Episode 33

1.8K 90 4
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

        *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*

Episode 33
27_12_2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Lumshe idanun ta tayi hawaye masu zafi suka kwarinyo mata.
     Abbah ne ya matso ahankali ya rungume ta yana rarrashi, kunya ta jiyo wane ta nutse, da Abbah yasan itane sila da bai rarrashe ta ba sanda tayi shiru ya zame ta daga jikin sa ya rik'o hannun ta ya soma yi mata nasiha mai ratsa jiki.
Haka Suwayd ya kasance k'ark'ashin kulawan likitocin harna tsawon sati d'aya, a cikin sati d'ayan kuwa kullum saiya rok'i Allah ya d'auka rayuwan sa ya huta cause bazai iya d'aukan abinda *PureLamp* tasa ke masa ba, shi haryanzu ma ya kasa believing *Flower* d'in sa raguwa mai tsananin tausayi ce ta koma haka.
     Yauma yana zaune an jingina sa da pillow yayin da ita kuma kecan toilet tana wanka, tun kafin ta shiga wankan ya rok'i ta taimaka masa da ruwa amma tayi banza dashi ta wuce, gashi k'ishirwa yake ji sosai cause rabon data basa yasha yau kwana uku kenan, shikuma yayi alk'awari du abinda tace bataso bareyi ba shiyasa ya kasa tambayan su Abbah su basa.
Yana a wannan halin ta fito, ko arzik'in kallo bai samu ba ta wuce ta d'ibi kayanta ta koma toilet ta sanya ta fito, d'an k'aramin glass cup ta d'auka ta tsiyayo ruwa ko kwatan sa baiba ta tako ta mik'a masa, tsayawa yayi kallon ta yayin da zuciyan sa ke masa wani irin zugi, hawaye ne suka zubo masa abin tausayi ya mik'a hannun sa da haryau bai gama warkewa ba zai karb'a, mistakenly cup d'in ta sub'uce ta fad'i k'asa ta tarwatse dole Suwayd ya baka tausayi in kaga tsantsan tashin hankalin daya shiga.
Tausayi sosai ya bata ganin yadda hawayen sa suka tsanan ta amma ta moze ta soma magana harshly "Kaga halin kan ko? Yanzu ka huta ai dan wallahi inhar ni zan sake baka ruwa sandai in bara ka sha ba mtswee" taja tsaki ta fice daga d'akin gaba d'aya taje ta samu guri ta soma aikin kuka.
Runtse ido Suwayd yayi da k'arfi zuciyan sa wane zata tarwatse, shi bawai abinda ta masa bane ya tsaya masa arai sai tsaki cause ya mugun tsanan sa, data masa wallahi gara ta mare sa kuka ya fashe dashi gwanin ban tausayi kan sa na tsananin sarawa.
Ahaka su Abbah suka zo suka same sa and du yadda suka so ya sanar dasu damuwan sa ya kasa sai kukan sa daya dad'u, ganin ba mahalicci sai Allah aka k'ira Dr ya masa alluran bacci wanda bashi ya tashi ba sai k'arfe goman dare lokacin har tayi bacci.
Kwana yayi yana aikin tunane_tunane ga kewan Zee da son ganin ta dake d'awainiya dashi though suna waya, sai da gari ya soma haske bacci ya d'auke sa.
      Da safe wata nurse tazo basa abinci cause likitocin sun soma complain ulcer na k'ok'arin kama sa Saboda bai son cin abinci Safwah ta kore ta wai ita zata basa, bata kawo komai aranta ba ta ajiye abincin ta tafi.
Tana fita Safwah taja abincin tai bismillah ta soma ci tana kallon sa ta k'asan ido.
      Folding hannayen sa yai a k'irjin sa yana kallon ta wane lokacin ya soma sanya ta a ido, d'agowa tayi a tsiwace tana kallon cikin idanun sa tace "Hey Mister! ka daina kallo na haka kaman zaka cinye ni, idan yunwa kakeji zan rage maka kaji d'an gurgu!" ta k'arasa tana hararan sa ta cigaba dacin abinta.
Shaf ta manta bata rufe k'ofa ba saijin sallaman su Abuh tayi, jikin tane ya soma rawa tai saurin seta kanta ta sanya kuka, da mamaki Suwayd ya bita da kallo yana tunanin mai kuma take shirin yi.
    Da sauri ta rik'o hannun Abbah tana tsanan ta kukan ta tace "Abbah ka masa magana yaci abinci please".
"Yanzu Baby saboda yak'i yaci abincin kike wannan kukan?"
    Gyad'a masa kai tayi yadda bare gano pretending ne take ba.
Shafa kanta yayi yace "Toh shikenan Mamana! kukan ya isa haka share hawayen".
Hannu tasa ta goge munafukan hawayen then ta k'arfa kayan hannun sa ta k'arasa ciki dasu, kallon da Abuh kebin ta dashi sanda yasa hantar cikin ta kad'awa, ganin haka tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa tana addu'a Allah yasa bai gano ta ba.
