Episode 23

1.6K 100 2
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*​💭💭💭

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://

.
   . ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO*💞

       *Blinded  Love*
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

   *In dedication to Asmeey Real Pure Pinkeey*
*_This page goes to Hasana, Fatysha, Ummu Islam,Sparkle,Princess Ummu, Zee Hussain, Mhiz Rukye dadai sauran ku, know dat Beelkeey Shuwerh always love and cherish you guy no need for long essay I luv you guys plenty._*
  
Episode 23
November, 2018
Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Ya juye mata ajiki, duk inda ta fashe ajikin ta saida ruwan k'ank'aran ya ratsa, saboda tsananin azaba batasan sadda ta soma addu'an Allah ya d'auka rayuwanta ta huta ba.
      Idanun tane suka k'akk'afe gaba d'aya ta sank'ame, yana ganin haka ya sake goran ruwan yayi kanta hankali a tashe.
Hugging nata yayi so tight ya fashe da wata matsananciyar kukan da tunda Mammy ta haifesa bai tab'a yin irin ta ba, " Flower meyasa kike min haka? Meyasa bazaki gane tsananin kishin da nakeyi ba akanki? Meyasa kike son forcing d'ina hurting ki? What I Did Was Foolish & Impulsive, If I Cud Take It All Back I'd Do This So Instant, I Truly Didn't Mean To Hurt You In Any Way, I'm Sorry For Hurting You Flower, I Love you, I Love you, I Love you,words can't never ever explain how much I love you Safwah , the love I have for you is far beyond imagination, ni kaina har tsoron kalan soyayyar da nake miki nak..... " kukan daya ci k'arfin sa ne yasa sa k'ank'ame ta wane za'a kwace masa ita yana ta surutan sa wane zararre.
      Zame ta yayi daga jikin sa ya mik'e ya bud'o wata safe, nan take ta bayyano da expensive wines nasa, kwalba biyu ya cire ya maida ya rufe ya zauna ya soma bankawa cikin sa, du ya had'a ya shanye batare da tsoron illar da zatayi masa ba, komawa yayi kusa da ita ya had'e hannun su yana ta sumbatu har wani wahalallen bacci ya d'auke sa.

*3:00 am*
Ta bud'e idanun ta tayi saurin rintsewa dan gaba d'aya d'akin ya juya mata upside down, mugun zafin da jikinta ya d'auka ya isa shaida maka mawuyacin halin da take ciki, dakyar ta iya ta mik'e zaune ta jingina da bango tana fitar da numfashi a wahalance.
     Bud'e idanu tayi dakyar tana bin d'akin da kallo, nan take tsoro ya baibaye ta jan jiki ta somayi tana dafa bango tabar d'akin dan karta sake jawo wa kanta bala'i, ko lura da Suwayd dake kwance ta d'ayan side d'in ta bata yi ba, gashi dai a zaune take amma mugun jiri take ji, kanta saboda azaban ciwo ji take wane ta cire sa ta huta.
Dakyar ta fita mazaunan ta du sun d'au sanyi saboda jan jikin da tayi, a bakin k'ofan ta sake jingina tana maida numfashi sai da ta d'au tsayin lokaci sannan ta daddafa ta mik'e dakyar tana tangad'i tana had'a k'afa wane 'yar maye ta nufi part d'in Granny , duk wani tsoron dare da takeji yau ta neme shi ta rasa sai mugun tsoron Ya Suwayd.
Luckily k'ofan a bud'e take dan sun manta basu kulle ba, ahankali ta shiga kai tsaye ta wuce d'akin su, toilet ta shiga ta had'a warm water a bathtub ta shiga ciki tana gasa jikin ta daya fashe, tanayi tana kuka saboda azaba harta gama ta fito, sai dai kuma ba laifi ta d'anji dad'in jikin ta.
        Kaya masu nauyi ta sanya saboda sanyi then ta d'auko Teddy'nta ta rungume ta zauna akan sallaya tana kuka ahankali dan karta tashi 'yan uwanta.
K'iran sallah'n asuba ya sata mik'ewa taje ta d'auro alwala ta fito, Kallon su ta rik'ayi abin sha'awa ganin yadda suke bacci peacefully, hawaye ne suka ziraro mata tayi saurin gogewa ta soma tada su.
Tashi a wannan lokacin ya zame musu jiki dan haka nan take suka tashi aka soma layin toilet ita kuma ta soma nafila.
   Bayan sun idar ba wadda ta koma bacci aka soma shirin school, " innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un Sisi me haka ajikin ki? " Kuwaysah tayi ex claiming cike da k'in yardar abinda take gani idanun ta na cikowa da kwalla.
Nan take du attention d'in su yawo kanta suna kallon yadda jikin ta ke a fashe, sai lokacin suka lura da yadda jikin ta ke rawan zazzab'i.
       Kuka ta fashe musu sosai ta rik'o hannun Kuwaysah dake hawaye tace " Sis dan Allah ki fad'amin daga yarinta na zuwa yanzu mai nayiwa Ya Suwayd ya tsaneni? nasan zai fad'a miki, meyasa baya sona kaman ba jinin sa ce ni ba?... "
      Toshe mata baki tayi ta rungume ta suna kukan tare abin tausayi, ta sani du gidan ita da Safwah sunfi cin wahala a gurin sa amma compared to yadda yake wa Safwah nata nafila ne.
Samha ce ta k'araso tana rarrashin su, dakyar ta samu sukayi shiru aka cigaba da shiryawan, badan ranan zasu soma Exam ba da babu inda zata je, amman zuwan ya zama dole inhar ba repeating take so ba cause third term Exam ne daga shi kuma sai final year tasu.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now