanta k'asa.
     Washe gari k'arfe goma ta gama shiryawa tace da su Mammy zataje gida, driver akasa ya kaita.
Tana shiga falour'n su ta fad'a jikin Daddy'n su dake zayyanewa Mammy halin da ake ciki tana kuka helpless.
       Rungume ta yayi yana aikin rarrashi inda ya samu tayi shiru dakyar, d'agowa tayi daga jikin sa ta rumgume Mummy'n ta tana feeling warm nata tana sauke ajiyan zuciya, ta dad'e ajikin ta kafin ta d'ago tana binsu da wani irin kallo mai cike da ma'anoni.
"Ina MieMie?" ta fad'a a sanyaye.
"At your back" tajiyo muryan ta, hugging juna sukai so tight sai kuma kuka, sanda sukayi mai isan su sukai breaking hug d'in, Zee ta mik'e wane an mintsine ta tace zata tafi, du yadda Daddy yaso ta Bari ya shirya ya tafi da ita tak'i dole ya kyale ta.
Har gate suka rakata both cike da kewan ta, ita kuwa saida ta zura k'afan ta waje ta dawo ciki ta had'a su both sukai group hug, sun dad'e a haka kafin tazame ta fice tana wani irin kuka mai ban tausayi.
     Cab ta tare ta basa address d'in inda zai kaita batare da neman ragin kud'in daya fad'a mata ba tace suje, minti talatin ya kawo su har k'ofan gidan da Suwayd yake.
Sauka tayi ta bashi kud'in sa ya tafi then ta saita nutsuwan ta tashiga cikin gidan.
     Tana shiga soron gidan duhu ya mamaye ta, tana k'ok'arin ciro phone nata a cikin side bag aka toshe mata baki ana tura ta har ciki, sanda suka isa har falour sannan ya sake ta.
Haske ne ya mamaye falour'n ta hango Suwayd daya mugun fita a hayyacin sa kwance kan tiles yana ta rawan sanyi.
      Da gudu ta k'arasa kansa tana kuka wane zata cire ranta, jin kukan ta yasa Suwayd bud'e kumburarrun idanun sa dakyar yana kallon ta cike da tsantsan tashin hankali.
"Baby!"
     Dakyar maganan sa ke fita dan yadda muryan sa ta dishe yace "Very Own mai ya kawo ki nan? Meyasa kika zo? Na rok'eki dan Allah ki tashi ki tafi?"
"No Baby! I can't! I just can't ka tashi mu tafi kowa yana can yana kukan rashin ka, waya kawo ka nan fisabilillah? And what do you do to deserve this?"
      "Auren ki" tajiyo muryan Ammar a bayan ta.
A firgice ta d'ago tana kallon sa in crack voice ta soma magana "Why Ammar? Meyasa ka biyo ni?"
       "Ni ba biyo ki nayi ba nadai saki kinzo".
Kanta ne ya kulle ta mik'e zata gurin sa Suwayd yakai hannu dakyar ya rik'o k'asan skirt d'in ta yana girgiza mata kai.
     Fuskantan Abinda yake nufi yasa ta tsayawa chak tana bin Ammar dake binta da d'an iskan kallo da ido, dakyar bakin ta ya bud'u tace "Ammar me kake nufi ne? Duk shige da ficen da kake kan b'atan Baby du pretending ne? Kuka and everything da kake du na munafinci ne?"
"Hakane abinda kika fad'a and du saboda ke nakeyi, da fake mijin ki yayi abinda na umarce sa da komai ya wuce hankula sun kwanta, sai dai kash taurin kai irin nasa yak'i barin sa".
      "Me kake so yayi maka? Idan kud'i ne wallahi ka fad'i ko nawa kake so zan baka".
Dariya yayi sosai kafin yace "lmao na miki kala da mai fatara ne? Hmm lallai to bari kiji ke nake *SO*, Ke nake so ya saki na aura and gaki kinzo rayuwan sa tamkar a hannun ki yake, tunda shi ya kasa yin abinda ya dace yanzu ke sai kiyi".