K'arasawa yayi yaja kujera ya zauna ya bud'e abincin dake hannun sa ya tamke fuska, d'iba ya soma yi yana bawa Suwayd yaga yadda yake ci sosai, koda ya cinye Abuh yaga alaman bai k'oshi ba dan haka ya bud'e masa wanda aka kawo matsayin na Safwah, shima Kuwa sanda ya gama masa aiki cause an dad'e ba'a had'u ba. 
Ruwa kuwa daya soma sha har kwarewa sanda yai dan gani yake kaman Safwah zata kwace.
Kallo d'aya zakayi wa Abuh kasan ransa a bala'in b'ace yake, juyowa yayi a tsawace yace "Dan Ubanki zo nan!"
jiki na rawa ta soma b'uya a bayan ba, "idan kika kuskura nazo nan wallahi sai nayi mummunan sab'a miki" ta sake tsinkayo muryan sa.
Bata da option daya wuce zuwa, kallon ta yai daga sama har k'asa a fad'ace yace "Yanzu ubanki ne yaci abincin?"
shiru tayi tana hawaye ya sake cewa "nace ubanki ne yaci?"
Girgiza kai ta soma yi tana hawaye sosai sai jin muryan Suwayd tayi yace "Abuh please a hannun tane bana so", d'agowa tayi tana kallon sa yai saurin kawar da kansa yana takaicin k'aryan da yayi.
Nan take jikin Abuh yayi sanyi tausayin d'iyar tasa ya kama sa, ashe kenan haryanzu Suwayd bai sauko daga tsanan dayama k'anwar tasa ba.
  Fad'a sosai Abbah ya rufe Suwayd da cike da takaici, sannan ya jaddada masa daga rana irin ta yau inhar bazai ci abinci a hannun Safwah ba sandai yata zama da yunwa, sunkuyar da kansa yayi k'asa ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Cike da tausayin halin da yake ciki Abuh ya soma calming nasa yana masa nasiha, nan yake ji gobe Sayyid zaizo su kuma zasu tafi dukan su.
Ta wani fannin yaji dad'in zuwan da Sayyid zai ta wani fannin kuma sam baiji dad'i ba.
Washe garin kuwa suka tafi, a ranar kuma yaga tashin hankali dan kuka Safwah ta zauna ta dinga yi masa wai saiya tashi ya goya ta, rarrashin duniya yayi amma tak'i yin shiru.
Haka ya zuba mata ido yana kallo zuciyan sa na matuk'ar tafasa dan shikad'ai yasan yadda kukan ta ke tab'a masa zuciya.
Suna zaune da daddare tana zuba masa rashin mutunci saiga Sayyid, yaso yayi suspecting wani abu Suwayd ya d'auke masa hankali.
Haka suka kasance har tsawon wata biyu, inta faki idon Sayyid tata gallaza masa, wani abin ma in Sayyid zai masa saita hana tace already ta masa which k'aryan ta ne kawai.
Ya samu sauk'i sosai sandai ciwo da zuciyan sa take cause abinda Safwah ke masa ya wuce duk tunanin mai tunani, ita kanta mamaki take ya akai ne ta zama evil haka bata sani ba.
Fitowan ta kenan daga wanka daga ita sai guntun towel Dr Asim ya shigo, tsare ta yayi da idanu wane zai had'iye ta yayin da Suwayd ke mata alama taje ta sanya hijab dan ya lura ba tun yau ba Dr Asim is up to something towards her amma tai banza dashi, cike da azaban kishi yace " *PureLamp* dan Allah badan ni ba kije ki sanya hijab" yadda yai pleading wane itane gaba dashi dole ya baka tausayi.
Haushi ne ya kama Dr Asim jin sunan daya k'irata ya juya ya fice da kud'irin fayyace mata du abinda yake ji game ta ita a yau.
      Glares masu rai da lafiya ta masa sending ta wuce taje ta soma sanya kaya, addu'a kawai Suwayd yake a zuciyan sa Allah yasa sai ta gama shiryawa wani zai shigo.
Luckily kuwa sanda ta gama Sayyid ya shigo, ajiyan zuciya ya sake wanda both sai da suka jiyo.
Suna zaune sai ga wata nurse ta shigo wai Dr Asim nasaon ganin Safwah, kallon nurse d'in tayi tace "Ohk i will be right there!"
Da sauri Suwayd yace "You are not going anywhere! Akheey please kaje kaji mai matsalan" yadda yayi maganan ya isa shaida maka jaraban kishin sane ya motsa. 
     With nod kawai Sayyid ya ansa sa yabi nurse d'in, Sayyid na fita bakin rashin kunyan ya bud'u, kuma hartayi ta gama baiko kalle ta ba.
Lokacin da Sayyid yaje fayyace masa komai Dr Asim yayi, nan ya bashi hak'uri ya fad'a masa matar Suwayd d'in ce, daga nan masaukin sa kawai ya wuce dan Dr ya tab'o masa inda ke k'aik'ayi, Suwayd kuwa kwanan sanyi da yunwa yai yayin da Dr Asim ma sam kasa rintsawa yayi.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now