   "Ka fad'i kome ne zanyi matuk'ar bai sab'awa addini ba amma on one condition har sai an tabbatar min yaje gida".
"No Very Own! stay out please!" Suwayd ya fad'a dakyar yana tears yana girgiza mata kai.
       "Junky mai yasa bakajin magana ne? Now lemme warn you for the last time, wallahi kaji na rantse inhar ka sake magana sai nayi maganin ka" cewan Ammar in serious note.
Taass kakeji Zee ta d'auke sa mari bai gama dawowa saiti ba ta sake sauke masa wani, ko gezau baiba ya tsare ta da idanu yana wani irin makirin murmushi.
   Afusace tace "zan iya juran komai amma banda wulak'an ta min miji, ban tab'a sanin baka da hankali ba sai yau, na tsane ka wallahi da du ma masu hali irin naka, I really hate you!.."
     "Shut up! Saboda wannan abin da kike kira miji kika mare ni?"
"An mare ka! Nace na mare ka" d'aga Hannu tayi da niyyan sake marin sa ya rik'e hannun nata k'ank'am.
K'ok'arin kwata ta somayi amma ta kasa dan rik'on daya mata bana wasa bane, kallon yaran sa yayi yace "ku maida sa kan kujeran kukai min shi wancan d'akin, kai kuma nasan maganin ka and yau basai gobe zan mallake ta".
"Kar wanda ya tab'a sa na fad'a muku" cewan Zee tana k'ok'arin kwatan kanta daga hannun Ammar.
  Ba wanda ya kulata suka cika umarnin shugaban su suka dawo, janta Ammar ya soma yi zuwa d'akin tana tirjewa, ganin zata b'ata masa lokaci ya d'age ta chak a kafad'an sa, dukan sa take da iya k'arfin ta amma yak'i ya sauke ta har zuwa d'akin.
Ajiye ta yai ya maida k'ofan ya rufe, da gudu taje ta k'ank'ame Suwayd ta baya tana kuka sosai, hannayen sa yakai kan nata ahankali shima yana hawaye.
       K'arasowa Ammar yai yana kallon su cike da azaban kishi, murmushin yak'e ya sake yace "kak'i ka saketa ta lallami, yanzu zaka sake ta ai dan nasan bak'in kishi bazai tab'a barinka ka zauna da matar da wani d'a namiji yai mu'amula da ita ba".
Sake k'ank'ame Suwayd tayi tana wani irin kuka Ammar ya fuzgo ta ya cilla kan gadon dake d'akin, mik'ewa tayi da sauri yaja k'afan ta tasake fad'awa yai joining ta.
Kuka Suwayd yake sosai muryan sa na fita dakyar yace "Ammar dan Allah dan Annabi ka kyale ta, i beg of you Ammar dan Allah ka barta, ka bari please".
Kojin sa Ammar dake kokawa da Zee baiba saima cigaba da abinda yake so yayi.
   Yak'ushi sosai yasha amma sam yak'i sakin ta sai wasu abubuwa yake mata wane tsohon maye.
Wani irin k'aran azaba ta sake jin wani mugun damk'a da yawa k'irjin ta, runtse ido Suwayd yayi yana jin dama ya mutu ya huta da ganin wannan bak'ar rana, da yana ji yana gani za'a keta haddin matar sa amma bazai iyayin komai ba.
Sunan sa da Zee take k'ira ya taimaka mata yafi komai d'aga masa hankali, runtse ido kawai yayi jikin sa na wani irin kakkarwa, zuciyan sa wane zata tarwatse.
Mugun dukan da akayiwa k'ofan ta fad'o yasa Suwayd bud'e ido, idanun sa basu sauka kan kowa ba sai........

Follow
Vote and
Comment on Wattpad
@Shuwerh Beelkeey22

MAKAHON SO ~Blinded Love~

*'Yar Gatan Miss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now